Askin sarauta na nufin askin da ake yi wa sarakuna ko wasu masu riƙe da sarauta a ƙasar Hausa. Ga al’ada ba kowane wanzami ne yake yi wa sarki aski ba, kowane sarki yana da wanzamin da yake yi masa aski, kuma wannan wanzami shi ne sarkin aska ko magajin askar wannan sarki.
Kowane sarki akwai ranar da yakan keɓe wadda ake yi masa aski. Mafi yawancin sarakuna an fi yi masu aski a ranar Litinin ko Talata. Dalilin da ya sa ake ware waɗannan ranaku shi ne, shi wanzamin ya san da wannan rana da kuma lokacin da zai riƙa zuwa, to a ranar ba zai yi tafiya zuwa wani wuri ba domin kar ya saɓa. Wasu kuma suna yin aski a waɗannan ranaku ne saboda camfe-camfe.
Kuma kowane sarki yana da askar da ake yi masa aski wadda ba a yi wa kowa aski da ita sai shi. Sai kuwa idan bayan rasuwarsa a ci gaba da yi wa wanda ya gaje shi aski da ita. Bugu da ƙari, ba a kowane wuri ake yi wa sarki aski ba, sarkin askarsa ko magajin askarsa yake tarar da shi a gidansa ya kai shi bargarsa domin ya yi masa aski. Dalilin da ya sa ake bin waɗannan sharuɗɗa na yi wa sarakuna aski shi ne, domin kariya daga maƙiya kar su harbe su, ko su yi masu wasu surkulle ta hanyar aski da zai yi dalilin su rabu da sarautunsu ko wani sharri ya same su, ko rashin lafiya, ko ma dai su mutu.
Game da ladar da sarakuna suke biyan wanzamansu bayan sun gama masu aski, ba a lokacin da suka yi askin suke biyansu ba. Su sarakuna a lokacin da suka bukata sukan aika wa sarakunan askarsu da kyauta mai yawa. Ire-iren kyaututtukan da sarakuna kan ba sarakunan askarsu sun haɗa da manyan riguna da kuɗi da abinci (gero da dawa da makamantansu) da dawaki. Haka idan wani biki na aure ko na haihuwa ya sami wanzamin sarkinsa kan taimaka masa sosai.
Aski da Gyaran Fuska
Aski na nufin amfani da askar aski mai kaifi domin a aske sumar da ta tsiro a kan mutumin da ya bukaci a yi masa askin.A ƙasar Hausa masu yin sana’ar aski ana kiransu da sunan wanzamai. Gyaran fuska na nufin amfani da irin askar da ake yin aski domin aske gashin da ya tsiro a fuskar mutumin da ya bukaci a yi masa gyaran fuska.A al’adar Hausawa maza ne kawai ake yi wa aski da gyaran fuska.
Ga kuma wanda ya ajiye gemu sai a gyara gemun ya fito sosai. Gyaran fuska yana da matuƙar muhimmaci ga rayuwar Hausawa, domin kuwa ana kiran wanzamai yin gyara saboda masu gashi da yawa ko ƙasumba su ji daɗi ga fuskarsu. Ga wasu suna nuna, idan gashi ya tsiro masu a fuska yana yi masu ƙaiƙayi sosai har sai in an aske shi sannan za su ji daɗi ga fuskarsu.
Akwai aski iri daban-daban da ake yi wa Hausawa, kuma kowane daga cikinsu akwai dalilan da kansa a yi shi. Ire-iren waɗannan aski sun haɗa da askin ƙwaryar molo da gyaran fuska da askin sarauta da askin jarirai na suna da askin tuba da zanko da tukkaye da bawale da askin muzantawa da kuma tsayar da gemu.
Askin Ƙwaryar Molo
Askin ƙwaryar molo aski ne wanda ake yi wa Hausawa da wasu al’ummomi. A irin wannan aski ana aske dukkan suma ne tas har idan rana ta haskaka kan wanda aka yi wa askin sai mutum ya ga kan yana ƙyalli. Idan za a yi askin ƙwaryar molo da fari ana fara jiƙa sumar da ruwa sai ta jiƙa sosai daga nan sai a bi da sabulu domin ta ƙara laushi.
Yana da muhimmanci a fahimci cewa, duk sumar da ba ta jiƙa da ruwa sosai ba, idan aka yi saurin shafa sabulu, ba za ta yi laushi kamar wadda ta jiƙa sosai ba. A irin wannan gaggawar ce za a tarar idan ana yi wa mutum aski zai ce da zafi. Idan ta jiƙa sosai aka shafa sabulu ta fi sauri da daɗin aski ga wanda yake yin askin da kuma wanda ake yi wa.
Bayan suma ta jiƙa, sai a fara aski daga ɓangaren fuska kusa da kunnen dama a nufi wajen ƙeya. Ana bi ana askewa tare da la’akari da bin kwanciyar sumar, wato ana bin yadda sumar ta kwanta ba tare da tarbar kan gashin ba. Idan an aske dukkan gashin da yake baya, sai a juyo tsakiyar kai a nufo wajen goshi domin shi ma a aske shi.
Bayan duk an aske gashin da yake bisa kai, sai a sake shafa ruwa domin a maimaita askin tare da bin hanyoyin da aka bi lokacin aka fara yin askin.Haka kuma idan babban mutum ne mai gashi a fuska, sai kuma a yi masa gyaran fuska.
A’al’adar Hausawa askin ƙwaryar molo yana da muhimmanci sosai, domin kuwa al’ada ta mayar da shi dole, har ma Hausawa a da can sun ɗauka dukkan wanda ya bar suma da yawa bisa kansa tamkar mahaukaci ne, mai yin koyi da ɗabi’a marar kyau. Wannan ne ya sa iyaye kan tilastawa ‘ya’yansu yin askin ƙwaryar molo, wasu ‘ya’yan ba cikin suna buƙata ba. Maroƙan Hausawa na gargajiya suna yi wa wanzamai kirari kamar haka:
“In ba domin ku ba,
Da mahaukata sun yi yawa”
Ma’ana, in ba don wanzamai suna yi wa mutane aski ba, da yawan mutane masu gashi duguzun kamar mahaukata sun yi yawa cikin duniya.
Askin Jarirai na Suna
Askin jarirai na suna shi ne askin farko da ake yi wa jarirai bayan an haife su, ana yi wa jarirai maza da mata aski. A al’adar Hausawa ana yin wannan aski a ranar da aka raɗa wa jaririn suna. A da can kafin zuwan addini Musulunci a ƙasar Hausa ana yin wannan aski ne a lokacin da dangi na wajen uba da dangi na wajen uwa suka taru domin raɗa wa jariri suna.
Misali, a al’adar Kaina-Fara Arnan Birci da suke zaune a Ƙauyen Goda ta Birci a Ƙaramar Hukumar Kurfi ta Jihar Katsina, sai jariri ya kwana arba’in da haihuwa sannan za a yi masa aski, kuma a wannan rana ne za a raɗa masa suna. A halin yanzu ana yi wa jarirai askin suna a rana ta bakwai da haihuwa. A wasu ƙauyuka ana yin askin jariri da maraice lokacin da dangi mata na wajen wadda ta haihu da dangin wanda ya haihu duk sun haɗu a wannan lokaci ne wanzami zai yi askin. Dalilin haka kuwa shi ne, don kowa ya ba da tasa gudummuwar wajen yin askin
Dangane da ladar da ake biyan wanzami idan ya yi askin jariri na suna za mu ga a gargajiyance a ƙasar Hausa kafin samuwar kuɗin zamani ana biya ne da hatsi da dabbobi da kuma tsuntsayen gida irin su kaji. A nan dangin masu haihuwa na maza da na mata duk suna ba da nasu ga wanzamin.
Bayan an gama aski sai a fitar da kushekara ko karfata daga ragon suna a ba wanzamin. Daga nan kuma sai a ba wanzamin ƙwaryar aski. Dukkan waɗannan kayayyaki da ake ba wanzami, Hausawa sun ɗauka ba su biya shi ladan aikin da ya yi ba, domin in ba shi ba, babu mai iya yin ayyukansa. Wannan dalilin ne ya sa ake haɗa wa wanzami dukkan waɗannan kayayyakin abinci, saboda kar rashin abinci ya sa shi tafiya neman abinci, haka ka iya jawo idan an haihu aka zo neman sa ba za a same shi ba, don ya tafi neman abinci.
Tukkaye
Tukkaye ana yin su ne bisa kan yara maza ɗaya-ɗaya. Abin nufi a nan shi ne, su tukkaye ana barin gashi a lokacin da ake aski kaɗan-kaɗan a wasu wurare bisa kan yaron da ake yi wa aski waɗanda a mafi yawancin lokaci ba a aske su sai lokacin da za a yi wa yaro kaciya. Wasu tukkayen kuwa manya ne, waɗanda masu wasan fage suke sanyawa a yi masu domin kwalliya a bisa kawunansu.
Ire-iren masu wasan fagen da suke yin tukkaye sun haɗa da ‘yan kokowa da ‘yan dambe da ‘yan kwarako da ‘yan dadale da gardawa da sauransu. Su tukkaye da ma can asalinsu na Hausawa ne, sauran baƙi da suka shiga cikin Hausawa su ma sun zo da irin nasu tukkaye, misali, Buzaye da a yanzu sun koma Hausawa, ana yi wa ‘ya’yansu tukkuwa ɗaya a bisa ƙeya, har sai ta kai ga matakin da gashin tukkuwar ya yi tsawo sai a yi masa kitso.
Shi ma ba za a aske shi ba sai lokacin da za a yi wa yaron kaciya. Wasu kuma daga cikin Hausawa kan yi wa ‘ya’yansu tukkuwa ɗaya bisa tsakiyar kai, wasu kuma a kusa da goshi. Ita wannan tukkuwa ta kusa da goshi an fi yi wa almajirai ita, don har ana kiran wannan tukkuwa “leƙa tukunya”. Dukkan waɗannan tukkaye da aka yi bayani a sama ana aske wa yara su ne lokacin da za a yi wa yaron kaciya.
Su kuwa waɗannan da suke yin tukkaye domin wasan fage suna yin tukkayen ne a lokacin da za su fara wasan fagen, ba kuma za su aske su ba sai lokacin da suka manyanta suka tuba da yin wasan fage, a lokacin ne za su yi askin tuba.
Ana yin wasu tukkayen domin a muzanta mutum, watau idan aka kama wani mutum ya yi sata ko wani mummunan laifi wanda ya saɓa wa al’ada, idan ana son muzanta shi a idon jama’a, sai a sanya wanzami ya yi masa tukkaye da yawa a bisa kansa, a shafa masa baƙin tukunya a fuska, sai a sami makaɗi a zagaya da shi cikin kasuwa da wasu wuraren da mutane suke zama, ana yi masa kiɗa yana rawa tare da faɗar irin laifin da ya aikata wanda ya sa aka yi ma sa irin wannan aski.
Ana kuma yin irin waɗannan tukkaye a lokacin wasan kalankuwa, idan wani ɗan kallo ya yi laifi aka kama shi.Idan aka yi masa tara ba shi da kuɗin biya, sai a kira sarkin askar wasan ya yi masa tukkaye da yawa bisa kai, a kuma shafa masa baƙin-tukunya a fuska. Daga nan sai a sanya shi ya goya wata budurwa a riƙa zagayawa da shi a cikin filin da ake yin wasan kalankuwa. Ana yi masa kiɗa yana rawa da wannan budurwa a goye, har sai ya zagaye ko’ina, sannan ya zo gaban Sarkin Samari ya ajiye budurwar ya yi godiya shi ke nan an sallame shi.
Haka kuma ana yin tukkaye a lokacin da ake yi wa jariri askin suna, idan iyayen jariri da abokan arziki ba su biya kuɗin ana aski ba, ko kuma ba su ba wa kakanni kuɗin ana aski ba, sai su kakannin su biya kuɗin askin, daga nan sai su riƙa yi wa iyayen jaririn gorin cewa sun sayi jaririn, ya zama ɗansu ke nan, idan ana son a fanshe shi dole a nunka yawan kuɗin da kakanni suka ba da na ana aski a mayar masu.
Tsayar Da Gemu
A al’adar Hausawa, mutum ba ya ajiye gemu, sai ya kai wasu shekaru na haihuwa, ko kuma sai ya kai lokacin da al’ada ta ƙayyade mutum ya ajiye gemu. Yawanci lokacin yakan zo idan matar ɗansa ta ko ‘yarsa ta haihu, watau ya ɗauki jika ke nan, ya isa ya ajiye gemu.
Idan kuwa ba shi da ɗa ko ‘ya wadda ta isa aure har ta haihu, to sai a kwatanta da haihuwar ɗan abokin haihuwarsa ko ‘yarsa. Ba za a sa gemu ba sai a lokacin wani biki na aure ko na suna a gidan. Tun kafin zuwan ranar ake sanar da ‘yan ‘uwa da abokan arziki da wanzamin gidan wanda shi ne zai yi wa wanda za a sanya wa gemu aski da tsayar da shi.
Karanta Sana’ar Wanzanci A Jiya
Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA
MAYU 2009/JUMADA ULA 1430
Edita@rumasau-kallamu