Yadda Mace Ke Yin Bincike Da Kanta A Kan Manema Auranta

0
103

Mace za ta yi bincike don ta ji mene ne halayen mai neman aurenta. Sai kuma ta yi shawara da mutanen kirki. Sannan ta yi azama a cikin lamarinta, to in sha Allahu ba za ta yi nadama ba. Domin faɗin Allah da ya ce:

“Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka ƙudiri aniya, to ka dogara ga Allah”.

(Al’imran:159)

Domin karanta cikakken bayani a kan Muhimmancin Aure A Rayuwa danna nan

Sannan kuma mun samu cewa a mata sahabbai akwai Faɗimatu bnt Qais tana da manema guda biyu, Mu’awiyah da Abu Jahmin. Sai ta je wajen Annabi don ya ba ta shawara wanda za ta zaɓa, sai ya faɗa mata cewa, “Abu jahamin ba ya ajiye sandarsa. Wato mai dukan mata ne”. Wasu kuma suka ce yana nufin matafiyi ne. shi kuwa Mu’awiya talaka ne, ba shi da komai”. Sai Annabi (S.A.W) ya ce mata “Ga Usama bn Zaid, ki aure shi mana”. Sai na ƙi Usama a raina. Sannan Annabi ya sake cewa, “Ki auri Usama”. Sai  dai na aure shi a haka. Sai Allah ya sanya mana alkhairi.

Domin Dauko Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceAbubuwan Dake Sa Wa Miji Ya Zamo Mafi Soyuwa A Wajen Matarsa
Labarin na GabaYadda Namiji Zai Bi Wajen Zaɓen Mace Tagari