Yadda Namiji Zai Bi Wajen Zaɓen Mace Tagari

0
124

Wannan babban aiki ne a kan namiji. Daga inda ka kuskure wajen nemar wa kanka mace tagari. To haka za ka yi rayuwa mara daɗi. Domin mace tagari ita ce ke ba da natsuwa da jin daɗi, ta kuma taimake ka duniyarka da lahira.

Ta tsaya wajen kula ma da yara har su zamo mutane nagari. Annabi Alaihissalam ya yi nuni da mace tagari, ita ce fa cikar jin daɗi. Annabi (S.AW) ya ce:

“Duniya wani ɗan wuri ne na jin daɗi ƙanƙani, amma mafi ɗan wannan jin daɗin, shi ne mace tagari”. (Muslim)

Haka kuma Annabi Alaihissalam ya yi wa maza nuni da irin abin da ake dubawa don mutum ya dace wajen samun mace tagari.

Domin karanta Abubuwan Da Suke A Farkon Aure Danna nan

Annabi Alaihissalam ya ce:

“Ana auran mace don abubuwa guda huɗu: Saboda kyanta, ko dukiyarta,

ko danginta, ko kuma don addininta, na lazamta muku (auren) ma’abociyar

addini. (idan ba ka auri mai addini ba) Damanka ta yi kuka”

Bukhari

Domin Dauko Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceYadda Mace Ke Yin Bincike Da Kanta A Kan Manema Auranta
Labarin na GabaKakannin Manzon Allah (Saw)