Jin ƙaiƙayi kamar ƙwaro yana yawo a ƙarƙashin ko saman fatar jikin mutum shi ake kira “formication” a likitance. An samo Kalmar ne daga “formica” a harshen Latin na ƙasar Rome, wacce take nufin tururuwa (ant).
Ƙaiƙayin yakan zo ta siga daban-daban. Yana iya kasancewa jin tsikari (tingling), ko jin waiwayi (sensation), ko jin ƙaiƙayi (itching), ko jin raɗaɗi (burning). Wani lokaci kuma yakan zamo ɗaukewar jin motsi gaba ɗaya idan aka taɓa fatar mutum (numbness), wato mutum ya ji kamar ba jikinsa aka taɓa ba.
Abinda aka sani shi ne ana jin ƙaiƙayi ne idan wani abu ya taɓa fata. Amma idan jin tafiyar kiyashi a jiki ne, to, mutum zai ji ƙaiƙayi alhalin babu abinda ya taɓa fatarsa. Ma’ana, zuciyarsa ce take riya masa cewa wani abu yana yawo a saman fatarsa ko ƙarƙashin fatarsa, don haka sai ya riƙa jin ƙaiƙayi.
Irin wannan ƙaiƙayin yakan haifar da rashin jin daɗi tare da soshe-soshen jiki, har yakai ga yi ma fata rauni ba tare da daina jinsa ba.
RABE-RABEN ƘAIƘAYIN TAFIYAR KIYASHI A JIKI
Ƙaiƙayin tafiyar kiyashi a jiki ya rabu gida biyu kamar haka:
1. Tafiyar kiyashi a jiki na sa ruɗanin ƙwaƙ\walwa, wanda yake faruwa ba tare da wata matsala ta rashin lafiya ba amma mutum ya riya a zuciyarsa kamar kwaro yana bin jikinsa. A likitance ana kiransa “primary delusional infestation”.
2. Tafiyar kiyashi a jiki wanda wata rashin lafiya ko kuma wani yanayi da mutum ya sami kansa a ciki yake haddasawa. A likitance ana kiransa “secondary delusional infestation”.
Primary da secondary delusional infestations ɗin suna aukuwa ne idan aka sami rashin daidaiton wani sinadari mai suna “dopamine” a cikin ƙwaƙwalwa. Shi ne yake da alhakin aika saƙo daga ƙwaƙwalwa zuwa sassan jiki domin yin motsi, tunani, nishaɗi, damuwa, da sauransu. Saboda haka ake kiransa “neurotransmitter hormone”, wato ɗan saƙon sinadari.
A nan za mu fahimci cewa tafiyar kiyashi a jiki tana kasancewa a dalilin matsalar ƙwaƙwalwa (psychiatric disorder), ko rashin lafiya (underlying medical condition), ko kuma amfani da ƙwayoyin magani (drug and medication use).
TAFIYAR KIYASHI A JIKI DALILIN MATSALAR ƘWAƘWALWA
Matsalar ƙwaƙwalwa (psychiatry) a likitance ba tana nufin ciwon hauka ba ne. A a, wani fanni ne na ilimin lafiya wanda ya shafi ganowa da magance matsalolin hankali (mentality), tunani (memory), shu’uri (emotion), da sauransu. Tafiyar kiyashi a jiki dalilin matsalar ƙwaƙwalwa ya ƙunshi:
1. Damuwa (depression): Tana sanya mutum ya riƙa jin ɓacin rai mai tsanani ba tare da an yi masa wani abu da ya cancanci ya ɓata masa rai ba. Hakan zai sanya mutum ya daina sha’awar komai a rayuwarsa, har ya riƙa tunanin cutar da kansa ko kuma wani makusancinsa. Mutum yakan gane cewa yana da matsalar damuwa idan ya ɗauki tsawon makonni biyu ko fiye da haka yana jin ɓacin rai babu ƙaƙƙautawa. Damuwa na sanya mutum ya riƙa jin tafiyar kiyashi a jikinsa.
2. Jin tsoro (anxiety): Shi ne mutum ya riƙa jin fargaba da bugawar zuciya kamar wani mummunan abu zai faru da shi. Yakan faru ne a dalilin matsalar talauci, rashin masoyi, halakar dukiya, rashin aikin yi, da sauransu. Jin tsoro yana sanya mutum ya riƙa jin tafiyar kiyashi a jikinsa.
3. Ruɗewa (schizophrenia): Matsala ce ta ƙwaƙwalwa wacce take sanya tunanin mutum ya rikice ya riƙa gane-gane, ko mafarkai, ko sambatu. Ruɗewa tana sanya mutum ya riƙa jin tafiyar kiyashi a jikinsa.
TAFIYAR KIYASHI A JIKI DALILIN RASHIN LAFIYA
Akwai rashe-rashen lafiya waɗanda suke da alaƙa da lakar jiki (neurological illnesses) da za su iya haddasa jin tafiyar kiyashi a jiki. Sun ƙunshi:
1. Parkinson’s disease: Ita ce cutar rawar jiki, wato jikin mutum ya riƙa kyarma. Wani lokaci kuma sai jiki ya sandare ya daina motsi.
2. Dementia: ita ce cutar yawan matuwa da ɗimaucewa.
3. Traumatic brain injury: Shi ne samun rauni a ƙwaƙwalwa sakamakon bugewa ko haɗarin da ya shafi kai.
4. Stroke: Shi ne mutuwar ko kuma shanyewar tsagin jiki. Yana aukuwa a dalilin hawan jini mai tsanani.
5. Meningitis: Shi ne ciwon sanƙarau, wanda yake kama lakar wuya da baya (spinal cord) kuma ya sanya jikin mutum ya sandare.
6. Multiple sclerosis: Cuta ce ta ƙwaƙwalwa da laka, wacce take haifar da rashin gani, kasala, da raɗaɗi a jiki.
7. Huntington’s disease: Cuta ce wacce ake iya gadonta, kuma tana haddasa lalacewar ƙwayayen halittar ƙwaƙwalwa da laka.
8. Delirium: Cuta ce ta ƙwaƙwalwa wacce take sanya rashin magana, rashin barci, gane-gane, da ruɗewa.
9. Chronic liver or kidney disease: Ciwon ƙoda ko hanta wanda ya yi tsanani.
10. Cancer: Ciwon sankara, kamar sankarar jini da sauransu.
11. Infections: kamuwa da ƙwayoyin cuta kamar ciwon sanyi, HIV, ciwon sugar, da sauransu.
12. Ƙarancin jini, da kuma ƙarancin wasu sinadarai a jiki kamar vitamin B12.
13. Perimenopause: Kusantowar ɗaukewar jinin al’ada ga macen da shekarunta suka fara nisa.
TAFIYAR KIYASHI A JIKI DALILIN AMFANI DA ƘWAYOYIN MAGANI
Yin amfani da ƙwayoyin maganin ƙara kuzari ga masu yin wasannin motsa jiki da kuma shan kayan maye kamar cocaine, giya, wiwi, yana iya haddasa jin tafiyar kiyashi a jiki. Waɗannan su ake kira “recreational drugs”, domin ana shan su ne ba domin a magance wata cuta ba, sai domin buƙatar jin tasirinsu kawai a jiki.
Haka nan waɗansu daga cikin ƙwayoyin da ake sha domin magance cututtuka wato “prescription drugs” suna haddasa jin tafiyar kiyashi a jiki. Kaɗan daga cikinsu su ne:
1. Methylphenidate (Ritalin) wanda ake amfani da shi wajen magance matsalar rashin natsuwa (attention deficit hyperactivity disorder – ADHD).
2. Antibiotics kamar ciprofloxacin da clarithromycin wanɗanda ake amfani da su wajen magance cututtukan numfashi (respiratory tract infections), cututtukan mafitsara (urinary tract infections), cututtukan sanyi (sexually transmitted infections), cututtukan narkewar abinci (digestive tract infections), da sauransu.
3. Antidepressants (citalopram, fluoxetine, escitalopram etc.) waɗanda ake amfani da su wajen magance cututtukan damuwa.
4. Corticosteroids (dexamethasone, hydrocortisone, methylprednisolone, etc.) waɗanda ake amfani da su wajen magance cututtukan kumburi.
MAGANCE JIN TAFIYAR KIYASHI A JIKI (TREATMENT OF FORMICATION)
Magance jin tafiyar kiyashi a jiki ya danganta da dalilin da ya haddasa shi. Idan cututtukan ƙwaƙwalwa ne, to, dole sai an ga likitan ƙwaƙwalwa. Idan shan recreational drugs ne ya haddasa shi, to, dole sai an daina amfani da su. Haka kuma idan laulayin shan prescription drugs ne (side effects) ya haifar da shi, to shi ma sai a daina amfani da su, misali ƙaiƙayin da chloroquine ke haddasawa.
Idan kuma ƙarancin sinadarai a jiki ne, to, sai a riƙa cin wadatacce, kuma ingantaccen abinci. Idan kuma wata rashin lafiya ce cikin waɗanda na lissafa a sama, to, sai a magance ta. Idan kuma kusantowar ɗaukewar al’ada ne ya haddsa shi, to, sai a riƙa shafa mayuka waɗanda zas u samar da damshi a jikin fata.
Domin karanta Mutuwar Mata Masu Jego danna nan
Edita@rumasau-kallamu
[…] Don karanta Ƙaiƙayi Mai Kamar Tafiyar Kiyashi A Jikin Mutum danna nan […]