Abin lura a wannan sashe shi ne waɗannan adabin baka na Hausa masu alaƙa da ƙagaggun labaran gargajiya za a ga duk a kai suke, ana kuma gudanar da su da fatar baki, sai dai wasu sun canza fasali ko kuma siga sakamakon haɗuwar Bahaushe da baƙin al’ummu na kusa da nesa.
Kafin mu fahimci yanayin canjin ya dace mu san cewa waɗannan ƙirƙirarrun labaran na gargajiyar Bahaushe da ya tashi ya gan shi cikinsu tsamo-tsamo sun taimaka masa sosai wurin fito da ɗabi’u da al’adunsa fili, ta yadda kowane ɗaya daga ciki aka ɗauka za a samu nason irin yadda Bahaushe ya tashi yana gabatar da rayuwarsa ta yau da kullum a cikin wannan zamani da suka wanzu.
Waɗannan ƙagaggun labaran na Bahaushe sun samu ne kafin zuwan baƙi, bayan haɗuwarsa da Larabawa sai suka fara sauya fasali. Wasu, kamar yadda muka yi bayani da ma Bahaushe yana da su, amma zuwan Larabawan sai yaƙara fiddo da su, ko kuma a ce cuɗanyarsa da Larabawa sai suka fito da wasu sassan adabin nasa na baka cikin waɗansu kamanni daban, waɗanda tun kafin zuwansu, yake tare da su ko kuma ya samar da wasu sababbi da ya gino su daga cuɗanyarsa da Larabawan, a nan ana magana ne kan almara da ƙissa da kuma hikaya da sauransu.
Ita dai almara kalma ce ta Larabci, kamar yadda muka yi bayani Bahaushe yana da labarai nasa na ban dariya da sanya nishaɗi da raha, amma ba za a kira su labaran jaruntaka ko na matafiya ko kuma na yaƙe-yaƙe ba. Bayan Bahaushe ya aro kalmar almara ne da abin da ke cikinta daga Larabawa, sai ya haɗe su suka zama labarai na ban dariya da wasa ƙwaƙwalwa da makamanta su.
Wannan ne ya sa aka ba ta ma’ana mabambanta, wasu masanan na ganin ‘almara ita ce hanyar gabatar da wasu matsaloli kara-zube ko kuma ta hanyar labari, sannan a buƙaci mai sauraro ya bayar da amsa ko kuma ya zaɓa tsakanin abubuwan da aka ambata, (Magaji, 1982:5).
Shi kuwa (Gusau, 1995:59), yana ganin almara wani shiryayyen labari ne na hikaya da jawo hankali da ake bayarwa don kaifafa tunanin masu sauraro ko nishaɗi. Amma (Umar, 1983:14) na ganin almara ba ta fiye tsawo sosai ba; sai dai takan ƙunshi wani abu na ban dariya ko ƙalubalen da za a nemi mai sauraro ya warware. Haka kuma (Ɗangambo, 1984:16) na ganin almara labari ne ƙirƙirarre wanda ba lalle ne ya auku ba.
Abu muhimmi dai shi ne, dama can tun kafin Hausawa su haɗu da Larabawan suna da ire-iren waɗannan labararrukan na ban dariya da sa nishaɗi, sai dai kawai a ce dacewarsu da ire-iren na Larabawan ne waɗanda suke kira Al-mizahu. Saboda haka tattaruwa aka yi tsakanin labaran Hausawa na gargajiya da irin na al’amarar Larabawan a waje ɗaya domin dacewa da zamani.
Muhimmancin almara kamar sauran fannoni ne na sassan adabin bakan Bahaushe bai wuce haɓaka basira da ƙara hankali da kuma zurfafa tunanin mai sauraro ba. Ita ma hikaya kamar almara an aro sigar ne daga Larabci labaran gargajiya ne waɗanda akasari na masu hikima ne, wato ko dai sun faru da gaske saboda abin da suke koyarwa aka kawo shi, ko kuma ana tunanin idan aka sarrafa hikimar ta wannan hanyar za a ci nasara.
Duk da cewa kalmar ta Larabci ce amma wannan ba wai yana nufin Hausawa ba su da labaran hikaya ba ne tun asali, a a, su ma Hausawa suna da labaran hikaya tun asali, waɗanda suke yi ba wai sai da suka haɗu da Larabawa ba. Sannan kuma akwai wasu labarai da dama da suka danganci hikayoyin da Hausawa suka samo daga na Larabawa. Tasirin gargajiya da hulɗa da al’ummomi da shigowar addinin Musulunci da karatun littattafai shi ne ya haifar da samuwar hikaya a tsakanin Hausawa (Gusau, 1995:65).
Sai dai su al’ummar ƙasar Larabawa na tun asali, wato na lokacin jahiliyya, suna ganin hikaya na nufin kwaikwayon wani abu da wani ya yi, sai daga baya ne suka faɗaɗa ma’anar ta koma ba da wani labari. Da Hausawa suka aro kalmar, suka sanya ma labarai irin nasu da suke ba junansu, sai suka kira ta da hikaya.
Hikaya labari ne da ake ba da wa da ya faru dangane da mala`iku, ko aljannu ko mutane ko rauhanai ko dabbobi ko tsuntsaye ko kuma ƙwari. Wani lokaci kuma takan ɗauki yanayin ƙago wasu labaran don ƙarin bayani kan wani abu ko kwaikwayon sa.
Irin wannan yanayi ne ƙasar Hausa da Hausawa suka samu kansu dangane da labaransu na gargajiya da yadda suka shiga cikin wani fasali bayan haɗuwarsu da baƙi, musamman Larabawa da yadda ya sa suka gina waɗansu sababbin fasaloli da suka aro daga Larabawan. Wannan yaƙara tabbatar mana da cewa wannan tada ta kasance da daɗewa tsakanin Hausawa.
Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.
Don karanta Ƙagaggun Labaran Hausa Cikin Tarihi danna nan
Edita@rumasau-kallamu