Me Za Ka Yi Idan Ka Ga Ɗan Uwanka Zai Mutu?

0
27

Manzon Allah S.A.W Yayi Mana Wasu Bayanai Dangane Da Mutuwa: Da farko babbar alama da za a gane kusantowar mutuwa ga mutum mai matsananciyar jinya ta rashin lafiya shi ne, lokacin da ka ga bayan tsananin ciwo sai ka ga an samu ɗan sauki, zufa wato gumi ya fara fita daga goshin shi mara lafiyan. To wannan in dai ba a yi Sa’a  ba to alamar mutuwa kenan.

IDAN KA GA WAƊANNAN ALAMU SUN BAYYANA MENENE ZA KA YI WA ƊAN UWANKA

Abinda akeso a daidai wannan lokaci shi ne, kalmar shahada wato LA’ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADURRASULULLAH. A sigar karantawa tare da maimaitawa. Ba za ka ce wane ka ce LA’ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADURRASULULLAH ba, ba za ka ce haka ba, za a yi ta maimaitawa a gabansa har shi ma ya kama faɗa, ko kuma ya faɗi a zuciyarsa, saboda ya mutu akan sunnar annabi Muhammad S..A.W.

Abu na gaba shi ne, idan kai makaranci ne, an so ka karanta masa Suratul-Yaseen. Bayan ka tabbatar ya rabu da duniya, wato bayan ran ya fita. Abinda za ka yi na gaba shi ne za ka rufe idanunsa da kuma bakinsa, shi mamacin.

Sa’annan kuma a wannan lokacin ne za ka ba da labarin mutuwarsa ga makusantansa, kafin sanarwa ga sauran jama’a. Daga wannan lokaci ne za a fara shirya shi izuwa ga masaukinsa, ba tare da jinkiri ba.

Bayan shirya shi, abinda ke biye shi ne yi masa wanka tare da sutura wato likkafani kenan, daga nan kuma sai yi masa rakiya zuwa makwancinsa, wato kabarinsa tare da sanya shi a ciki da rufewa, wato binnewa.

Daga wannan lokaci da aka binne mamaci, shari’a ta hana ake ambatarsa da mummunan aiki da ya aikata ko kuma wasu munanan kalamai ko suna. Domin duk abinda ya aikata ya koma tsakaninsa da Ubangijinsa.

Domin daga wannan lokacin dukkan lamuransa sun koma ga mahalicci Ubangijinsa.

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceYaushe Tura Za Ta Kai Bango?
Labarin na GabaAbin Da Zai Faru Gobe