Ko kun san:- kuli-kuli abincin yara ne ko ince yara nason Kuli Kuli kuma ana iya sarrafata ta hanya yin garin quli-quli sannan ya zama ingredients din abincin kowa.
Abubuwan Bukata
Gunda
Gishiri
Citta
Barkono
Sinadarindandano
Sugar
Yadda ake hadawa
A soya gyada sama-sama sai barzata tabbatar an tsince an barza (babu mai bori kwata-kwata).
A fitar da baqin gyada, domin tana saka daci
Sai ka kai a markada kar a zuba ruwa kamar kullin gyada (peanut butter)
A jiqa
A tsince gyada, a cire mai bori sannan a cire bakin gyadar sai a soyata sama-sama karta qone
A mar kada gyada dan gishiri, citta ko in mai sugar za’ayi sai an dan saka sugar.
A tace ruwan tsamiya a barshi ya kwanta sai a juye abu mai kyau.
Bayan an markada gyada, sai a sakata cikin kwano mai zurfi a zuwa wannan ruwan tsamiya kadan ayita juyawa da muciya ko cokalin katako har sai anga mai ya fara fitowa.
Sannan za’aga gasarar ya curewa ko ince yana dunkulewa. Sai a tsiyaye mai sannan a cura qulin a soyata.
Domin saninyadda ake kek din gyada danna nan