Waƙa Mai Taken Abokin Tafiya

0
36
  1. Rabbi ban hikima basira,

Baituka zan so na tsara,

Kyauta aiki kan mu lura,

Don mu ɗau hanya ta tsira,

Duniya har ran tsayawa.

2. Zan rubutun baituka ne,

Kan Hadisin Musɗafa ne,

Don misali ya saɓa ne,

kan gudanmu a duniya ne,

In ajal gu nai ya zowa.

3. Ga mutum ga ‘yan uwansa,

Su Uku da suke a gunsa,

Zai tafi gun khaliƙinsa,

Yai biɗar ɗaukinsu gunsa,

Don su ne ya ƙyale kowa.

 

4. Sai ya dubi gudansu yac ce,

“Wane loto ya yi fauce,

Me gare ni za ka zam ce,

Taimaka min don na dace,

Ban da kai ban nemi kowa.”

 

5. Sai ya ce “Zan jinyatar ka,

Zan tsaya nai hiddimar ka,

In ko rai ya kau gare ka,

Za na yo sutura gare ka,

Zan biye ka zuwa kushewa.

 

6. “Har da ni za ai saka ka,

Ƙabbari a zamo rufe ka,

Addu’a zan yo gare ka,

San da duk an ambace ka,

Zan tuna ka ina yabawa.”

 

7. Wanga shi ne dangi nasa,

Duk iyali har ɗiyansa,

Za su ɗauke shi su kai sa,

Sai su dawo can su bar sa,

Fin haka ba sa iyawa.

 

8. Ɗan uwa na biyu gare shi,

Za ya nemi garai kira shi,

Sai ya ce mar “Wane ga shi,

Lokacina ya tuƙe shi,

Zan tafi ba dawayowa.

 

9. “Kanka nai duk rayuwata,

Don biɗar ka na yo mutunta,

Don na samu abin bajinta,

Me kake amfanuwa ta,

Yau na samu abin riƙewa?”

 

10. Sai ya ce “Ai ni gare ka,

Lokacin ruhi gare ka,

Garkuwa kuma irli naka,

Duk  buƙatu zan biya ka,

Har ka zam ka zarta kowa.

 

11. “In ko rai ya kau gare ka,

Mun rabon hanya da ni ka,

Za ka tai gun khaliƙinka,

Ni ko ‘yan gado gare ka,

Za su ɗau ni su zam rabawa.

 

12. Wanga shi ne dukiyarsa,

Wadda ya ba rayuwarsa,

Duk wahalta ya yi don sa,

Sun rabu bai ba shi fansa,

Ko gare shi ya taimakawa.

 

13. Ɗan uwa na Uku ya nema,

Yac cane mar “Wane kai ma,

Kai sani yau babu dama,

Dawwamar ruhi jiki ma,

Za na amsa kiran da anwa.

 

14. “Me kake amfanatarwa,

Don na zamto ƙetarewa,

Zanguna da suke tahowa,

Kwai haɗar da rikirkicewa,

Zan buƙaci ka agazawa?”

 

15. Sai ya ce “Duk inda za ka,

Dukka zango ban barin ka,

Tun kushewa ƙabbarinka,

Zan cire kewa gare ka,

Ran zuwan ‘yan tambayawa.

 

16. “Ran tsayo gun khaliƙinka,

In ka tashi ina biyar ka,

Zan yiwo rana gare ka,

Can a mizanin awonka,

Zan shiga yai nauyayawa.”

 

17. Wanga shi ne nasa aiki,

Wanda ya yo shi na kirki,

Kyautatar bauta ga Sarki,

Kyauta niyya babu surki,

Shi yake yin dawwamewa.

 

18. Ko fa aiki bai yi kyau ba,

Ya ƙazanta bai fari ba,

Zai lazimci mutum a turba,

Ƙabbari ba zai bari ba,

Dole shi za yai riƙewa.

 

19. Babu amfaninsa zai ci,

Zai zamo babban kumurci,

Yai ta saran sa yana ci,

Hakka zai wanzu a ƙunci,

Har zuwa ranar tsayawa.

 

20. Gun awo muni na aikin,

Sai ya rinjayi na kirkin,

Rabbi tserar mu tafarkin,

Muna aiki wanda kaidin,

Shaiɗana ke shiryatarwa.

 

21. ‘Yan uwa lallai mu farka,

Tanadin aiki mu ɗauka,

Wanda zai bi mu ya haska,

Ƙabbarinmu har mu farka,

Don fita ranar tsayawa.

 

22. Ran da tarin dukiyarmu,

Kaddarori dangi namu,

Ba su amfani gare mu,

Sai fa mai kyau ayyukanmu,

Ba riya ba goratawa.

 

23. Kar mu ruɗu yawan mutane,

In a kan hanyar ɓata ne,

Gwamma mun ɗau mai mutane,

‘Yan kaɗan in shiryata ne,

Don mu samu abin riƙawa.

 

24. Mun yi roƙo Jalla Sarki,

Sa mu dace wajje ɗaki,

Mui kulawar kyauta aiki,

Don mu dawwama kan tafarki,

Wanda ba zai karkacewa.

 

25. Nasiru G. Ahmadu ne,

Kowashe almajiri ne,

Mai biɗar ƙarin sani ne,

Shi ya saƙo baitukan ne,

Ayyuka mui kyautatawa.

Alhamdu lillahi.
Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.
labarin da ya wuceYadda Aka Yi Bautar Kurmin Jakara A Kano
Labarin na GabaLabari Mai Taken Tsatsar Zuciya
Nasiru G. Ahmad
Haifaffen jihar Kano ne a unguwar 'Yan awaki. Ya yi digiri na ɗaya da na biyu a kan harshe da adabin Hausa. Yana cikin ƙungiyoyi da dama na marubuta a ciki da wajen jihar Kano. Malami ne kuma mawallafin littattfai da waƙoƙi.