khairatu.shehu
Wasu daga cikin masu sha da kuma waɗanda suke zaune da masu shan ƙwayoyin, musamman mata, sun bayyana an fi koyon waɗannan shaye-shaye a waɗannan wurare:
- Wajen liyafa (party) wato taron mata da maza a wajen biki
- Zuwa kwana gidan ƙawaye masu shaye-shaye
- Zuwa wajen zaman ‘yan daba
- Wuraren kallon wasanni
- Zama direban ‘yan maye (a bisa hanya yayin tafiya cikin adaidaita-Sahu ko akan babur Acaɓa
- Zaman makarantun kwana, a sakandare ko gaba da sakandire, kamar jami’o’i da manyan kwalejoji da cuɗanya da ɗalibai masu shaye-shaye a makarantar, a gida Nijeriya da kuma a ƙasashen waje
- Gidajen biki ko suna
- Ƙananan da manyan otal-otal
- Filin dambe
- Gidajin wasannin kwaikwayo na daɓe da gala
- Wuraren da ake yin sababbin gine-gine (kangwaye)
- Tashoshin mota
- Wuraren masu gyaran motoci da Babura
- Gidajen saukar baki
- Sababbin gidaje da ke wajen gari da sauransu
Domin karanta Hanyoyin Ta’ammali Da Kayan Maye danna nan
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.
Edita@rumasau-kallamu