Hanyoyin Bincike A Rubutu

0
24

Kusan duk rubutun da marubuci zai yi, ƙirƙirarre (fiction) ko wanda ba ƙirƙirarre ba (non-fiction) abu na farko da ake sa ran mutum zai yi shi ne; bincike. Bincike hanya ce ta fito da abinda ke ɓoye zuwa sarari. Hanya ce da ake bi don ganin an amsa wasu tambayoyi game da wani al’amari.

Ta hanyar bincike ake tattaro bayanai da killace su tare da sarrafa su ta yadda za a iya samun wani sabon ilimi, ko tabbatar da wani abu da ake zargi ko ake da tantama a kai. Kusan duk wani cigaba da ake samu a duniya to bincike ne ke haifar da shi.

Kamar yadda idan aka tsinci gawa, za a ɗauke ta a je a yi forensic investigation har a gano dalilin mutuwar mamaci, haka ake sa rai idan marubuci ya samu jigo, zai soma gudanar da bincike kafin ma ya fara rubuta komai.

Bincike na nufin karantar wasu abubuwa ko hanyoyi, don gano haƙiƙanin gaskiyar da zai iya zama wata hujja ko madogara kan abinda ka ke son bayyanawa. Wani marubuci mai suna Robert Mekee na cewa; “Idan ka gudanar da wadataccen bincike, to za ka ga tamkar labarin ya kammala rubuta kan sa, tun ma kafin ka fara rubutawa.”

Bincike ba abu ne mai sauƙi ba, wasu marubutan ba su san ta yadda za su fara yi ba. Sai ka ga mutum ya tattara bayanai har sun yi masa yawa. Ya kasa gane ta hanyar da zai sanya bayani a cikin labari. Garin a rubuta labari mai cike da nishadantarwa, sai rubutun ya zama mai gundura. A maimakon ya rubuta novel sai ka ga ya ɓuge da rubuta textbook ba tare da ya kula ba.

DALILAI BIYU NA YIN BINCIKE

1) Wataƙila kana da cikakken ilimi kan abinda ka ke son yin rubutu a kai, to amma duk da haka kana buƙatar ƙarin bayani ta wata mahangar. Hakan zai taimaka wajen gamsar da mai karatu har ya gamsu cewa wannan ba kawai zallar ra’ayinka ba ne.

2) Wataƙila ba ka san komai game da saƙon da ka ke son bayyanawa ba ta fuskar ilimi. To amma kana buƙatar sani don ka wayar wa da mutane kai.

KAFIN FARAWA

Kafin ka fara bincike akwai abubuwa guda uku da ya dace ka halarto zuwa allon majigin zuciyarka.

1) Wanne saƙo kake son ka isar (message)

2) Su wane ne za su karanta saƙon (target audience)

3) Sai ka yi wa kan ka tambaya kamar haka; “Wacce irin hujja zan ba wa mai karatu ya gamsu da bayanin nan nawa?”

Sai dai kada ka damu da lallai sai ka gamsar da mai karatu. Duk abinda ka yi ba za ka iya gamsar da kowa ba. Kawai ka yi iyakar bakin ƙoƙarinka.

Danna nan don karanta babban kundi

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceHaihuwarsa Da Shayar Da Annabi S.A.W
Labarin na GabaTarihin Salmanu Faris Adamu