Mene Ne Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)

0
2366

Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria) cuta ce da take damun mutanen duniya, musamman mutanen Afrika, kuma wannan cuta, tana ɗaya daga cikin cututtukan da suke damun mutanen Nigeria. Tana iya shafar yara, manya, tsofaffi, maza da kuma mata.

 Ma’anar Malaria

Malaria cuta ce wadda take saka zazzaɓi da ciwon jiki, waɗanda za mu yi bayaninsu a nan gaba kaɗan.

  • Yadda ake kamuwa da malaria

Asalin abin da yake janyo cutar shi ne shigar wata ƙwayar halitta da ake kira ‘plasmodium’ cikin jinin mutum

Ita wannan plasmodium ba ta shiga jinin mutum kai tsaye, sai ta hanyar sauro. Ma’ana dai, sauro shi ne wanda yake yaɗa wannan ƙwayar halittar (plasmodium).

Shi sauro yana yaɗa wannan cutar ne a tsakanin mutane (daga mutum zuwa wani mutum daban) a yayin da yake neman abinci, wato jini. Ma’ana dai, abincin sauro shi ne jini.

  • Alamomin cutar Malaria

Idan sauro ya ciji mutum, kuma ya saka masa wannan plasmodium ɗin a cikin jininsa, to ba a lokacin zai fara jin alamun ciwon ba, har sai bayan wasu kwanaki.

Alamomin ciwon sun haɗa da:
  • Zazzaɓi
  • Ciwon kai
  • Jiki yana ciwo
  • Gaboɓi suna ciwo
  • Kasala
  • Amai
Idan ta yi tsanani, za ta iya haddasa:
  • Fita daga hayyaci
  • Jijjiga
  • Ƙarancin jini
  • Rasa rai….Da sauransu

Hanyoyin kariya daga cutar malaria 

Kamar yadda aka yi bayani a baya, ita wannan cuta dai sauro ne yake yaɗa ta. Don haka duk wata hanya da mutum zai bi don yaƙar sauro, to wannan hanyar za ta iya kare shi daga samun wannan cutar.

Waɗannan hanyoyi sun haɗa da:

(1) Hana sauro haihuwa

(2) ka hana sauro ya cije ka (ya sha jininka)

(3) Kashe sauron.

Hana sauro haihuwa:
  • Gyara kwatoci: A daina barin ruwa yana zama a cikin kwatoci ba tare da yana gudana ba. Sannan kuma a rufe kwatocin.
  • A daina barin ruwa ya daɗe a buɗe a cikin muzubi.

Yadda zaka hana sauro ya cije ka:
  • Amfani da gidan sauro (wato Insecticide Net): Ma’ana kwana a cikin gidan sauro.
    Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)
    Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)
Yadda za a kashe sauro:
  • Amfani da maganin sauro na fesawa ko kuma na hayaƙi.
  • Abin da ya kamata mutum ya yi idan ya ji alamun cutar.

(1) Idan akwai zazzaɓi, musamman a yara ƙanana, to sai a samu tsumman zani ko tawul a tsoma shi a ruwa (ba ruwan zafi ba, ba kuma ruwan sanyi ba), kamar dai ruwan fanfo.

Sannan sai a matse ruwan, sai a cirewa yaron rigar sa, sannan sai a riƙa ɗan daddana jiƙaƙƙen tsummman a jikin yaron (ko’ina da ina) musamman inda ya fi zafi. Za a yi ta maimaita haka, har sai jikin ya yi sanyi (zazzaɓin ya sauka).

(2) Ai maza a garzaya asibiti.

Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)
Zazzaɓin Cizon Sauro (Malaria)
Abubuwa masu mahimmanci:

Malaria daban, Typhoid daban. Zan yi bayanin zazzaɓin Typhoid nan gaba.

  • Amma dai yakamata a sani cewa:
  • Malaria ba ɗaya take da Typhoid ba
  • Typhoid ya yi ƙaranci a cikin al’ummarmu matuƙa da gaske musamman idan aka kwatanta ta da Malaria.
  • A guji yin allura da zarar ana zazzaɓi. An fiso asha ƙwayar magani idan ana zazzabi saboda yin allura kan iya haifar da wasu matsalolin.
  • A guji yin allurar jijiya idan ana yin zazzaɓi. Allurar jijiya tana da haɗari ƙwarai da gaske. Tana iya haifar da matsaloli iri daban-daban. Idan aka yi kuskure, mutum zai iya rasa ransa.

Sai an samu ƙwaƙƙwaran dalili, likita yake umarni a yi allurar jijiya, kuma idan za a yi, to sai ƙwararren me yin allura ne zai yi (Nurse ko likita).

Kammalawa.

Cutar zazzaɓin cizon sauro(malaria), cuta ce da ta addabi mutanen Africa. A kowane lokaci ko kuma daƙiƙa sai an samu wanda ya mutu ta dalilin cutar malaria.

Don haka mu kare kanmu daga kamuwa da wannan cuta sannan kuma mu guji yin allura (ta jijiya da ta tsoka) da zarar an fara zazzaɓi

karanta yadda ake kare kai daga ciwon sanyi (toilet infection) ko Mene ne taifud (TYPHOID) ko mene ne zazzaɓin cizon sauro (MALARIA) danna koren rubutu

labarin da ya wuceYadda Ake Bread-egg Toast A Sauƙake
Labarin na GabaMene Ne Taifud (TYPHOID)
Dr. Adamu Bala
Sunana Dr Adam Bala Husaini, likita da yake aiki a sashin lafiyar iyali (Family Medicine), a asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital, Kano Nigeria. Kuma shugaban sashin lafiya na wikiHausa