An haifi Malam Muhammad ɗan Malam Ali a unguwar Zage da ke Birnin Kano a zamanin Sarkin Kano Usman. Gwani Ɗan birni ya sha bam-ban da ragowar takwarorinsa makaranta.
Domin kuwa ya fara neman ilmi ne a fagen Fiƙhu da Hadisi cikin tsarin ilmin zaure; musamman ma wurin Malam Baƙo da Malam Habu da ke Unguwar Ciromawa.
Tsananin sha’awarsa ga zurfafa neman karatun Alƙur’ani ya sa ya nemi izinin mahaifinsa don ya fita zuwa wasu wurare da ke wajen Kano. Koda Gwani Ɗanbirni ya samu izinin mahaifinsa sai ya yi niyya ya fita. A lokacin ba wanda ya san inda ya nufa, ballantana inda za a same shi. Bayan wani lokaci ne aka samu labarin yana wurin Gwani Abdullahi da Gwani Ahmadu.
Koda Gwani Ɗanbirni ya samu labarin wani mashahurin masanin Alƙur’ani a garin Ubba sai ya tafi izuwa gare shi. Daga nan ya dawo gida Kano bayan ya tumbatsa kuma ya shahara wajen ƙarfin tilawa da baiwa a fagen karatun Alƙur’ani. Wannan ya zaburar da irin abokansa na ƙuruciya da ke Unguwar Zage, saboda ganin irin ɗimbin ilmin da Ubangiji Maɗaukaki Ya yi masa a wani lokaci taƙaitacce. Manyan abokan karatun Gwani Ɗanbirni sun haɗa da Gwani Saleh Ɗanzarga da Malam Abdu Ɗankankare da Malam Kafi-ɓari da Malam Musa jikan Shehu da Malam Sani Adam.
Manyan malaman Gwani Ɗanbirni sun haɗa da mashahurin masanin Alƙur’anin nan Gwani Hamad da Gwani Abdullahi Ɗan Gwani Ahmadu da Gwani na Ubba da Malam Awaisu na Madabo da Malam Inuwa almajirin Malam Salga da Gwani Dubu da Gwani Hamidu.
Game da yawan almajiran Gwani Ɗanbirni kuwa za mu iya cewa ɗaruruwan almajirai sun sami Alƙur’ani a hannunsa Fitattu; daga cikin Su sun haɗa da Malam Tijjani Rabi’u da Malam Idi da Malam Ahmadu Ɗanjajaye da Malam Isa ƙofar Mata da Sharu Bala da Sharu Ahmadu da Malam Ahmadu Mai Makarantar Dare Gabari da Alhaji Gagara da Na’ibin Masallacin Juma’a na Shehu Ahmadu Tijjani da Malam Inuwa Mai Gemu da Alhaji Ali Indabawa.
Gwani Ɗanbirni ya shahara da kyawawan halaye da sabo da jama’a. A lokaci guda kuma yana da ƙima wurin Sarki da attajirai na Kano irin su marigayiya Mai Babban ɗaki; mahaifiyar mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da Khalifa Sarki Sunusi (Murabus) da Alhaji Aminu Ɗantata. Gwani Ɗanbirni ya rasu a watan 10 na shekarar 2004. Ya bar ‘ya’ya maza da mata goma sha biyar (15).
Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Malam Mahmud Manzo Arzai danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.