Yadda Maguzawa Suke A Taƙaice

0
44

Muhammad Sahal Aliyu

SHIMFIƊA
Hoton rayuwar wata al’umma takan fito cikin ayyukan adabi wanda adabin Hausa bai keɓanta ba. Hakan na faruwa ne idan marubuci ya taɓa jin labari, ko gani, ko karanta wani aiki da ya shafi wannan al’umma. Wani lokaci kuma zamantakewa ke kawo nason rayuwar wasu al’ummomi na kusa ko na nesa cikin aikin adabi.

Idan kuwa ba haka ba, hoton rayuwar da aka gani wadda marubuci ke bayani; yana yiwuwa jinin marubuci ne da ke da asali tun daga iyaye da kakanni. Kenan asalin marubuci yana iya tasiri cikin rubutu har a ga hoton rayuwar magabata ta kusa ko nesa na mai rubutu, ya sani ko bai sani ba.

MAGUZAWA

Maguzawa Hausawa ne na asali da ke zaune a ƙasar Hausa tun da daɗewa. Tarihin Hausa da Hausawa ba zai kammalu ba sai an ambaci Maguzawa domin ba su da wani harshe sai Hausa.

HALAYYA DA ƊABI’UN MAGUZAWA

Wayo: Wayo yana ɗaya daga cikin ɗabi’ar Maguzawa (Abdullahi, 2008:4). Ana iya gane wayon Bamaguje idan aka yi mu’amala da shi, ko aka ji labarin wani abu da ya faru tsakaninsa da wani. A labarin Ɗan hakin da ka raina na cikin littafin Magana Jari Ce na uku, an nuna cewa Maguzawa mutane ne masu wayo. Ga dai abin da Anunu Mahauci da abokansa suke cewa:

Suka hanga, guda ya ce , Bahaushe ina? Kuna ganin Bamaguje, ku dubi irin kayan gogan mana, iya magana yanzu nan ko ɗan Kano. Daga nan sai guda wanda ake kira Anunu ya ce : “Haba wane wayo ke ga Arne, daga dai an ƙyale su”. Guda ya ce: A! don wayo dai suna da shi. A nan Anunu da abokansa sun tabbatar da cewa duk wani Bamaguje yana da wayo. To amma dai haɗuwarsu a wannan wuri an yi wa Bamaguje hikima an cuce shi.

Shi kuwa marubucin littafin Malam Inkuntum, ya nuna wayon Maguzawa ne a wurin da ya ambaci wani Arne da ke neman bawan Allah wanda zai ba ɗiyarsa a matsayin miji. Arnen ya gwada wayonsa ga wasu musulmi da cewa:

Arne:Kai! Bawan Allah ne kai in kashe ka maimakon nawa da ya kashe jiya.
Ladan : Lallai ni kam bawan Allah ne. In ka kashe ni ka kashe bawan Allah.
Arne: Kashe ka fa zan yi yanzu, ko ƙyaftawa babu.
Ladan: Ai ta samu gare ka. Allah ya ba mu cikawa da imani, mu tashi da imani, amin.
Arne: (ya mai da gatarinsa a kafaɗa, ya kama hannun Ladan ) Zo mu je gidana , kuma kwantad da zuciyarka, ba kashe ka zan yi ba.

Wannan misali ya nuna wayon da Arne ya yi amfani da shi domin ya tantance wanda zai ba ɗiyarsa aure. A ɓangaren su Anunu da Bamaguje kuwa, cutar da Anunu ya yi wa Bamaguje ya rama ta hanyar ɓad da kama kamar haka:

To Bamagujen nan ya yi kamar ya ƙyale, sai da ya bari an yi kamar kwana ashirin har an bar wannan Magana, sai ran nan ya sami kayayyaki farare irin na Hausawa ya sa, ya nemi rawani ya bayar aka naɗa masa. Bamaguje ya nufi wajen Anunu ya tarad da shi da kan akuya yana sayarwa. Da zuwansa sai ya dafa kan Anunu, ya dubi kan akuya ya ce: “wannnan kan nawa ne?” Anunu ya ciro ido ya dube shi ya ce: “ Mene ne kuma na dafa mini kai? Ku dai Malamai kun raina mu..To ga shi nan faɗi abin da za ka biya.

Nan ma wayo Bamaguje ya yi wa Anunu domin ya dafa kansa a matsayin kan akuyar da ake ciniki. A ƙarshen wannan ciniki dai sai da aka dangana da gaban alƙali. Ko da alƙali ya ji duk yadda aka yi tun lokacin da Anunu ya sayi San Bamaguje har ya zuwa cinikin kan akuya, ya san cewa, Bamaguje ya rama abin da aka yi masa ne. Ga shi kuma Bamaguje ke da gaskiya, don haka a ƙarshe dai Anunu ya yi hasara fiye da wadda Bamaguje ya yi lokacin da aka sayi Sansa.

MUHALLIN MAGUZAWA

A duk inda Maguzawa suke, sun fi son su zauna cikin daji, wato nesa da gari ba tare da mutane sun tsangwame su ba. Wannan ya sa suka ba noma muhimmanci a rayuwarsu fiye da duk wata sana’a. Cikin littafin ƙarshen Alewa Ƙasa marubucin ya yi bayanin muhallin Maguzawan Tsaunin Gwano da cewar:

Wannan gari na Tsaunin Gwano yana da gidaje kamar guda ɗari biyu. A gefen garin akwai wani dogon tsauni wanda ta wajen ne garin ya sami suna. A da can ‘yan shekaru kaɗan da suka wuce dukkansu suna zaune a kan tsaunin nan ne. Wannan kuwa ya faru ne saboda tsoron masu harin bayi suna sayarwa. Nan ma nuni ne da muhallin Maguzawa tun lokacin da suke a saman duwatsu, har ya zuwa saukowarsu daga duwatsu, kuma a cikin daji.

SANA’O’IN MAGUZAWA

-Noma
-Ƙira
-Farauta

NOMA

Sana’ar da ta fi kowace muhimmanci wajen Maguzawa ita ce noma. Ita suka gada kaka da kakanni, da ita suke alfahari fiye da komi a duniya, (Abdullahi 2008). Ya ƙara da nuna baya ga noma Maguzawa suna da wasu sana’o’i irin su: ƙira, da farauta, da kiwo. Hoton sana’o’in waɗannan mutane sun fito cikin littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa inda marubucin yake bayanin yekuwar farautar shekara da za a yi kamar haka :

“Hyai, hyai! Ina mazajen Tsaunin Gwano, Sarkin Ƙira ya gaishe ku. Bayan gaisuwa ya ce a faɗa maku lokaci ya yi wanda duk mai ji da kanshi ya shirya….” Wani Saurayi wanda ake kira Mailoma yana zaune a kan wani buzu da aka yi da fatar biri ya miƙo hannu suka tafa. Sai ya yi wuf ya miƙe gaban hantsi yana gyaran lagen gwadonsa.

Ya ce bara kuwa an yi farauta da sa’a. Ka tuna lokacin da muka darkaki ƙatuwar Barewar nan? Shi wannan ɗan tsoho sunansa Ci-wake. Duk garin Tsaunin Gwano da kewaye an san shi da yin jima. Wannan sana’a da yake yi ta sa a kullum ba ya rasa abin yin kayan miya.

Waɗannan misalai sun kawo hoton sana’o’in Maguzawa da suka ƙunshi farauta, da jima. To amma ba waɗannan sana’o’in ba ne muhimman sana’arsu ba kamar yadda ya zo cikin littafin , noma shi ne babbar sana’arsu.

Shi kuwa labarin Ɗan Hakin da ka Raina na cikin Magana Jari Ce ya nuna cewa noma da kiwo suna daga cikin sana’o’in Maguzawa. Farkon labarin ya fara ne da bayanin sana’ar Maguzawa kamar haka: Wata rana wani Bamaguje ya lafta wa takarkarinsa hatsi, ya kora zai kai kasuwa. Kasuwar da za shi kuwa ana ɗam mudu ƙwarai, don kullum in ya kai kayan takarkarin nan, daga ya sayar sule talatin sai ya sayar talatin da biyar.

Haka ma a cikin littafin Malam Inkuntum, lokacin da Arne ya je neman bawan Allah, ya nuna cewa shi manomi ne inda ya ce:
Arne:Kai tsaya tambayarka zan yi. Akwai mutane cikin akurkin nan naku?
Malam Almu: Ai tukuna. Yanzu dai muke harama. Anjima kaɗan za a taru. Sallar za ka yi yau?
Arne: Tir! Me ya kai ni wannan abin duƙe-duƙe ba wurin noma ba.
Wannan Arne ya nuna babu wani abu da zai sa ya dinga wasu duƙe-duƙe in dai ba wurin noma ba. A ganinsa wurin noma ake yin duƙe-duƙe a nasa tunanin.

SUNAYEN MAGUZAWA

Suna shi ne kalmar da ake amfani da ita wajen kira ko ambato ko wani abu, (Ƙamusun Hausa 2006:401). Akwai abubuwa da dama da kan ba da haske wajen sa wa yaro ko yarinyar da aka haifa suna.

Cikin irin waɗannan abubuwa akwai: yanayi, da halin haihuwa, da yanayin haihuwa, da siffar mutum , (Yahaya 1979:5-8). A wasu lokuta kuma, akan sa sunan wata dabbar daji ko ta ruwa a matsayin suna ga Maguzawa. Wasu daga cikin sunayen gargajiya da aka yi amfani da su cikin waɗannan littattafai guda uku su ne :

Arne: Wanda ke yin tsafi, kuma ana kiran Maguzawa da wannan suna.
Bamaguje: Suna ne na namiji tilo mai bin addinin gargajiya na Hausa.
Dubu: Wadda aka haifa lokacin da ake yin bikin dubu da tambarci.
Hantsi: Yaron da aka haifa lokacin da rana ta fito kafin ta kai tsakiya
Juda: Suna ne na wata dabbar daji mai kama da Mage. Ana samun turare daga wasu sassa na wannan dabba.

Maguzawa: Jam’i ne na kalmar Bamaguje
Malka: Ita ce Yarinyar da aka haifa lokacin da ruwan damina ya kai tsakiya.
Sarkin Arna: Shugaban Maguzawa kuma mai jagorancin bautar gargajiya.
Sarkin Dodanni: Abin bautar gargajiya ne.
Sarkin Noma: Mai yin jagoranci wajen harkokin noma.
Sarkin Tsafi: Mai yin jagoranci wajen tsafi.
Tayani: Sunan abin zama ne wanda aka saƙa da kaba tare da fatu, mata suke kaɗi kansa.
Tamu: Suna ne da ake sa wa yaron da aka haifa shekarar da gyaɗa ba ta yi kyau ba.

MAGUZANCI

Maguzanci a Wasu Rubutattun Littattafan Adabin Hausa:
Imani da tunanin Maguzawa na gargajiya shi ke jagoranci wajen tafiyar da harkokin rauwarsu. Wannan shi ne abin da ya bambanta Maguzawa da sauran ‘yan’uwansu Hausawa. Wannan fasali ya dubi wasu ɓangarori cikin imani da tunanin Maguzawa a gargajiyance da suka haɗa da bautar gargajiya, da cin mushe da sharholiya, da zagi da batsa da dai sauransu.

Bautar Gargajiya:

Bauta da abin bauta a wajen Maguzawa suna da muhimmancin gaske, don haka suke kiyayewa da mutunta duk wani abu da ya shafe su. A tsarin bautar Maguzawa, akwai abin da ake yi wa bauta, da wurin bauta, da hidima ga abin bauta, da kiyaye dokokin abin bauta, da kuma sakamakon da ake samu ida an saɓa ma abin bauta.

Abin Bauta:

Addinin Maguzawa addini ne na gargajiya ne da suka gada wajen iyaye da kakanni. Hanyoyin bautar Maguzawa su ne tsafi, da bori, da mu’amala da dodo. Abubuwan da suke bauta ma kuwa su ne Aljanu, da Dodanni, da wata dabba da sukan keɓe, ko wani itace. Aljanu su ne abubuwan da suka fito a matsayin abin bauta cikin wannan aiki.

Misali, a rigimar Bamaguje da Anunu Bamagujen na cewa:
Da ni dai na fi son kan da kome , don in kai wa gunkinmu ya sha jini.
Bayanin wannan Bamaguje ya nuna cewar gunki yake bauta ma, amma ba gunkin ba ne aljani yake nufi domin gunki ba ya shan jini. Shi kuwa littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa Aljani ne aka ambata a matsayin abin da suke yi wa bauta.

Kodayake an ce yakan fito cikin siffar maciji ko wani abin daban, amma dai Aljani ne. An bayyana shi da cewa:
Wannan surin yana ƙarƙashin wata babbar tsamiya ce …… Sarkin Arna da jama’arsa Talakawa sun yarda cewa wai a cikin wannan surin akwai wani tsohon Aljani. Shi wannan Aljani an san shi a cikin siffar maciji, ko da yake an ce kuma ba abin da ba ya rikiɗa.
Shi ma wannan ya nuna babu tsayayyar sifar da abin bautar yake da ita, sai dai a iya cewa ya fi bayyana cikin sifar maciji.

Ana iya samun jinsin mata cikin aljanun da ake yi wa bauta kamar yadda Arnen cikin littafin Malam Inkuntum ya ce:
Ladan: Na ji na yarda, amma ina so a ɗaura aure.
Arne: Ku yi can ruwa ga wuya, in ji mata. Ai ni tun da Uwar Dawa (aljana) ta yi mini izini, iyakar nawa ke nan. (arne ya koma gida).

Wurin Bauta:

Maguzawa ba kamar sauran mutane ba, sukan keɓe wani wuri na musamman domin yin bauta. Duk wurin da suka keɓe suna yin bauta nan ne mazaunin da abin bautar tasu yake. Suna kula da wurin fiye da makwancinsu ta fuskar tsaftacewa, da ba wurin kariyar da ta dace musamman ga wanda bai san darajar wurin ba. Irin wannan wuri na iya kasancewa ɗaki a cikin gida, ko bishiya a ƙofar gida ko bayan gari.

Misali cikin littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa an ambaci wurin bauta da cewa:
Ita fadar Sarkin Dodanni wani irin wuri ne inda yake da wani irin babban shuri wanda girmansa ya kai tsawon mutum uku dogaye. Wannan shurin yana ƙarƙashin wata babbar tsamiya ce, kuma a kowace rana Sarkin Arna yakan sanya yaran shi su share wurin nan fes. Lallai wannan wuri ya amsa sunansa wurin bautar gargajiya na Maguzawa kasancewarsa bayan gari, kuma ga shuri jikin bishiyar tsamiya. Wanda ake sharewa a duk safiya.

Hidima ga Abin Bauta:

A tsarin bautar gargajiya ana yin hidima ga abin da ake yi ma bauta. Hidimar da ake yi ta haɗa da tsaftace wurin, da yin yanka ga abin bauta, da sagale ƙasusuwan dabbar da aka farauto, da yin kyautar mutum ko dabba ga abin bauta. Cikin labarin Bamaguje da Anunu na Magana Jari Ce , an nuna inda Bamaguje ya so a bari ya yanki Anunu domin Gunkinsu ya sha jini. Bamagujen na cewa: Da ni dai na fi son kan da kome, don in kai wa gunkinmu ya sha jini.

A littafi Ƙarshen Alewa Ƙasa kuwa, an yi bayanin hidimar da ake yi wa abin bauta kamar haka: A kowace shekara Sarkin Arna yakan zo ya yi sujada, kuma ya kawo wa Sarkin Dodanni ‘yar gaisuwarsu. Irin gaisuwar da Sarkin Arna ke kawo wa tana da nauyi ƙwarai. Wato kyautar da ake yi ita ce rai guda na mutum. Ita ma wannan hidima masu gudanar da bautar sun gaje ta ne tun iyaye da kakanni ba sai cikin wani labari ba.

A wajen wasu Maguzawan kuwa, ba sa bayar da ran mutum sai na dabba. Bayanin Maguzawan garin Jinjin Wawa na cikin Ƙarshen Alewa Ƙasa ya tabbatar da haka:
Jinjin Wawa wani gari ne wanda shi ma girmansa kamar na Tsaunin Gwano yake. Suna da Sarkinsu na tsafi, to amma shi ba a ba shi ran mutum sai na dabba.

Sakamakon Saɓa Ma Abin Bauta:

A duk lokacin da ake gudanar da bauta a Maguzance, ya zama wajibi a kiyaye tare da mutunta wannan abin bauta. Idan ba haka ba za a ga sakamako wanda ba daɗi. A lokacin da Mailoma ya yi karambanin zuwa fadar Sarkin dodanni ya aikata abin da ba a yi kamar haka:

Da yake wannan yaro ba ya cikin hankalinsa, ko tufafinsa bai tuɓe ba. Da ya ji tarin ya ƙi tsakaitawa sai ya tura ɗan yatsa a maƙogwaro ya yiwo aman giya a kan shurin nan. Yace ma shuri, “sha mana” Ya sake kecewa da dariya. Wannan rashin kunya da Mailoma ya aikata ga Sarkin Dodanni na daga cikin abin da ba a yi a wurin tsafinsu. Yin haka kuwa kan haifar da mummunan sakamako ga wanda ya aikata.

A dalilin wannan rashin kunya da Mailoma ya yi, wasu abubuwa sun faru da shi kamar haka: Ai wannan babu shakka cizon maciji ne, don kuwa ga alamar ɗan jini da kuma shaidar haƙora. Maciji? Aha ga amsa a fili. Nan take ya fusata ya yi ruri cikin dajin nan yana kira, MACIJI. MACIJI! SARKI. SARKI! Kai ne ka cinye Tayani.

Zagi Da Batsa:

Zagi shi ne faɗa wa mutum baƙar magana ko bacin iyayensa, (Ƙamusun Hausa 2006: 487). Zagi wani ɓangare ne cikin lafuzzan ɗaurin auren Maguzawa wanda a wasu lokuta yake zuwa surke da batsa. Maguzawa suna sanya zagi cikin lafuzzan ɗaurin aure domin wanda yake da niyyar ƙalubalantar ɗaurin aure idan ya tuna girman zagin, da kallon da jama’a za su yi masa ya fasa, (Abdullahi 2008: 5-7).

Ko ba wurin ɗaurin aure ba Maguzawa sukan yi ashar cikin magana ta yau da kullum, ko da kuwa zagin surke yake da batsa. A irin wannan yanayi, ba sa jin nauyi ko kunyar wani don sun yi irin waɗannan kalamai. Misali an sami zagi cikin litttafin Ƙarshen Alewa Ƙasa a yayin da Mailoma yake yin kirari kamar haka:

“Ni ne na bara ni ne na bana
Mijin Tayani dogon yaro
Samun irinku sai an tona
Yaro ko kana musu in ci ubansa”.

Haka kuma Mailoma ya sakeƙunduma wani ashar ɗin lokacin da matarsa ta sheda masa tana da juna biyu inda ya ce:
“ Sai ni Arne tsaran manya na Chiwake da Tayani.
Yaro ko kana shakka ne yanzu in ci ƙundun durin uwarka .

Batsa ita ce maganar banza musamman wadda ta danganci ambaton al’aurar mace ko namiji. Ga Bamaguje, batsa ta zama jiki, domin tana cikin lafuzzan ɗaurin aurensu. A maganganun yau da kullum, al’ummar Maguzawa ba sa jin kunyar yin batsa. Haka ma a littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa batsa ta fito a wannan wurin kamar haka:
Dutsen niƙa: Kakir-kakir
Malka: “Ba ruwan ka da yaron kowa”
Malka ta sake maimaitawa.
“Ba ruwan ka da yaron kowa
To, zagayo ka ci gutsu,
A hankali ba da garaje ba”.

Batsar da ke cikin wannan zance na Malka tana ƙunshe da kalmomi waɗanda idan ba Bamaguje ba, babu wanda ke iya faɗi ba tare da jin kunya ba. Dalili kuwa, an ambaci al’aurar mace ba tare da jin kunya ba.

ABINCIN MAGUZAWA

Cin Mushe:
Hausawa na cewa: “kyawun Bamaguje ya ci mushe”. Mushe shi ne naman wata dabba ko tsuntsu da ya mutu ba tare da an yanka ba. A wurin Maguzawa dabba ko tsuntsu da ya yi mushe nama ne mai kyau. Wasu Maguzawa da aka kira da sunan Filani cikin littafin
Malam Inkuntum, an nuna cewa sun ci mushen Biri a cikin daji kafin su iso gari.

Marubucin na cewa:
Ana ta rawa da waƙa sai ga waɗansu Filani su uku sun fito daga cikin daji. Ashe sa’ad da suke can daji yunwa ta kama su har sun tarad da gawar bika sun gasa namansa sun ci. Sun yi wa juna alƙawarin ba wanda zai faɗi wannan magana har abada. Ko kafin su iso nan ƙishirwa ta kama su ƙwarai da gaske. Sai kuma suka ji durin kiɗa ake yi, suka tona asirinsu.

Bafillace na Farko: Ho ɗan kare da ba da ƙishirwa
Bafillace na Biyu: Hala kana so ka faɗi.
Bafillace na Uku: He, ku faɗi, mun ci biri, mun ci biri, mun ci biri.

Shan giya

Sharholiya ita ce yin abubuwa na jin daɗin rayuwa da nufin more rayuwa da shaƙatawa. Abubuwan sharholiya ga Bamaguje su ne shan giya, da wasanni, da auren mata da yawa, da yin bukukuwa, da sha’awar doki, (Abdullahi 2008:5) Daga cikin waɗannan ɗabi’un, giya ita ce ta mamaye littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa. A farkon littafin an fara zancen giya lokacin da ake sanarwa domin gayyatar farauta da cewa:

Hantsi ya ajiye ƙoƙon da ya gama shan burkutu da shi, ya yi wata doguwar miƙa ya yi murmushi. Hantsi ya ƙara ciko ƙoƙonsa da giya ya ce: A wannan rana duk tsawon rai na ba zan iya mantawa da ita ba. Lallai da ban sa baki ba da ai da kun yi ɗanyen aiki, ya miƙo masa giya cikin ƙoƙo, Mailoma ya karɓa.

Ko da yake yin wannan sanarwa, waɗannan samari suna cikin sharholiyarsu ne da giya. Wannan ya nuna cewa rayuwa ba ta gudana wurin Maguzawa sai da giya, kuma wa da ƙani suna iya haɗuwa su sha ba tare da sun ji komi ba. A lokacin da Mailoma ya je yi ma Juda gaisuwar ɗansa, an nuna cewa ko a nan sai da ya sha giya ya yi tatul har aka ba shi wadda ya yi guziri da ita. Juda ya fara bayani da cewa:

Ku kawo masa giya nan, hankalin yaron nan ya tashi.” Ku yi sauri mana ku zubo, ka bar kukan nan.” Bayan an zubo giya a ƙoƙo sai aka miƙa wa Mailoma don ya sha. Ya karba.
Bayan da Mailoma ya ƙare zaman gaisuwa, sai ya yi sallama da jama’a ya nufi ƙauyensu. Ko da yake dai shi ya yi sallama da mutane, amma a gaskiya bai san lokacin da ya yi ba.

Giyar da ya ɗirka da kuma naman da ya ci duk sun yi masa babakere a ciki. Ga shi saboda buguwar da ya yi har da ƙyar yake iya takawa. Kuma tun lokacin da ya zauna gindin su Manje mai kukuma yake ɗaukar ƙoƙo bisa ƙoƙo na burkutu, wanda ma ba ya ko ɗan saurarawa domin ya huta. Ya tinkaro hanyar Tsaunin Gwano da wani goran giya mai girma a hannunsa.

Wannan kyauta ce wadda Juda ya yi masa saboda ba a samu wani wanda ya kama ƙafansa wajen shan giya ba. Kusan kowane lungu da saƙo na rayuwar Maguzawa, giya ba ta rasa gurbi. Idan kuwa babu wata hidima, to haka nan ma sukan sha domin annashuwa.

NAƊEWA

Haƙiƙa adabi ba ƙaramin tanadi ya yi wa rayuwar Maguzawa ba, ya kuma haskaka mana rayuwar Maguzawa. Kenan hoton Maguzawa da Maguzanci cikin wasu littattafan adabi, rayuwa ce ta wata al’umma da wasu marubuta suka ƙyallaro cikin fasaharsu a rubuce.

MANAZARTA

Abdullahi, I.S.S. 2008. Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa. Kundin Digiri Na Uku. Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato..
Abdullahi, I.S.S 2008. “Bamaguje da Ɗan Akuya: Rashin Ƙauna Ko Ƙiyayya?” Departmental Seminar Series, Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.
Abdullahi, I.S.S 2012. “Falsafar Ɗaurin Auren Maguzawa”. Muƙalar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani a Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Karanta Gudunmawar Ali Gumzak Wajen Samarwa Da Kuma Haɓaka Finafinan Hausa

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceGudunmawar Ali Gumzak Wajen Samarwa Da Kuma Haɓaka Finafinan Hausa
Labarin na GabaMatakan da Iyaye Za Su Bi Don Kare Tarbiyyar ‘Ya’yansu A Intanet