Fasalce-Fasalcen Adabin Kasuwa

0
27

Kamar yadda muka gani a babi na biyu, rayuwar adabin Hausa ta biyo zanguna mabambanta, wannan ba sai an yi dogon sharhi ba, domin kuwa daga tashin Hausawa na zaman gargajiya har zuwa lokacin da suka cuɗanya da baƙi an sami sauye-sauye da adabin Hausawa ya yi ko dai ta fuskar sauyawar riga daga ta gargajiya zuwa ta zamani (Larabci ko Ingilishi ko Faranshi) ko kuma ta sauyawar kayan cikin adabin saboda haɗuwa da sababbin ladubban rayuwa.

Irin sauye-sauyen da aka samu daga gargajiya zuwa zamani abu ne da masana sun sha ambaton sa, ƙila abin da ba a fi mayar da hankali kai sosai ba shi ne yadda gwamutsuwa da baƙin al’amurra ke haifar da sababbin batutuwa da ke buƙatar ƙara bincike da nazari.

Batutuwan da suka yi tashe a cikin ‘yan shekarun nan, musamman abin da ya shafi ƙagaggun labaran Hausa, bai wuce batun nan na Adabin Kasuwar Kano ba, wato littattafan da yawancinmu ke kira Labaran Soyayya da suka tuzgo daga sassa daban-daban na ƙasar Hausa da hedikwata a birnin Kano.

Samuwa da watsuwa ko kuma karɓuwa da kuma ce-ce-ku-ce da wannan sabon salon adabi ya samu kansa a ciki, tsakanin marubuta da manazarta da masana a  ƙasar Hausa da ma sassan duniya daban-daban ya jawo ayyukan nazari da musayar miyau mai tarin yawa.

Abin da aka yi ƙoƙarin yi a wannan babi shi ne shimfiɗa tabarmar nazari game da wannan fage ta hanyar neman sanin yadda adabin kasuwa yake ta hanyar tambayar ko akwai wani abu wai shi adabin kasuwa? Idan akwai shi to a yaya yake? Shin ana iya samun sa a ƙasashe masu tasowa kamar Nijeriya? Ko kuwa dai wanda ake da shi da ake kira Adabin Kasuwar Kano, an sa masa sunan ne domin cin mutunci da ɓatunci ko son rai?

Abin da wannan babi ya sa gaba bai wuce amsa waɗannan da ma wasu tambayoyi da ka iya biyo baya ba, ta haka ƙila haske ya ƙaru game da wannan fage na tarihin adabi da zai bayyana mana bambancin da ke tsakanin adabi na zahiri da wanda ake kira na kasuwa da kuma yadda irin fasali ya samu ginuwa a ƙasar Hausa.

Yanayin Adabi da Adabin Kasuwa

A duk lokacin da aka soma batun da ya shafi Adabin Kasuwa abubuwa da dama ke zuwa zuciyar mai nazari ciki kuwa har da tunanin nan da ke nuni da cewa idan har akwai adabin kasuwa to ke nan ashe akwai wani adabin da ba na kasuwa ba.

Idan kuma ka ɗauki ma’anar Adabin Kasuwa a luggance da ke nufin adabi na kowa da kowa ko na yayi ko abin da ke jan hankalin jama’a a kodayaushe, ke nan ana iya cewa akwai adabin da ke da akasin haka, wato adabin da ba na kowa da kowa ba, adabin manya, masu ilmi ko sarauta ko daraja a tsakanin al’umma, a taƙaice dai adabin da ke shimfiɗe a wani wuri domin manazarta da masana ko kuma wanda fagensa ba na kowane ɗan tagaja-tagaja ba ne wajen saye da karantawa da nazari, wato abin da ake wa laƙabi da gangariyar adabi.

Saboda haka ƙoƙarin wannan babi shi ne ya bambanta tsakanin gangariyar adabin da wanda ake wa laƙabi da na kasuwa, domin ta haka ne za a gane yadda tunanin samuwar Adabin Kasuwar Kano ya tusgo, yake kuma gudana.

Adabi dai kamar yadda masana suka yi nuni, kundi ko hoto ko madubi ne (dubi Ɗangambo, 1984:1 da Gusau, 1995:58 da Malumfashi, 2002) da ke ɗauke ko nuna hanyar gudanar da rayuwar al`umma. Za a iya fahimtar irin wannan adabi ta yin la`akari da abubuwa guda biyu; Na farko shi ne harshen da ake amfani da shi, wanda yake maƙunshin tarihi, kuma linzamin bayyana tunani ko kuma wata manufa. Na biyu kuma ita ce fasaha wadda ita ke bayyana tunanin da ke cikin zuciya a aikace (Muhammad, 2001:3).

Shi kuma Cuddon (1999) da yake ƙoƙarin fitar da ma’anar adabi a luggance, cewa ya yi adabi na iya kasancewa abubuwa da dama da suka haɗa da wasan kwaikwayo da waƙa da ƙananan labarai da rubutattun litattafai da dai sauransu. Ya ci gaba da cewa idan har aka ce wannan aikin adabi ne, to maƙunshiyar aikin ta bambanta da sauran kwashe-kwashe na yau da kullum, musamman idan abin ya shafi gaskiyar lamari ko kuma faɗar tarihi, ke nan adabi yana da wasu siffofi da suka bambanta shi da wasu ayyuka da ba su da tasiri irin nasa.

Duk da haka akwai ayyuka ko rubuce-rubuce da dama waɗanda ba a yi su don su kasance na adabi ba ne, amma kuma za a iya sanya su cikin aikin adabi; saboda ingancin aikin da asalinsa ko kuma irin kyawu da kuma fasahar da aka nuna wurin rubuta shi, kamar yadda (Cuddon, 1999) ya nuna.

Daga wannan hasashe za a iya cewa adabin da ke da waɗannan siffofi da aka ambata a sama, shi ne ke kasancewa gangariyar adabi, akasin haka kuma sai ya zama wani abin, ƙila ma na kasuwa ko kuma gwanjo ko makamancin haka.

Kamar yadda kowane sashe na duniya yake da gangariyar adabi, to haka a wasu sassan duniya ake da adabin kasuwa, (Market Literature) ko kuma adabin yayi. To amma idan muka ce adabin kasuwa, nan zai iya kasancewa na yayi, domin kuwa duk abu ɗaya suke tattaunawa. Duk abin da ya kasance na kasuwa to yana da alaƙa da yayi.

Kasuwa dai wuri ne da ake saye da sayarwa na dukkan abubuwan rayuwa, duk wanda ke cikin wannan al`umma yana iya zuwa cikinta domin yin kasuwancinsa. Saboda haka adabin kasuwa wani ɓangare ne na adabin al’umma da kowa zai iya shiga cikin kogin ya yi iyo ko kurme; masani ko malami ko manazarci ko akasin haka. Ke nan irin wannan adabi wani abu ne ko dai waƙa ko wasan kwaikwayo ko ƙananan labarai, ko rubutattun litattafai da aka tsara a wani zangon rayuwar jama’a, ake kuma tsintar su a tsakanin jama’ar ba tare da wani kandagarƙi ba.

Ta fuskar sayar da su ba a yi wani tanadi na wurin da ya dace ba, ko dai a same su a kasuwa ko wurin hirar matasa ko tsakanin matan aure ko makarantu ko kuma ma duk inda jama’a ke tururuwa domin karatu da rubutu. Haka kuma idan aka ce adabi na yayi ne ana nufin cewa zai rayu daga wani lokaci zuwa wani, wato akwai lokacin da yake tashe, akwai kuma lokacin da yake sallacewa, sai a bar masana da yin rubdugu kansa, (Malumfashi, 2002).

Sai dai ya kamata a lura cewa akwai lokutta kuma da ake kallon irin wannan adabin na kasuwa ko yayi a matsayin adabin talakawa ko marasa shi, wato ya keɓanta ne ga wasu gungun jama’a a cikin wani zamani da ba su damu da adabin da ke gudana ba, ƙila ko don ba su da kuɗin sayen sa ko kuma ya kasance na masu gari. Idan aka faɗaɗa tunani a nan za a ga cewa shi wannan adabi na kasuwar ko yayin, saboda canzawar zamani ta sa ake masa wani sabon kallo, musamman da yake  ba a damu sosai da yi masa gangariyar nazari ba.

Kai ba wannan ba ai masana da dama ba su ɗauki aikin adabi irin wannan abin tinƙaho ba, shi ya sa ba a damu da sanin inda ya sa gaba ba. Sai dai ko da aka soma nazarin nasa daga baya, an kuma shigo da ayyukan adabi da mutum na iya cewa ba irin na adabin kasuwa ko yayin da aka saba ji da gani ba ne.

A halin yanzu daga cikin ayyukan adabin kasuwa ko na yayi da ake da su an sanya irin ƙagaggun labaran da a da ba su cikin irin wannan rukuni, wato irin waɗanda suka haɗa da labaran bincike ko tsafi ko na ban tsoro ko soyayya ko na Amurkawan dauri ko na ban dariya ko kimiyya, wato dai ƙagaggun labarai da miliyoyin jama’a ke saye da karantawa a sassan duniya daban-daban ko da kuwa ba a nazarin su a ajin adabi ko jami’o’i, musamman daga shekarun 1930.

Har yau taƙaddama ba ta ƙare ba dangane da ko waɗannan irin ayyukan adabi na gangariyar adabi ne ko kuma kwamacala. Ga masana kamar yadda aka bayyana a (eNotes.com), irin wannan aikin adabi na kasuwa bai da nasaba da aikin ƙwarai, ana nuni da cewa dabara ce kurum ta samun kuɗi da suna, amma ba adabin da za a ta da jijiya wajen karatu ko nazari ba ne.

Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

Don karanta Fasalin Ƙagaggun Labaran Hausa A Zamanin Zuwan Turawa danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMai Maɗi Ke Talla (Mai Zuma Gida Ake Tad Da Shi)
Labarin na GabaFasalin Adabin Kasuwa A Duniya
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.