khairatu.shehu
An yi bayani cewa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na cutar da mashaya da ma danginsu. To waɗannan matsaloli ba sun tsaya nan kaɗai ba ne, har ma al’ummar da suke ciki ba ta tsira ba. Wasu daga matsaloli ko illolin da shaye- shayen miyagun ƙwayoyin yake haddasawa ga al’umma, sun haɗa da:
Rashin Tsaro: Abu ne sananne cewa mashaya miyagun ƙwayoyi ne ke aikata akasarin manyan-manyan laifukan da suke faruwa a yau. A yau duk inda ka ji an kama ‘yan fashi ko ‘yan ɗaukar amarya ko ‘yan caca ko ɓarayi ko masu tayar da tarzoma, idan aka bincika za a iske mashaya ne, kuma mafi yawan maɓoyar su bai wuce gidan mata ‘yan uwansu mashaya ba.
Tashe-Tashen Hankula: Kusan dukkanin rikice- rikicen addini da na ƙabilanci da na siyasa, na ruruwa ne sanadiyar yin uwa da makarɓiya da mashaya miyagun
ƙwayoyi ke yi, kuma mafi yawan waɗannan fitintinu mata mashaya suna ba da gudummawa sosai.
Yawaitar Haɗura: Aukuwar haɗura ya zama ruwan dare a wannan lokaci. Sau da dama haɗuran na faruwa saboda masu tuƙin na cikin maye, wasu ma suna tare da mata mashaya ‘yan uwansu a cikin motocinsu suna ta sharara gudu don son a nuna birgewa ga matan da ke cikin motocin, musamman lokacin da ake tafiya wajen liyafa ko yawon shaƙatawa na ƙarshen mako (picnic).
Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa: Tattali yana daga abubuwa da shaye-shayen kayan maye ke yı wa zagon ƙasa. Mashaya ba sa iya yin wani aiki mai fa’ida ga kansu ma balle kuma ga al’umma. Maimakon haka sai su zamo ci-ma-zaune, kuma nauyi ga al’umma. Hakan yana yi wa tattalin arziki zagon ƙasa ta ɓangarori guda biyu. Na farko shi ne kuɗin da suke ɓarnatarwa wajen sayen kayan maye. Na biyu kuma shi ne kuɗaden da hukuma ke kashewa wajen yi musu magani ko kuma gyara ta’asar da suka tafka.
RABE-RABEN MAGANI
Masana sun bayyana rabe-raben magunguna zuwa gida uku, ga su kamar haka:
*Ƙwayoyin da aka yarda da su, aka amince da a yi amfani da su don maganin wata cuta (legal/licit drugs), misali Paracetamol.
*Ƙwayoyin da ba a amince a yi amfani da su ba don yin magani saboda haɗarinsu (illegal/illicit drugs), misali wiwi da hodar Iblis (coceine) ko Heroin.
*Abubuwan da jama’a suka yarda da su a al’adarsu da ɗabi’unsu na zamantakewa cewa ba laifi ba ne in an yi amfani da su, (social drugs), misali taba da goro da kofi (caffe) da bammi ko kuma fura mai tsami da sauransu.
Na farko su ne waɗanda aka yarda da su, ana rubuta wa marasa lafiya bayan an duba shi, kuma ya je ya saya ya yi amfani da su. Su ne ƙwayoyin da aka yarda kuma aka amince a yi amfani da su bisa ka’idojin likita. Misali akwai maganin da ake kira Baliyam (diazepam).
Wannan magani ana bai wa marasa lafiya da suke da matsala misali ta rashin barci da hawan jini da cutar farfaɗiya domin su sami natsuwa da barci, kuma yawanci ana ba da shi ne rabin ƙwaya ko kuma ƙwaya ɗaya idan an shiga matsanancin yanayi, kuma yawanci ana sha ne da daddare. Sauran misalai su ne maganin mura ko tari, wato maganin rage zafi ko zugi ko raɗaɗi ko ciwo. Don haka duk maganin da aka bayar da shi bisa jagorancin likita da amincewarsa shi ake nufi. Ana bin ƙa’idojin lokutan da za a sha maganin don samun fa’ida.
Na biyu su ne waɗanda ba a amince a yi amfani da su ba. Hakan yakan faru ne sanadiyyar yin abin da ba a yarda da shi ko amincewa da shi ba. Yin amfani da ƙwaya ba bisa ƙa’ida ba. Misali kamar shi dai maganin diazepam ɗin wanda a baya na ce ya kamata a sha rabi ko guda ɗaya, sai ya zamanto an sha fiye da haka ba tare da amincewar likita ba, maʼana sha ba tare da izini ba aka sha shi; hakan ya zamanto ba bisa ƙa’ida ba (a sha shi ba adadi) sai ya zamanto an sha kamar ƙwaya 10 ko fiye. Wannan shi ne shan magani ba bisa ka’ida ba.
Na uku su ne, kasancewa al’umma sun aminta da hulɗa da wasu abubuwa a zamantakewarsu, kamar cin goro ko shan fura mai tsami da sauransu, to in aka yi amfani da ire-iren waɗannan abubuwa suka wuce ƙa’ida (na hankali) sai su zama in ba a sha ba ko ba a ci ba ba zaman lafiya, daga nan kuma sai su zama har rashin lafiya lafiya ake yi, daga nan kuma ya zama ƙwaya wadda za ta iya cutarwa.
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.
Domin karanta Wasu Daga Dalilan Shaye-shayen Ƙwayoyi danna nan
Edita@rumasau-kallamu