Waƙa Mai Taken Haƙƙin Dabbobi

0
31

1. Muna godiya ga jalla sarki Rahimuna,
Da ya horace mana halittunsa bai ɗaya.
2. Ya fifita ɗan Adam bisa dukka talikai,
Na kogi tudu da masu tashi samaniya.

3. Salati gurin Muhamman da ya zamo,
Mai jinƙai da tausayi ga kowa a duniya.
4. Salamu Alaikumu zumaina ina kuke?
Batu zan yi kan hali na zulmu ga khalƙiya.
5. Dabbobi nake nufi da tsuntsaye wanda ke,
Zaman rayuwa cikinmu yamma da safiya.
6. Allah ya huwace su gare mu mu mallaka,
Mu turke mu garkace nau’i ne na dukiya.
7. Wasunsu kayanmu munka lafta bisa nasu,
Mai nauyi su kai wuri mai nisa na nahiya.

8. Wasunsu Allahu ya ce mu ci su ne,
Mu yanka da sunansa a gyare mu sha miya.
9. Wasunsu har gonaki mukan sa su ayyuka,
Na noma da huɗa duk buƙatunmu sun biya.
10. Wasunsu don sha’awa muke kiwatar su ne,
Ganin su ke ba mu jin nishaɗi a zuciya.
11. Wasunsu girman jikinsu ya zarce tambaya,
Wane namu har wa yau sun fi mu ƙarfin tsiya.
12. Misali ɗau Raƙumi da Sa har da sha bugu,
Da doki ya ‘yan uwa mu zam yin tunaniya.

13. Allah ya hore mana muna sarrafa su duk,
Ta duk yadda munka so muna masu fariya.
14. Amanar su Rabbi ya aje gun mu mun shina,
Domin jin daɗi namu mu bauce shi shi ɗaya.
15. Abin ban takaici shi ne yadda muke musu,
Mugunta da cin zali da dukan bulaliya!
16. Ina mai sakin dabba kiwon Allah ya isa?
A ran lahira wallahi kai za a tambaya.
17. Ina mai aje kare da kyanwa wuri nasa,
Ya kasa ciyar da su sai dai sui ta shan wuya?

18. Ina mai lafta wa jaki kaya niƙi-niƙi,
Ya daure yana tafe amma ga dukan tsiya?!
19. Ina mai barin yara su kamo tsuntsu da ma,
Sarkin-ƙwai domin wasa da su ba shi tausaya?
20. Ina masu ragaita da dabba don su sayar,
Ba ci sai galabaita ga zafi na shamsiya?
21. Ina masu taskace ta dabba su killace,
Ba ci ba fita ta nemi nata a rariya?
22. Ina mai zama ƙoto kare na zaman suɗi,
Farko ya hana shi ga bugu babu zanbiya?

23. Ashe ba mu yin tsai mu tuna duk halittuka,
Na Allah ne mu da su don Allah mu tausaya.
24. Mu bar zaluntar dabba da tsuntsu da ƙwaruka,
Allah za ya tambaye mu ranar hisabiya.
25. Dukkansu rai ne da su jin daɗi suke biɗa,
Kamar mu da ‘yancin rayuwa har da wataya.
26. Idan ka aje dabba ka cishe ta kowashe,
Ruwa mai kyawu ba ta a kwano kwatarniya.
27. Lallai kar ka cuce ta da duka ko razani,
Ko kyara da zagi in ka yo su tana jiya.

28. Idan kai mai kiwo ne yawansu ya kai zuwa,
Nisabin zakka ka fid da ta banda noƙiya.
29. Manzo ya hana wahal da dabba a lokacin,
Yanka ta ka zam wasa wuƙa kar ta sha wuya.
30. Bayanin na nan a “Arba’una” da mun biya,
Hadisi na sha bakwai ku duba shi bai ɗaya.
31. Amma fa ku san kashe kunama halal yake,
Da ɓera ɓarawon nan Hankaka Macijiya.
32. Kare mai hauka a kar shi Kura da ma Tsaka,
A duk inda an gan su kashe su halaliya.

33. Don Allah mu tausaya wa dabba a kowashe,
Mu ma sai Allah ya tausaye mu ran tambaya.
34. Kiwo sai an haƙuri don Allah mu tausasa,
Ku san babu hankali ga dabba haiwaniya.
35. Abin duk da ka ciyar da dabba ai sadaka,
Ake ba ka ladanta mu zam yin rigeniya.
36. A nan zan tsaya da wagga waƙa ya ‘yan uwa,
Ya Allah ka yafe mu kurenmu gaba ɗaya.
37. Sunana Muhammad Nasiru G. ɗan Ahmadu,
Kano birnin Dabo masu mota da Saniya.
38. Fa’ulun Mafa’ilun fa’ulun Mafa’ilun,
Ma’aunin Ɗawilu ke da waƙar da na biya.

Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.
Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Haƙƙin Maƙwabci

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTarihin Garin Rimin Gado
Labarin na GabaYadda Hukuncin Tsotsar Al’aura Yake A Likitance
Nasiru G. Ahmad
Haifaffen jihar Kano ne a unguwar 'Yan awaki. Ya yi digiri na ɗaya da na biyu a kan harshe da adabin Hausa. Yana cikin ƙungiyoyi da dama na marubuta a ciki da wajen jihar Kano. Malami ne kuma mawallafin littattfai da waƙoƙi.