1. Bismillah za ni fara
Waƙar yaƙar Korona
2. Nai Salati nai Salama
Ga manzo mai Madina
3. Mu haɗo ƙarfi da ƙarfe
Domin yaƙar Korona
4. Duniya yau ta ɗumame
Da annobar Korona
5. Da ta ɓullo can ƙasar Sin
Ta wuce har Basalona
6. Ta mamayi duk Urubba
Har Amurka akwai Korona
7. Asiya, har nan Afirka
Mun ga kutsowar Korona
8. Larabawa ta shige su
Ai waba’i ce Korona
9. Garkuwa, mu biɗo ta ƙarfe
Don tare kibiyar Korona
10. Wanke hannaye da Soda
Don cire ƙwayar Korona
11. Ku rufe baki da hanci
Don gudun shaƙar Korona
12. Ku tsaya can nesa-nesa
Haka nan in za ku zauna
13. Tsafta ta jiki, muhalli
Kuma cunkoso a daina
14. Garzaya a gwado jikinka
In alamu sun ka nuna
15. Zazzabi mai sa kasala
Tari da murar Korona
16. In ko numfashi ya shaƙe
Sai a killace mai Korona
17. Har sai an maganin ta
Can a killace za ya zauna
18. In ka so ka fice ƙasarku
To ka fara gwajin Korona
19. Haka ma in can ka sauka
Sai ka ƙara gwajin Korona
20. Ga riga-kafi mai aminci
Kariyar cutar Korona
21. Biɗi inda ake a yi ma
Ta ka allurar Korona
22. Za ta ƙarfafa garkuwarka
Domin yaƙar Korona
23. ‘Yan uwa nan zan taƙaita
In kuna son ambato na
24. Faruuku Sarkinfada
A Kanon Dabo gari na
25. Ya Ilahi ka taimake mu
Ka Ije cutar Korona
26. Domin darajar Nabiyyu
Ka kashe ƙwayar Korona
Alhamdulillahi
©Faruk Sarkinfada
Saturday 20/03/2021
11:25 pm
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu