Babahabu49
Gabatarwa
Haƙiƙa rayuwa tana tafiya ne tare da zamani, wanda kowanne zamani akwai abubuwan da ya ke zuwa da shi lokacin shi, wani lokaci ya zo da na ilimantarwa wani lokaci kuma na akasin haka, wannan a ƙarƙashin wannan batu za mu iya cewa shigowar fim ya ilimantar da mutane da dama ta hanyoyi daban-daban kamar :sanarwa, ilimantarwa, nishaɗantarwa da sauransu.
TARIHIN SAMUWAR FIM
A cikin ƙarni na goma sha tara ne aka fara tunanin yadda za a yi fim ko majigi a ƙasar Hausa wato a shekarar 1824, wani likita mai bincike a fannin ido, ɗan ƙasar Bartaniya mai suna Peter Mark Roger, shi ne ya fara bincike don samar da wata na’ura mai amfani da kamar idon mutum. Daga shi ne aka samu ci gaba aka ƙirƙiro wani abin wasan yara mai suna Zoetrope wato kallo-kallo na yaro.
Shi kuwa wani ɗan ƙasar Faransa mai suna Charles Emile Ronoad, a shekarar 1844 zuwa 1918 ya fito da wata na’ura mai suna Proxiono Scope, wadda ya lilliƙa hotuna a jikin wani kwarkwaro kamar kallo-kallo da a ke yi na akwati. Wani mai suna Thomas Alra Edison ya samar da wata kyamara mai suna KENETOGRAPHY da kuma na’ura mai SUNA KENETO SCOPE, mai kamar talabijin. Ya kuma tara jama’a a New York ya nuna musu.
A shekarar sai ya gina shago a London da Faris, ya mayar da shi gidan kallo. Daga nan ne mutane fara cewa ashe lallai za a samu kuɗi a harkar. Daga wannan lokaci ne a ka fara tunanin ƙirƙiro Majigi (projector) don a damar damar tara mutane da yawa. Sai fasahar ta fara zama haɗin gwiwa, in da wani Bafaranshe mai suna Louans Jean Lumi’era (1864-1948)da wani Robart W.Palt ɗan ƙasar Bartaniya (1869-1943) da wani ɗan ƙasar Amurka Charles Francis Jonkins (1867-1934) waɗannan mutane su ne suka ƙirƙiro Majigi (projector).
Duk wannan bayanan sun ƙunshi yadda a ka samo fim ko majigi a duniya.
A 1903 a ka fara yin fim a Ikko ta Nijeriya. Fim na farko da aka fara kawo wa aka kalla a gidan kallo na Gloria Memorial Hall da ke Ikko shi ne MORAL RE-ALMAMENT wanda ya ƙunshi (Decomentry) fim ne da yake koyar da a yi biyayya ga Nasara a guji Yahudawa shi ne ma yasa suka sa masa suna ‘Farfaɗo da ɗa’ a’.
Idan kuma muka juyo samuwar fim a Arewa, bayan an samu ‘yancin kai da Nijeriya ta kasu kashi uku sai aka bai wa ma’aikatar yaɗa labarai kula da fim daga nan ne sai ya samu koma baya saboda da ƙarancin tallafi da ya ke samu daga hukumar.
TARIHIN SAMUWAR FINA-FINAN HAUSA
Fim sun fara samuwa ne a wajen 1950-1970 lokacin da ma’aikatar yaɗa labarai ta Arewa (Ministry of information northern Nigeria) take ƙoƙarin wayar da ‘yan Arewa dangane da harkokin noma da wayar da kansu a al’ amuran da suka danganci rayuwar yau da kullum, to sai ma’aikatar ta zaɓi ta yi amfani da fim domin shi ne hanya sauƙi da za a jawo hankalin ‘yan Arewa a kan su noma abubuwa da gomnati ta ke buƙatar su da su a kan yadda za a gudanar da noma da hanyar amfani da abubuwan zamani.
To gomnatin wannan lokaci ta yi amfani da fim domin gudanar da wannan aiki wadda a ka gudanar ta hanyar amfani da mota wadda ta ke ɗauke da na’urorin nuna fim wato (Projector) yadda aka riƙa amfani da wannan mota,ana bi birane da ƙauyuka domin ilimantar da su a wannan ɓangare na noma da kuma ɗebe musu kewa.
Fina-finan Hausa na farko da ma’aikatar yaɗa labarai ta Arewa ta fara nuna wa jama’a sun haɗa da: fim ɗin ‘Baban Larai’ da ‘Ɗan Arewa a London’ da ‘Musa ya zo birni’ da sauransu. Kafin mu ƙara tsunduma cikin aikinmu za mu yi abin da ake kira waiwaye adon tafiya domin musan wai shin menene fim ko majigi?
Fim wani ɓangare ne daga kafar sadarwa ta lantarki wadda ta ke samar da gani da ji da motsi domin amfanin mutane masu yawa. Fim tantagaryar kimiyya da fasaha ce kuma rayuwar ɗan Adam ce a ke nunawa. Fim yana ɗauke da tarihi da ɗabi’un jama’a da mahallinsu da kuma suturunsu, musamman bisa harshensu da tsarinsu na rayuwa da hanyoyin tunaninsu.
Har ila yau fim hanya ce ta sanarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa da faɗakarwa da yaɗa manufa da tallatawa. A dunƙule kafa ce daga cikin kafafen yaɗa labarai, sannan kuma hanya ce ta kasuwanci da samar da aikin yi ga al’umma. Idan muka duba ma’anar da muka kawo za mu ga in da muka ambaci “Fim hanya ce ta ilimantarwa” wanda aikinmu zai koma ƙarƙashin wannan gaɓar ne.
Kafin mu bayar da ma’anar fim na ilimantarwa (Educational film) za mu ɗauki ita kanta kalmar “ilimantarwa” domin mu ji ma’anarta. Asalin kalmar “ilimantarwa” an samo ta ne daga Larabci ‘Al’ilmu’ wacce ta ke nufin (Rashin jahilci) a Larabce, ma’ana mutum ya san abu. Shi kuma fim na ilimantarwa (Educational film) yana nufin fina-finan da a ke yin su domin ilimantarwa.
Fina-finan ilimantarwa suna da muhimmanci da amfanarwa ta fuskoki mabambanta da kuma kanu daban-daban. Gidan kallon majigi ko fim ya rabu zuwa wasu muhimman rukuni guda uku waɗanda su ka haɗa da :
- Ilimantarwa
- Umarni
- Nishaɗantarwa
Amma aikin mu ya karkata zuwa ga fina-finan ilimantarwa. Fina-finan ilimantarwa ana shirya su ne don sanar da al’umma ko jama’a a kan wasu al’amari na rayuwa da kuma wayar musu da kai. Misali idan muka ɗauki fina-finan ilimantarwa a harkar tsaro; A lokacin yaƙin duniya na ɗaya, sojojin ƙasa da na ruwa an haska musu fim na atisaye wanda hakan ya zamo wata babbar hanya don koyar da jami’an tsaro. Ta haka ne ya zamanto wata hanya ta samar da wasu muhimman bayanai.
Haka kuma idan muka kalli fim ɗin ‘Baban Larai’ ya ilimantar da yadda jama’a za su samu ƙaruwar abin hasafi ta yadda ya nunar da su noman auduga ya ɗara noman hatsi samu. Ire-iren fina-finan ilimantarwa.
- Fina-finan ilimantarwa na tarihi.
- Fina-finan ilimantarwa na fasaha da ƙere-ƙere.
- Fina-finan ilimantarwa na wallafe-wallafe da fasahar harshe.
Kammalawa
Duba ga yadda muka rattabo samuwar fim tun daga sarari (duniya) har cikin ƙasa Nijeriya har zuwa Arewa da ƙasar Hausa, da kuma yadda muka bayar da ma’anar fim da kuma fim na ilimantarwa, za mu ga cewa lallai fim na ilimantarwa ƙaruwa ne na dukkanin al’umma.
Manazarta
Multiple examples of language training films
Ahmad N.(2003)The influence of indigenous and foreign culture on Hausa Home Video in Nigeria in Adamu A. U (Educational) Hausa home videos ;Technology, economy and society. Kano:Gidan Dabino publishers.
Danna nan don karanta Alaƙar Hausa Da Fulatanci
Edita@rumasau-kallamu