Allah ka daɗo aminci ga Rasulu uban zumunci, da sahabbai ‘yan halacci, shiriya ce bin su babu cuta.
- Allah ƙaran basira,
- Hikima da yawan ishara,
- Na yi waƙa ba Gadara,
- Burina duk a daina wauta.
- ——————————–
- Faɗakarwa za na kunce,
- Za na yi shi a ɗan taƙaice,
- ‘Yar ƙwar huɗu kar ku mance,
- Daudu zan faɗakar da kyan halitta.
- ————————————
- Kun san tushen bayani?
- Mai bilicin zo ka ji ni,
- Ke zan wa ƙira da nuni,
- Manufata yau ki dai rabauta.
- ———————————-
- Yau mata idan ka lura,
- Sun faɗa cikin lalura,
- kuma sun nufaci sahun fitsara,
- dan sun raina Ubangijin halitta.
- ———————————
- Yarinya mai bilicin,
- Burinki ki zarce cincin,
- Sai kin zama ja da nacin,
- Don bilicin kin yi ja ya gauta.
- ————————————
- ‘Yar’uwata ga nasiha,
- A gare ki, ki ƙyale rahha,
- Ki riƙe ta ki daina haha,
- Dariyar ƙeta cikonta cuta.
- ————————————-
- In ka lura da har mazan ma,
- Wasu sun koma zilama,
- Sai bilicin babu ƙima,
- Sun zubarta da sauya fata.
- ——————————-
- Na mazan ma ya fi haushi,
- Laifinsa kwa ya fi kaushi,
- Ya yi daudu da illimin shi,
- Wai fari ne salsalar rabauta.
- ———————————
- Mai bilicin bar gadara,
- Allah ya yi hanin tijara,
- In kana so zo ka tsira,
- Bar wa kanka baƙi a fata.
- ——————————
- Ɗan iska ɗan asara,
- Shashasha uban fitsara,
- Ɗan daudu uban tijara,
- ——————————
- Allah wadaran ka daudu,
- Ɗan iska mai fasadu,
- Mai raina kyautar Wahadu,
- Wanda yai masa baƙi a fata.
- ———————————
- Shashasha ɗan bala’i,
- Kullum aikin jafa’i,
- Ba ka komai sai kata’i,
- Da nufin umma da cuta.
- ———————————-
- In ka amshi batun ga nawa,
- Kafin ka shige kushewa,
- Fata ka rabauta dan’wa,
- Daina girman kai da nuna wauta.
- ———————————–
- In ka juya batun ga baya,
- Za ka sha dukan taɓarya,
- Za ka sha matsa a baya,
- A Kufai kake babu mai jiɓinci.
domin samun karanta cikakkiyar shawara ga me billicin danna koren rubutu.