Ma’anar Aure A Ƙasar Hausa 2

0
22

Aure wani zama ne halastacce tsakanin mace da namiji bisa ga matsayin miji da mata, wanda al’adar Bahaushe da kuma addinin musulunci suka amince da shi. Babban dalilin da yasa ake yin aure shi ne, don samun yaɗuwar jinsi a doron ƙasa gami da wanzuwar al’umma. Aure ba ya inganta sai da waliyyi (mace waliyyi, namiji kuma wakili), siga, sadaki da kuma shaidu.

Abubuwan da suke da alaƙa da aure a ƙasar Hausa

1. Samartaka (Zance ko hira).

2. Sallama/ nuna kai.

3. Toshi.

4. Baiko / sa rana.

5. Sa lalle/ rufi.

6. Ɗaurin aure.

7. Wankan amarya.

8. Biki (gidan su amarya da ango).

9. Biɗar kai/ buɗan kai.

10. Sayen baki.

11. Kai Gara.

12. Gai-da surukai.

13. ‘Yar zaman ɗaki/ ƙanwar rana.

Danna nan don karanta rabe-raben auren Hausawa

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceTarihin Hajiya Halima Jumare Kudan
Labarin na GabaTarihin Marigayi Malam Mammada Kudan