Mawaƙi: Jamilu Alhassan
Amshi: Zaman lafiya muke so,
Allah daɗo ƙasata Rabba.
Bisimilla Sarkin baiwa, Baiwarka ta ishe kowa,
Bara nake kai nawa, Baiwar Ka yo ƙarawa,
Bari nai nasiha babba.
Ƙaro salati Jallah, Gare sa Manzon Allah,
Ƙaunarsa ɗan Abdullah, Silar barin yin kwalla,
Faɗar Ma’aikin Rabba.
Waƙa nake ƙullawa, Zaman salam roƙowa,
Allah Ka zam ƙarowa, Ƙasarmu Naija tawa,
Mu daina yin tababa.
Ku tabbata dangina, Kwai batu ruhina,
Ku zo ku ji ikhwana, Ku daina yaƙar juna,
Kuu san hakan ba riba ba.
Zaman lumana duba, Yana da rana babba,
Rashin sa ba riba ba, Mu daina yin wata gaba,
In ji Shi Sarki Rabba.
Ku tsaya ku ji wani zance, Mu riƙe shi sai mu yi dace,
Fitina tana nan kwance, La’ana ta gun Mahalicce,
Ga masu ta da ta duba.
Aya cikin Anfali, Ashirin biyar ɗan kalli,
Halin masifa kalli, Ba ta barin mai hali,
Yaro fa har ma babba.
Zama idan ai ba fis, Da ka ji an ce zan ƙis!
Tamkar baru an ce is! Kowa yana yin tinƙis,
Ba mu so ganin wannan ba.
Wa’atasimu faɗar Mahalicci, Bihablillahi har da maƙoci,
Jami’an, babu mai yin ƙunci, Idan mun farraƙe zai ɗaci,
Rayunmu ban ƙarya ba.
Idan ka ɗauki Afirka, Akwai ƙasashe leƙa,
Waɗanda akke yaƙa, Wasunsu na yin kuka,
Ba su samu zaman aunu ba.
Burundi in ka dubi, Ruwanda har ma Libi,
Ka tabbata sun ƙi bi, Kundi na mulki kitabi,
Ba su daina yin yaƙi ba.
Laberiya Somali, A nayinti-wan ɗan kalli,
Sun ƙaurace nasu mahalli, Waɗansu an bar kwalli,
Domin ba su ma zauna ba.
Itofiya ita wannan, Iritiriya shi ke nan,
Nayinti-et su biyun nan, Sun yaƙi juna rannan,
Ba suy yi adalci ba.
Sierra Leone har Sudan, Mutum fa wane metan,
Gidansu sun bar wannan, Zaman rashin fis ke nan,
Ya sa ba sa zauna ba.
Idan ka zo nan Naija, Farin ido sai yai ja,
Kano fa babbar haja, Na Marwa ne kuma yaj ja,
Amman fa bai kyauta ba.
Muhammadu na Marwa, Gyauronsa na can Yarwa,
Ƙala-ƙato ban mantawa, Fitinar da sun shukawa,
Da yawa akai binnewa, Ka ji halin ‘yan zamba.
Zangon katab, wayyo ni! Hausa Birom kaico ni!
Tivi-Jukun can ƙarni, Da yawansu ai sun rauni,
Wasu ma ba su ko shura ba.
Idan ka zo nan Yarwa, Boko haram kwai tsiwa,
A Bama ban mantawa, Wasunmu na a kushewa,
Abin fa bai kyawu ba.
A Mubi har ma Gombe, Ba yau ba har ma gobe,
Addu’arsu hannu tuɓe, Tamkar kwari ba kube,
Salam salam, ya Rabba.
Zaman salam kwai auki, Ya zarce ma ɗan sarki,
Kowa yana nasa aiki, Ticas muna yin maki,
Ba mu zam muna ganda ba.
A Yobe nan ce jahata, Abin fa ya so ƙazanta,
Gwamnanmu ai ya kyauta, Ya ce a bar yin wauta,
Bai bar mu muna ihu ba.
A 1st Disemba fotin, A YSU can hostel ɗin,
Aka zo da kutse domin, A kashe ake yin yaƙin,
A Monde ba zan manta ba.
Salmanu sannan Sulfa, Sun zo suna sassarfa,
Sawunsu sam ba safa, Sauran suna shan suffer,
Subhana Sarki Rabba.
Ciza nake tun ɗazu, A Yobe ai dai yanzu,
Zama na lau ya wanzu, Mun roƙi Sarki Azizu,
Bai ƙi ya yo amsa ba.
A yanzu zan yo busa, Na ba ku labarinsa,
Zaman lumana kansa, Ya zarce daɗin masa,
Ta Bauchi ban ƙarya ba.
Ga shawara zan bai wa, Gwamnanmu har ma kowa,
Ga wanda ke son yalwa, Gun zaman lumana aiwa
Mu kama Allah Rabba.
Ina ƙiranmu jumulla, Mai ɗan kwali ko mai hula,
Rawani da mai jan akala, mu kama Allah walla,
Mafuta ba za mu rasa ba.
Shi dai fa rai kwai tsada, Sojojinmu har ‘yan sanda,
Sun ce sun ji sun kuma yarda, Su nasu ran sun sai da,
Don kare ƙasata babba.
A bar batun ɓangaranci, A bai wa kowa ‘yanci,
Musulum, Kirista maƙoci, Mu mutunta juna.
Domin karanta cikakken Yabo Daga Waƙar Maryam Fantimoti danna nan.
Domin karanta cikakken Yabo A Waƙoƙin Baka danna nan.
Don karanta cikakken Dangantakar Harshe da Waƙa danna nan.