Har Yanzu Akwai Matsala Fa

0
27

Daga Lokacin da ya zamto mace na goyon ciki amma kullum tana cikin ƙunci da kuka lokaci zuwa lokaci, wannan na shafar yanayin bugun zuciyar abinda take ɗauke da shi (heart rate) wanda yakan iya developing ɗin heart problems tun a ciki (jaririn) Sannan ita kanta ba za ta dinga saurin warkewa ba akan lokaci in rashin lafiya ta same ta. Don haka wajibi ne mazaje ku gane matanku fa abokanku ne, ƙannenku ne, ƙawayenku ne, jikinku ne baki ɗaya don haka ku yi duk yadda za ku yi ku kyautata musu.

GA INDA BAYANIN NAWA YAKE

Akwai babbar matsala tabbas a yanzu mata sun duƙufa suna zuwa Awo (ANC)  amma ba sa zuwa asibiti haihuwa.

A gaskiya muna asarar rayukan mata masu ɗsmbin yawa Sakamakon matsalolin da ke biyo baya bayan an haihu. Kamar yadda nake faɗa muku ba fa a gane an haihu lafiya sai an sami kwana 40 da haihuwa. Wallahi mu muka san irin ƙididdigar da muke samu a ƙauyuka, garuruwa da birane.

Lallai muna buƙatar ku  ringa zuwa asibiti haihuwa, saboda jijjiga, da zubar jinin da komai. Wallahi dole mu kau da tunanin babu da zancen talauci. Daga Sanda ka ga iyalinka da ciki ya kamata a tanadin da za ka fara ya zamto har da na kaita asibiti ta sami kulawar jami’an lafiya wajen haihuwa don girman Allah.

Musamman jihohin Jigawa, Kano, Yobe, Maiduguri suna daga gaba-gaba cikin jihohin da ake rasa mata. Yanzu  an yi tsari a duk yadda mace ta saba haihuwa za a bar ta ta haihu a haka; walau a ruwa, a tsugune, a tsaye, a kwance ko a dire.

Fatan wannan sakon ya shiga kunnuwan mu, musamman ku maza wannan matsalar daga ku ne, wani azzalumin yana da hali amma in an magana sai Yace za a jawo masa wahala ko kuma wani ma da niyya, amma ‘yan uwansa su hana, to ka sani iyalinka haƙƙin ka ne kuma kai Allah zai kama da laifi ba ‘yan uwanka ba. 

Domin in ta mutu hidimar abincin da za ka yi da sauran ɗawainiya ai ka kashe ninkin kuɗin asibitin, wani dama ba ya gane Allah ya yi masa baiwa sai ran da ya rasa abinda yake ganin a da ba komai ba ne.

In kana son matarka da gaske to mu gani a asibiti. Allah yasa mu dace.

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceSanya Contact Lenses Domin Ado Na Birgewa
Labarin na GabaDuka A Murɗe