Littafin “Salmanu da Salma” littafi ne na soyayya da aka gina bisa tubalin kimiyya da ilimi. Marubucin ya nuna cewa soyayya ba motsin zuciya ba ne kawai, tana buƙatar fahimta, haƙuri da haɗin kai.
Babban jigon littafin shi ne soyayya, wacce ta haɗu da ilimi, inda jaruman ke fuskantar ƙalubale tsakanin burin rayuwarsu da kuma soyayya. Labarin ya nuna yadda ilimi ke taimakawa wajen yanke shawara mai kyau a rayuwa.
Salmanu jarumi ne mai son kimiyya da burin samun nasara, yayin da Salma ke ta kasance mace mai hankali, ilimi da juriyar zuciya. Rikice-rikicen da suka shiga sun sa labarin ya zama mai jan hankali.
Kuma an yi amfani da kalmomi masu sauƙin fahimta, waɗanda suka dace da kowane mai karatu. Saƙon littafin shi ne cewa soyayya ta gaskiya tana bunƙasa ne, idan an haɗa ta da ilimi da mutunta burin juna.
Karanta Tarihin Farfesa Abdallah Uba Adamu
Edita@rumasau-kallamu








