Ya’yan Alhazai laƙabi ne na Hausawa da Fulani da Bare-Bari (‘Yan Asalin Najeriya) waɗanda aka haife su a ƙasar Sudan, sakamakon tafiya aikin Hajji da iyayensu suka yi.
- Ganin ku ‘ya’yan Alhazai ya sa ina;
- Ta tunatunin manya mazajen gaskiya.
- Waɗanda ƙaunar Rabbana tsantsa ta sa;
Suka ƙaurace wa gida da daɗin duniya.
- Ba kasuwanci koko noma za su je;
Ba bare a ce wannan bahaushe zai iya.
- A a nufinsu kawai su keta duhun dare; Su fice saharar nan kamar tatsuniya.
- Su je “Hijazu”4 Gabas su yo aiki Hajji; Sannan su ga masu da sun ci burin duniya.
- Tun ma Bature bai yi ko da keke ba;
Balle su jirgi masu keta samaniya.
- Sai dai su hau doki gami da su taguwa;
Koko su Alfadari da Jaki sha-wuya.
- Ko Raƙumi ko ma su wanke ƙafafuwa;
Da ƙafarsu za su fito su doshi Sa’udiya!
- Gaishe ku! Bayin Rabbana yaya kukai;
Da zama a zango inda babu gida ɗaya?
- “Allahu Akbar” ya kuke a cikin Hama5;
Da lokacin rana kamar garwashiya.
- Fatar jikunku kamar gasa ta ake ta yi;
Ina kukan samo ruwan sanyi niya.
- Yaya kukai da harin ɓarayi masu son;
Su kashe mutum su fice da ɗimbin dukiya
- Ko ko harin kura da kan yi cikin dare;
4 Hijaz-Qasar Makkah da Kewaye.
5 Hamada – Sahara ke nan.
Ku ko kuna tsaye tun daren har safiya.
- Wata ma a sannan naƙuda kan zo mata:
Mata su je mata har ta haife lafiya.
- Fallomi ga su Junaina har da Lubayya ma;
Dukkansu su shaida da kun yi gwagwarmaya.
- Khartuumu Undurmana ga Madaninmu can;
Maƙil da ‘ya’yayen fataken gaskiya.
- Maiwurno ga Sinari Sinja akwai su can;
A garin Damazin har zuwa ga “Isofiya”
- A garin Gadarifu har zuwa Kasala da Bor;
Sudan Sawakin duk suna can bai ɗaya.
- Haka nan kukai artabu ɗulin shekaru;
Kafin a ce kun je ku bakin Maliya.
- Kogin da babu kamarsa ya haɗe duniya;
Zurfi da faɗi ga yawan ambaliya.
- Sannan ku ajjari6 Murkaba wato kwami;
Don keta hamshaƙin ruwan nan Maliya.
- Kukan yi kwanakki ɗari a cikin ruwa;
Wa ke batun girkin tuwo balle miya!
- Amma a sannan kun yi fama, ba ta ma;
Kogi ake ba kawai, abokan taffiya.
- Wani ba jimawa sai amai domin jiri;
Kullum yake yi har da tashin zuciya.
- Wani ko gudawa in ta rafkake shi sai;
Dai ai ta biƙi nai da kiwon lafiya.
- Shi ko matuƙin ba ruwansa gama mafi;
Yawan su ba su da tausayi ko da ɗaya.
- Cewa yake yi ba ruwana ni idan;
Wani ya mace lallai a jefa Maliya.
- Haka nan kukai har sai da kun ka haye ruwa;
Kuka je ku bautar Rabbana Sarki Ɗaya.
- Haka nan kukai gumu a faɗin rayuwa;
- Gaishe ku jikoki da ‘ya’yan alhazai;
Ku kanku aya ce ta aikin gaskiya.