Waƙar Shawara Ga Mai Bilicin

0
952

 Allah ka daɗo aminci ga Rasulu uban zumunci, da sahabbai ‘yan halacci, shiriya ce bin su babu cuta.

 • Allah ƙaran basira,
 • Hikima da yawan ishara,
 • Na yi waƙa ba Gadara,
 • Burina duk a daina wauta.
 • ——————————–
 • Faɗakarwa za na kunce,
 • Za na yi shi a ɗan taƙaice,
 • ‘Yar ƙwar huɗu kar ku mance,
 • Daudu zan faɗakar da kyan halitta.
 • ————————————
 • Kun san tushen bayani?
 • Mai bilicin zo ka ji ni,
 • Ke zan wa ƙira da nuni,
 • Manufata yau ki dai rabauta.
 • ———————————-
 • Yau mata idan ka lura,
 • Sun faɗa cikin lalura,
 • kuma sun nufaci sahun fitsara,
 • dan sun raina Ubangijin halitta.
 • ———————————
 • Yarinya mai bilicin,
 • Burinki ki zarce cincin,
 • Sai kin zama ja da nacin,
 • Don bilicin kin yi ja ya gauta.
 • ————————————
 • ‘Yar’uwata ga nasiha,
 • A gare ki, ki ƙyale rahha,
 • Ki riƙe ta ki daina haha,
 • Dariyar ƙeta cikonta cuta.
 • ————————————-
 • In ka lura da har mazan ma,
 • Wasu sun koma zilama,
 • Sai bilicin babu ƙima,
 • Sun zubarta da sauya fata.
 • ——————————-
 • Na mazan ma ya fi haushi,
 • Laifinsa kwa ya fi kaushi,
 • Ya yi daudu da illimin shi,
 • Wai fari ne salsalar rabauta.
 • ———————————
 • Mai bilicin bar gadara,
 • Allah ya yi hanin tijara,
 • In kana so zo ka tsira,
 • Bar wa kanka baƙi a fata.
 • ——————————
 • Ɗan iska ɗan asara,
 • Shashasha uban fitsara,
 • Ɗan daudu uban tijara,
 • ——————————
 • Allah wadaran ka daudu,
 • Ɗan iska mai fasadu,
 • Mai raina kyautar Wahadu,
 • Wanda yai masa baƙi a fata.
 • ———————————
 • Shashasha ɗan bala’i,
 • Kullum aikin jafa’i,
 • Ba ka komai sai kata’i,
 • Da nufin umma da cuta.
 • ———————————-
 • In ka amshi batun ga nawa,
 • Kafin ka shige kushewa,
 • Fata ka rabauta dan’wa,
 • Daina girman kai da nuna wauta.
 • ———————————–
 • In ka juya batun ga baya,
 • Za ka sha dukan taɓarya,
 • Za ka sha matsa a baya,
 • A Kufai kake babu mai jiɓinci.

domin samun karanta cikakkiyar shawara ga me billicin danna koren rubutu.

labarin da ya wuceYadda Ake Kwalakca
Labarin na GabaYadda Ake Sabulun Wanki