An haifi Manzon Allah (SAW) ranar Litinin 12 ga watan Rabi’u Auwal. Mahaifinsa shi ne Sayyidina Abdullahi ɗan Abdulmutallib, nahaifiyarsa kuma Nana Amina yar Wahab.
Ana kiran shekarar da aka haife shi (SAW) shekarar giwa, saboda a wannan shekarar ne Abrahata ya zo daga “Yaman” da rundunarsa tare da giwa don ya rushe Ka’aba, amma Allah ya halaka su ta hanyar aiko da tsuntsaye suka dinga jifan su da tsakuwa daga wutar “Jahimu” har sai da suka halaka baki ɗaya.
Domin karanta cikakken bayani akan Mafifitan Aiyukan Mai Azumi danna nan.
Annabi (saw) ya girma a cikin maraici, dama mahaifinsa Abdullahi ya rasu tun kafin a haife shi, sannan kuma mahaifiyarsa Amina ita ma ta rasu a lokacin da yake ɗan shekara shida a duniya! Bayan rasuwar mahaifiyarsa, sai kakansa Abdulmutallib ya karɓi rainonsa, shi ma Abdulmutallib ɗin sai ya rasu a lokacin Manzon Allah (SAW) yana ɗan shekara takwas a duniya! (wato bayan shekara biyu da rasuwar mahaifiyarsa) daga nan sai baffansa Abu Ɗalib ya karɓi rainonsa.
Da akwai abin lura a cikin wannan lamari, kasancewar Annabi (SAW) an haife shi maraya, kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya ɗauke rayuwar magabatansa amma kuma duk da haka ya sami kulawa ta musamman daga Allah Maɗaukakin Sarki, maraya ne shi amma ya fi kowa tarbiyya, da nutsuwa da halaye nagari, wannan bayanin ya fito a cikin Alkur’ani inda Allah yake bayyana wa Manzon (SAW) cewa (ألم يجدك يتيما فاوى ) wato:
Allah ya samar da Manzon Allah kuma ya ƙaddara masa tasowa a cikin maraici, sai Allah Ta’ala ya jiɓinci kulawa da shi, dama an ce Manzon Allah ya ce: “Ubangijina ne ya ladabtar da ni kyakkyawar ladabtarwa”
Domin karanta Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su Danna nan
Haƙiƙa irin waɗannan abubuwan lura suna daga alamun Annabta ga masu tsinkaye, kuma irin su suna da yawa a rayuwar Annabi Muhammad kamar abin da ya faru a lokacin da kakansa ya bayar da shi raino da shayarwa ga Nana Halimatus Sa’diyya wadda kafin ta karbi rainonsa (SAW) tana cikin ƙuncin rayuwa da rashin ƙosassun dabbobi, amma tana karɓar Annabi ta kai shi gidanta sai albarkatu suka dunga ɓarkowa ta ko’ina.
Kuma Annabi (saw) ya bambanta daga da dukkan sa’aninsa wajen nutsuwa da nagarta har sai da aka yi masa laƙabi da sunan “Amintacce” shi suke kaiwa ajiyar kayansu masu tsada, kuma shi su mke gayyata ya raba gardama a tsakaninsu idan jayayya ta tufke!
Bugu da ƙari, a lokacin da Manzon Allah (SAW) ya bi baffansa Abu Ɗalib zuwa ƙasar Sham don yin kasuwanci Wani Malami “Buhaira” ya ga alamomin Annabin ƙarshen a tare da Manzon Allah, waɗanda ya san su daga bayanan masana littafan da suka gabata. Nan take Buhaira ya tambayi Abu Ɗalib cewa: “Yaya kuke da wannan yaron?” (a lokacin shekarun Manzon Allah SAW goma sha biyu) sai Abu Ɗalib ya ce da shi, “Ɗana ne”. Ta ke Buhaira ya ce, “Bai kamata a ce mahaifinsa yana raye ba, sannan ne Abu Ɗalib ya ce “Ɗan ƙanina ne, wanda ya rasu kafin a haife shi….”
Haka ma a lokacin da Manzon Allah (SAW) ya cika shekara ashirin da biyar
Labarin kirkinsa da amanarsa ya yaɗu a garin Makka, wannan ne ma abin da ya ja hankalin Nana Khadija har ta nemi ya amince ya karɓi dukiyarta don kasuwanci, kamar yadda takan ba wa wasu mutane.
Manzon Alllah SAW ya amince ya tafi ƙasar Sham tare da yaronta Maisara, wannan tafiya ta kasance mai cike da albarka da kuma ɗumbin nasarori,
Domin karanta bayani Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da BismillAh A Cikin Sallah Danna nan
Bayan sun dawo Makka, sai Maisara ya kwashe duk labarin abin mamakin da ya dinga gani a wajen Manzon Allah (saw) ya gaya wa Nana Khadija ya faɗa mata kirkinsa, da nagartarsa da kuma amanarsa…. saboda haka ne Nana Khadija ta nemi Annabi ya amince ya aure ta.
Bayan Manzon Allah (SAW) ya auri Nana Khadija ta ruɓanya ƙaunarta da kuma biyaryarta gare shi, tare da ba shi goyon baya da sadaukarwa a kan duk abin da ya damu da shi.
Tun kafin Allah ya aiko Manzon Allah da saƙon Manzonci, ayoyi da alamomi sun nuna cewa yana da wata baiwa ta musamman wadda ta wuce irin baiwar da aka saba gani a wajen haziƙai da jarumai na tarihi. Shi tasa baiwar tanadi ce daga Allah, don ya zamar da shi Annabi kuma Manzon na ƙarshe, wanda saƙonsa zai zama gamamme mai shiryarwa izuwa tafarkin tsira har zuwa ƙarshen rayuwar duniya.
Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin “Bita A Cikin Tarihin Shugaban Halitta” Domin karanta cikakken littafin ko daukoshi danna nan