-
Sunanka farko ya Allah,
Tsira amincinka Allah,
Ƙara su gun Manzon Allah,
Shi munka burin mui kalla,
Ko da cikinsa mafarkinmu.
-
Yau damuwa ce ke raina,
Bisa batu da muke raina,
Cikin darenmu ko rana,
Son rai gare mu abin ƙauna,
Kan dukkanin harkokinmu.
-
Cika shi alƙawari sunna,
Ga dukka manya da ƙanana,
Saɓa shi ko aikin ɓarna,
Da Rabbi sarki ya yi hana,
Ga duk maza har matanmu.
-
Muna barin sa umarnin nan,
Na Rabbana da ya yo ɗin nan,
Ayar cikin Qur’anin nan,
“Ku zam cika alƙawarin nan,
Don za a tambayi shi” gun mu.
- “Ya muminai shin mis sa ne,
Kuke batu” a tsaye zaune,
“Da ba ku yin sa a aiki ne?”
Faɗin Ta’ala sarki ne,
Gare mu kan hali namu.
- Abin takaici mun ƙyale,
Wannan umarni sai hole,
Ran tambaya ba ma kalle,
Halinmu ba kyawu walle,
Don babu alƙawari gunmu.
- Alƙawari in mun ɗauka,
Na lokaci kan duk harka,
Ko yin wani aiki gun ka,
Ni kam gaske nake ɗauka,
Amma cikawa bai samu.
- Murna muke in mun saɓa,
Muna ganin ai mun caɓa,
Har jinjina muka zam karɓa,
Kuka ya dace mui sharɓa,
Don ya ƙazanta aikinmu.
- Ga ‘yan siyasa ko ado ne,
Suna ganin mai sauƙi ne,
Hanyar zuwa ga muradi ne,
Bayan guba mai halaka ne,
Gare su har umma tamu.
- Babu dalilin saɓawa,
Sai don mugunta aikawa,
Nuna isa ko burgewa,
Ko sakaci ga mutuntawa,
Da munka yi bisa zatinmu.
- Ƙarfe goma ka ce zan zo,
Ko ko ka ce wa wane ya zo,
Ba kai shiri goman ta zo,
Sai uzuri ba yin ƙwazo,
Ba ka nadama ko damu.
- Ka ce wa yaro bar kuka,
Abu kaza ne zan ba ka,
Alƙawari ne ka ɗauka,
Amma ka saɓa wa ɗanka,
Ka muna tarbiyyar ɗanmu.
- Wannan fa mugun hali ne,
Amma gare mu abin so ne,
Da takamar mun burge ne,
Bayan ko laifi babba ne,
Za ai hisabin sa kanmu.
- Bai zam cikar addini ba,
Bai zam shi halin kirki ba,
Bai zam abin tunƙaho ba,
Bai zam cika ga kamala ba,
Saba wa alkawari namu.
- In ka tsananta ga cikawa,
Ka ƙyamaci a yi saɓawa,
Wai ka yi halin Turawa,
Halinka na da tsanantawa,
Don ka ƙi mugun halinmu.
- Faɗa a cika dattaku ne,
Ko da ko mai yin yaro ne,
Ko a ina mai ƙima ne,
Abin a ba wa aminci ne,
Mai martaba gun sarkinmu.
- Da mu ya dace ai koyi.
Ya zam gare mu abin ya yi,
A zahiri da cikin rayi,
Mun bar Nasara kaɗai ke yi,
Mun zaɓi ɗaukar son ranmu.
- Wannan abin jin kunya ne,
Gare mu babban aibu ne,
Abin ragewar ƙima ne,
Da za mu taru mu gaggane,
Da sun yi kyau harkokinmu.
- Tsari rashin sa ka damun mu,
Na lokutan harkokinmu,
Loto abin banza gunmu,
Shi ne ko ai rayo tamu,
In ya wuce bai komen mu.
- Faɗa a saɓa laifi ne,
Loto a sauya aibu ne,
Warware zance nakasa ne,
Kin cika kawari sabo ne,
Mu zam cire shi a halinmu.
- Shi alƙawar ai kaya ne,
Bisa ga kai nannauya ne,
Kula da shi imani ne,
Cika shi aikin lada ne,
Mai nauyaya mizaninmu.
- Allah ya ba mu dukan dace,
Mu’amalarmu ta zam tsafce,
Ta zam gudana dinance,
Yara su koya su gwanance,
Su zam du’a’i bayanmu.
- Nan zan tsaya na ciyo burki,
Tabara ba mu yawan ɗauki,
Mu tabbata a halin kirki,
Kullum bisa dukka mataki,
Na rayuwa har ƙarshenmu.
- Mai tsara waƙar Nasir ne
Ahmad rarrauna ne,
Gare mu mai yin addu’a ne,
Bisa ga kyautata hali ne,
A dukka alƙawarorinmu.
Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Haƙƙin Dabbobi
Edita@rumasau-kallamu









