Makaɗan Hausa sukan sadar da waƙoƙin da suka yi bisa maƙasudai ne daban-daban gwargwadon waɗanda aka yi domin su. Waɗannan wurare da ake yin sadawar sababbin waƙoƙin baka sun haɗa da:
i) Gidajen al’umma na ɗaiɗaikun mutane kamar gidajen sarakuna da gidajen malamai da gidajen attajirai; da gidajen masu jarumta da sauran gidajen masu sana’a da kuma sauran gidaje na ɗaiɗaikun al’umma.
ii) Wurare na bukukuwa; kamar bikin aure da bikin suna da bikin kalankuwa da bukukuwan sarauta na al’adar Hausawa da bukukuwan masu sana’o’i da bukukuwan nunin amfanin gona da bukukuwan murna da bukukuwan da akan shirya na musamman da sauransu;
iii) Dandali na shirya wasannin yara; tun a musamman lokacin kiɗan kalangu na ‘yan mata da na asauwara da kuma kiɗan duma da makamantansu.
iv) Wuraren farauta; a fagagen da ake farauta a cikin dazuzzuka akan yi wa mafarauta sababbin waƙoƙi; kuma ana sadar da su da waƙoƙin ne a lokacin farautar a cikin dajin farauta, musamman a yayin da alalmisali, farauta ta rincime; ana buga in buga.
Waƙoƙin da Kassu Zurmi ya yi sababbi; na farauta ya rera su ne kuma ya sadar da su kai tsaye a fagen farauta.
v) Wurin noma, haka abin yake wurin manoma, musamman a yayi na gayyar noma a wata gona; kamar a Gandun Sarki, ko a gonar wasu Sarakai, ko a gonakin taimakon sauran talakawa. Nan ake sadar da sababbin waƙoƙi ga manoma, musamman waɗanda suke da sarautun noma kamar; Sarkin Noma da Madakin Noma da Gojen Noma da Kayayen Noma da sauran jaruman noma da makamantansu;
vi) Wurin wasanni; Wurin wasannin al’ada a ƙasar Hausa wuri ne da ake rera sababbin waƙoƙi, a kuma sadar da su ga waɗanda aka yi wa su da sauran jama’a masu sauraro.
Wurin wasannin al’ada sun haɗa da:
– Wasan Asauwara wadda ake yi a kowace ranar kasuwa ta gari. Ana yin wasan Asauwara a ranar cin kasuwa ta wani gari da yammaci ne, gab da kamar la’asar sakaliya wato kasuwa za ta watse. A wasan Asauwara ana yin waƙoƙi ne tsakanin matasa-‘yan maza da ‘yan mata ko zabiyi da kuma zabiya. Kuma ana yin wasan Baura da kiɗan Baura, a wannan lokaci ma ana rera waƙoƙi sababbi da zimmar sadar da su.
– Wasan kokawa
– Wasan dambe
– Wasan Sharu: wanda ake yi a lokacin da Hausawa suka shaƙu da Fulani
– Da sauran wasanni.
Wurin wasannin al’adun Hausawa, wuri ne ma wanda ake sadar da waƙoƙin baka na Hausa.
vii) Wuraren Tarukan Makarantu:
A lokacin da Hausawa suka sadu da Turawa, musamman a zamanin mulkin mallaka; Turawa suka ƙagi makarantu ga Hausawa tun daga zamanin karatun manya har zuwa karatun yara; an kakkafa wa Hausawa makarantu na boko daban-daban.
To a yanzu a waɗannan makarantu tun daga na boko da kuma na islamiyoyi da a masallatan addinin Musulunci; duka ana yin taruka mabambanta kamar:
– Tarukan fitar ɗalibai.
– Taruka na aikin makarantu, kamar tarukan gama makaranta wato Convocation a Jami’a.
– Taruka na maulidi, kamar Maulidin Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da na Shaihunai da na Mujahidai da na sauransu.
– Tarukan ga-Fili-ga-mai-doki.
– Taruka na Musamman.
– Da sauransu.
viii) Wurare na Musamman
Akwai kuma wasu wurare da ake shirya taruka na musamman domin kawai a rera waƙoƙi sababbi; a sadar da su ga mutanen da aka yi wa su da sauran jama’a na musamman. A ire-iren wurare da muhallai na musamman waɗanda ake nema domin a sadar da waƙoƙi sababbi sukan ƙunshi;
– Wuri wanda aka zagaye shi, kuma aka yi masa shuke-skuke na ciyayi da wasu hakukuwa masu ƙayatarwa; musamman masu ƙara ganin ido ko warware kwarkwatar ido;
– Wuri da aka tanada a matsayi na Gadina;
– Wurin da aka tanada a matsayi na utel-utel ko ɗakin taro na musamman a manyan garuruwa da birane;
– Wurin da aka keɓe domin shaƙatawa, ko na masaukan baƙi;
– da sauransu da yawa.
Domin karanta cikakken bayani akan Yin Waƙar Baka ko Sarrafa Waƙar Baka danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Aiwatarwa Da Sadarwa A Waƙoƙin Baka Na Hausa wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.