Tattalin Arziƙin Ƙasar Hausa

0
12

Ƙasar Hausa kamar kowace ƙasa tana da manyan hanyoyi da dama waɗanda suke taimaka wa tattalin arzikinta bunƙasa. Daga cikin waɗannan hanyoyi akwai waɗanda aka gada tun iyaye da kakanni, wato su ne na asali. Ire-irensu sun haɗa da noma da kiwo da fatauci da sana’o’in gargajiya. Bayan waɗannan akwai waɗanda aka samu sakamakon cuɗanya tsakanin Hausawa da wasu baƙin al’ummu kamar sana’ar kanikanci da kafinta da ɗinkin keke da mesin da dai sauransu.

Noma

Hausawa suna yi wa noma kirari da suke cewa “noma na duƙe tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar”. Wannan kirari na bayyana sana’ar noma daɗaɗɗiya ce a wannan duniya ba wai ga Hausawa kaɗai ba. Wannan ne ya sa idan ana maganar tattalin arzikin ƙasar Hausa, noma ne za a fara kawowa don kuwa shi ne ƙashin bayan tattalin arzikin wannan ƙasa.

Wannan kuwa ya faru ne saboda sana’a ce wadda kowa-da-kowa yake yi talaka da saraki, attajiri da matalauci, maza da mata, babba da yaro don a sami abincin da za a ci da kuma wanda za a sayar don yin hidimomin yau da kullum. Saboda haka ne manoma a dukkan faɗin ƙasar Hausa da kewayenta suke samun wurare masu nagarta waɗanda suka haɗa da fadama da jigawa don noma amfanin gona mai kyau.

Al’ummar Hausawa na yin noma iri biyu, na abinci da na kasuwa. Kayan noma na abinci sun haɗa da gero da dawa da masara da maiwa da dai sauransu, na kasuwa kuma sun haɗa da auduga da gyaɗa. Haka kuma ƙasar Hausa tana da albarkar da ake noma wasu abubuwan kamar rogo da dankali da sauransu (Nadama, 1977:90 – 92).

Kiwo

Kasancewar ƙasar Hausa shimfiɗaɗɗiya ce ga kuma sarari da ciyayi a ko’ina ya sa kusan a kowane gida ana kiwon dabbobi ko tsuntsaye. Hausawa na tsare dabbobi da tsuntsaye a gidajensu ta hanyar ba su abinci ko kuma a kora su zuwa daji don su nemi abinci a can. Ire-iren dabbobin da Hausawa suke kiwo sun haɗa da shanu da tumaki da awaki don cin namansu da kuma sayarwa.

Haka kuma ana sayar da fatunsu da ƙiragansu don yin amfani da su. Ana kuma ɗaukar kashin da suka yi don kaiwa gona a matsayin takin da zai ƙara wa gona albarkar ƙasa. Bayan waɗannan dabbobi, Hausawa na kiwon dawaki don hawa na ƙawa da jin daɗi. Haka kuma suna kiwon jakuna da alfadarai don ɗaukar kaya da yin wasu ayyuka irinsu fatauci. Ire-iren waɗannan dabbobi dukkansu ana kiran su da sunan dabbobin gida.

Bayan dabbobi Hausawa suna kiwon tsuntsaye irin su kaji da agwagi da zabi don cin namansu da ƙwayayensu da kuma sayarwa. Haka kuma saraki da attajirai suna kiwon tsuntsaye na alfarma irin su aku da ɗawisu da kanari don sha’awa da nishaɗi.

Fatauci

Tun kafin wannan zamani al’ummar Hausawa suna da irin nasu tsari wajen tafiyar da harkokin kasuwanci. Wannan tsari ana iya dubansa ta fuska biyu, kasuwancin cikin gida da kuma na waje. A cikin gida akwai kasuwanni na garuruwa waɗanda ake tafiyar da harkokin kasuwanci ta hanyar furfure. A irin wannan kasuwanci ana musayar abubuwan sayarwa ne, misali manomi ya ba masaƙi kayan gona don ya amshi kayan saƙa, ko ya ba makiyayi don ya amshi wata dabba da sauransu.

An daɗe ana yin irin wannan tsari na cinikayya a ƙasar Hausa har zuwa cikin ƙarni na goma sha takwas da aka shigo da hanyar yin amfani da kuɗin wuri da biringizau don yin saye da sayarwa a duk faɗin Afrika ta Yamma (Nadama, 1977:137 – 138). Ta fuskar kasuwancin wajen ƙasar Hausa ‘yan kasuwa daga ƙasar Hausa na yin fataucin kayayyaki daga wannan ƙasa zuwa garuruwan Adar da Azben da Nufe da ƙasashen Yarabawa da Gwonja.

Bayan sun sayar da kayayyakinsu a can, suna kuma sawo wasu kayayyakin daga waɗannan ƙasashe su kawo ƙasar Hausa don su sayar. Ire-iren kayayyakin fatauci da suka riƙa saye daga ƙasar Hausa suna kaiwa waɗannan ƙasashe, sun haɗa da daddawa da kayayyakin sutura irin waɗanda aka saƙa a ƙasar Hausa da kuma shunin gadi da baba da dabbobi da sauransu.

Haka kuma suna sawo kayayyaki irinsu bindigogi da kayan albarushi da riguna girken Nufe da kayan ƙarau daga ƙasar Nufe. Suna kuma sawo balma da kanwa da dabino da dawakin Azbin da awaki da tumaki da raƙuma daga ƙasashen Adar da Azbin da kuma Borno.’Yan kasuwar da suke zuwa fatauci kudu watau ƙasashen Yarabawa da Gwonja suna sawo goro don kawowa ƙasar Hausa da maƙwabtanta na arewa don sayarwa (Nadama, 1977:142 – 143).

Sana’o’in Gargajiya

Kafuwar garuruwa a ko’ina cikin ƙasar Hausa da kuma bunƙasar da noma ya samu ya ƙara taimakawa wajen samuwar sana’o’in gargajiya inda ake ƙera da kuma sarrafa kayayyaki iri daban-daban domin amfanin mutanen ƙasar Hausa da maƙwabtansu na kusa da kuma na nesa. Ire-iren waɗannan sana’o’i sun haɗa da ƙira da saƙa da rini da jima da dukanci da sassaƙa da sauransu.

Akwai kuma sana’o’in da ake yin ayyukan taimaka wa rayuwa kamar wanzanci da fawa da ɗori da sauransu. Bayan waɗannan akwai ƙananan sana’o’i waɗanda mata suke tafiyar da su kamar kaɗi da kitso. Waɗannan sana’o’i na gargajiya sun taimaka matuƙa gaya wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa. Yanzu za a ɗauke su ɗai-ɗai da ɗai-ɗai domin ganin yadda suka taimaka wa tattalin arzikin ƙasar Hausa.

Ƙira

Ƙira sana’a ce wadda aka fi yi a lokacin rani domin tanadar kayan aikin noma, amma duk da haka ana yin ta a kowane lokaci na shekara domin samar da kayan amfanin gida na yau da kullum. Maƙera sun kasu zuwa kashi biyu, akwai maƙeran baƙi da maƙeran fari. Maƙeran baƙi su ne suke tono tama su narka ta don ta zama ƙarfe wanda suke amfani da shi domin yin nau’o’in kayan ƙira.

Ire-iren kayayyakin da maƙeran baƙi suke yi sun haɗa da fartanya da masassabi da gatari da lauje da sungumi da adda da dai sauransu domin yin ayyukan gona. Haka kuma maƙeran baƙi suna ƙera takubba da gariyo da tsitaka da masu da kibau da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen yin farauta da yaƙi.

Bayan waɗannan suna yin kalaba da wuƙaƙe ƙanana da manya waɗanda ake amfani da su wajen yin ayyukan cikin gida na yau da kullum. Haka kuma su ne suke samar da kayan aikin wanzanci waɗanda suka haɗa da asake domin yin aski da kaciya da kuma kalaba wadda ake amfani da ita wajen cire belun-wuya. Suna kuma yin askar tsaga wadda ake amfani da ita wajen cire angurya a farjin mata da yin tsagar gado da ta magani da ta kwalliya da sauransu.

Saƙa

Saƙa sana’a ce wadda ake sassarƙa zare ko gashi ko ɓawo ko kaba don a mayar da su wani abu mai faɗi kamar tufafi ko shimfiɗa. Saboda haka a iya cewa, saƙa ta kasu zuwa iri biyu, ta tufafi da ta kayan shimfiɗa. Ana amfani da zaren auduga ne wanda mata suke kaɗawa domin saƙar tufafi.

Masaƙa wato masana’antar da ake sarrafa zare domin yin sutura ita ma ta kasu zuwa iri biyu. Akwai masaƙar tsaye wadda mafi yawanci mata ne suke amfani da ita don yin saƙar gwado ko zanen kujera ko ɗan goyo wanda ake goya jarirai. Akwai kuma masaƙar zaune wadda maza ne suka fi yin amfani da ita wajen yin saƙar sauran abubuwa.

Hakika wannan sana’a tana da matuƙar muhimmanci a ƙasar Hausa domin kuwa ba domin ita ba da an riƙa tafiya tsirara. Wannan a fili yake, sutura ita ce alamar da take bayyana bambanci a tsakanin mutum da dabba. A cikin mutane ma da sutura ake iya rarrabe bambancin al’adu.

Da ita ake gane cikakken mutum da akasinsa. Haka kuma da ita ake sanin mawadaci da mabuƙaci. Masana’antar saƙa ta taimaka sosai wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa. Wannan kuwa ya samu ne sakamakon kayayyakin da ta riƙa samarwa waɗanda ake sayarwa a kasuwannin cikin gida da na ƙasashe maƙwabta (Alhassan, 1982:52-54).

Jima

Jima sana’a ce wadda ake sulluɓe fata don a fitar da gashin da yake jikinta. A irin wannan masana’anta da ake kira majema ana sauya fata daga halinta na asali na gashi da kaushi a sarrafa ta, a gyara ta yadda za ta yi laushi kamar sutura.

Bayan an gyara fata ta yi kyau ana sayar da ita ga dukawa, kuma mafi yawancin fatar da aka gyara tana daga cikin manyan muhimman hajoji da ake safararsu daga ƙasar Hausa zuwa ƙasashe maƙawabta na kusa da na nesa. Ana yin wannan safara tun lokaci mai tsawo da ya gabata kafin shigowar Turawa wannan ƙasa.

Irin wannan fata na daga cikin kayayyakin da aka riƙa fataucinsu daga Kano da Katsina da Zamfara da Sakkwato ana ƙetare hamadar Sahara da su ana kaiwa Morocco da sauran ƙasashen da suke arewacin Afrika ana sayarwa. Daga nan ne kuma Turawa suke sayen ta su kai ƙasashensu inda suke sarrafa ta domin yin jikunkuna da takalma da riguna maganin sanyi da sauran abubuwa waɗanda kuma suke kawo wasu daga cikinsu zuwa ƙasashen Afrika da sauran ƙasashen duniya don sayarwa.

Dukanci

Dukanci sana’a ce wadda ake sarrafa fata don mayar da ita wani abu na amfanin yau da kullum. Ire-iren abubuwan da dukawa suke yi sun haɗa da jikunkuna da takalman fata da igiyar linzamin doki da burgami da zabira wadda ake zuba kayan wanzanci da jakar zuba ma dawaki dawa ko dusa. Haka nan kuma suna yin warki da gafaka da tandun kwalli da kuben wuƙa da na takobi da sauran abubuwa.

Bayan dukawa sun yi waɗannan abubuwa suna sayar da su ne ga waɗanda suke buƙata da kuma masu yin sari waɗanda suke kaiwa kasuwanni na cikin gida da na waje. Haka kuma ‘yan kasuwa na waje na shigowa cikin ƙasar Hausa don sayen ire-iren waɗannan kayayyaki da dukawa suka sarrafa.Wannan masana’anta ta dukanci ta bayar da gagarumar gudummuwa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa.

Rini

Rini na nufin sauya launin tufa ko zare don ya zama wani iri. Ana kiran masana’antar da ake yin rini marina. Abubuwan da ake amfani da su wajen yin rini sun haɗa da muciya da kwatarniya da guga da itace da ƙaiƙayi da ɗan kutuɓu da baba da katsi da shuni da zarta da marina da ruwa.

Wannan masana’anta ta taimaka sosai wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa. An fahimci haka ne kuwa ta la’akari da kayan rini irin na ƙasar Hausa na daga cikin muhimman abubuwan da fatake suke yin safararsu daga ƙasar Hausa zuwa ƙasashen maƙwabta don sayarwa.

Sassaƙa

Sassaƙa sana’a ce wadda ake gyara icce don a mayar da shi wani abu na amfani. Masassaƙan ƙasar Hausa na sassaƙa turmi da taɓarya da kujerar zama ta mata da kujerar gwado ta maza da ƙotar fartanya da ta masassabi da ta gatari da ta garma. Haka kuma masassaƙa suna sassaƙa akushi da ƙoshiyar dama fura da ludayin itace da allunan karatun Alƙur’ani mai girma da dai sauran abubuwa masu yawan gaske.

Wannan sana’a ta sassaƙa tana taimaka wa tattalin arzikin ƙasar Hausa matuƙar gaske. A iya ganin haka ta yadda take samar da wasu kayan aiki ga sauran masana’antun gargajiya. Misali, manoma na amfani da ƙotoci, wanzamai na amfani da ƙoshiya don cire belun-wuya, makaɗa na amfani itacen da ake yin kayan kiɗa, masaƙa na amfani da gwafa wadda ake kafa masaƙa ta zaune da ta tsaye da sauran abubuwa.

Wanzanci

A Hausance, sana’ar “wanzanci” tana nufin amfani da askar aski domin yin aski da gyaran fuska da yin kaciya da kuma amfani da kalaba da ƙoshiya don cire belun-wuya. Sana’ar wanzanci ba ta tsaya a nan ba don kuwa ana amfani da ‘yar tsaga don yin ƙaho da cire angurya a farjin mata da yin tsagar gado da ta kwalliya da ta magani.

A sana’ar wanzanci dai ana yin hujen kunne da yanke yatsan cindo (shiddaniya) da yanke linzami a cikin bakin jarirai da wasu ayyuka da dama. Haka kuma masu yin sana’ar wanzanci na bayar da magungunan gargajiya ga waɗanda suke buƙata.

A taƙaice a iya cewa sana’ar wanzanci ta taɓo aikin likita a ƙasar Hausa kafin zuwan asibitin zamani. Dalili kuwa shi ne wani daga cikin ayyukan wanzanci shi ne kula da lafiya musamman ta jarirai da ƙananan yara, ta wani fannin ma har da lafiyar manya. Masu yin ire-iren waɗannan ayyuka ana kiran su wanzamai waɗanda dole su kasance masu cikakkiyar lafiya, masu hankali da natsuwa.

A mafi yawanci maza ne suke yin sana’ar wanzanci, amma ana samun wasu mata waɗanda saboda rashin wani namiji a gida, ko kuma don wani dalili sukan koyi wannan sana’a daga mahaifansu. Ana gadon wannan sana’a a wajen iyaye ko kakanni na wajen uba. A gargajiyance yana da matuƙar wuya a sami wani mutum wanda bai gaji wannan sana’a ba yana yin dukkan ayyukan wanzanci.

A wannan zamani ana samun waɗanda kan koyi yin askin zamani na saisaye wanda suke yi da kayan askin zamani, amma iyakarsu askin don kuwa ba sa iya yin sauran ayyukan wanzanci. Haka kuma wajen yin ayyukan wannan sana’a gado na taka muhimmiyar rawa, don kuwa kowane wanzami yana da gidajen da yake zuwa don gudanar da ayyukansa. Wani wanzami daban ba ya zuwa gidan da wani wanzami ɗan’uwansa yake yin aiki ya yi.

Kowane gida ko zuri’a suna da wanzamin da suka gada wanda yake yi masu aiki, daga shi sai ‘ya’yansa ko wani da ya wakilta ne kaɗai suke iya zuwa waɗannan gidaje nasa don yin waɗannan ayyuka. Haka su ma masu gidajen ba sa kiran wani wanzami daban don yin ayyukan wanzanci a gidajensu dole sai wanda suka gada tun asali daga iyayensu.

Wani tsari mai ban sha’awa dangane da aiwatar da sana’ar wanzanci shi ne, wanzami ba shi da iyakar ƙasar da zai riƙa gudanar da ayyukansa. Yana iya fita daga garinsu ko ƙasar dagacinsu ko hakiminsu ko sarkinsu, kai a wannan zamanin har jiharsu ya tafi wuraren da mutanensa suke domin yi masu ayyukan wanzanci.

Misali, idan Bahaushe ya auri Bafulatana wadda ita a al’adarsu mace ba ta yin haihuwar fari a gidan mijinta, sai dai ta tafi goyon-ciki gidan mahaifanta. To, idan ta haihu ba mahaifanta ne za su kira wanzami ba, mijinta ko mahaifansa ne za su kira wanzaminsu na gida don ya yi ayyukan. Haka kuma a wannan zamani idan mutum na aikin Gwamnati a wani gari, idan matarsa ta haihu sai ya aiko garinsu don wanzaminsu na gida ya je domin yin ayyukan.

Misali, lokacin da nake gudanar da wannan bincike, da na ziyarci Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya na sadu da Dr.Kabir Chafe wanda shi ne Shugaban Sashen Koyar da Tarihi kuma Shugaban Tsangayar Fasaha da Zamantakewa na wannan Jami’a. A lokacin da nake tattaunawa da shi ya bayyana min cewa, a duk lokacin da aka haihu gidansa nan Zariya, yana aikawa garinsu Tsafe don wanzaminsu na gida ya zo ya yi ayyukan wanzanci.

Ni ma a halin yanzu mutanen da nake yi wa aikin wanzanci waɗanda kuma muka gaji juna waɗanda suke aikin Gwamnati a Katsina da Abuja da Kaduna da sauran wurare, idan matansu suka haihu suna aikowa don in je waɗannan garuruwa da suke don yin aikace-aikacen wanzanci.

A wani lokaci takan kama a sauya wanzamin da aka gada. Dalilan da kan sa a yi wannan sauyi sun haɗa da sauyin wurin zama. Wato idan mai gida ya tashi daga garinsu ya koma wani gari da yake nesa da garinsu na asali, to a sabon wurin da ya sauka idan aka yi masa haihuwa, ko yana bukatar a yi wa wasu yaransa kaciya ko dai wata bukata ta aikin wanzanci a gidansa, sai ya nemi wani wanzami don ya yi masa waɗannan ayyuka. Daga wannan lokaci shi wannan wanzami ya zama na gidansa, sai kuwa idan wani dalilin ya tilasta a sauya shi.

Haka kuma idan wanzamin gida ya rasu ko wata lalura ta rashin lafiya ta same shi, idan ba shi da mai gadonsa sai waɗanda yake yi wa aiki su sami wani wanda zai maye gurbinsa. Shi ma daga nan ya zama wanzamin waɗannan gidaje. Idan kuma rashin fahimtar juna ko wani saɓani ya shiga tsakanin wanzamin gida da mai gidan da yake yi wa aiki, misali maita ko siyasa ko aure da sauransu sukan tilasta a sauya wanzami.

Idan ba ta waɗannan hanyoyi da aka yi bayaninsu ba, matuƙar wani wanzami ya yi shisshigi ya shiga gidajen da wani wanzami yake yin aiki ba tare da izininsa ba, ɓarna na iya shiga. Domin kuwa kowannensu zai yi ta ƙoƙarin yin ire-iren surkulle da sihirce-sihircen da ya iya domin nakasa abokin hamayyarsa ko ya lalata ayyukan da ya yi.

Wanzaman Hausawa sun kasu zuwa rabo biyu. Akwai wanzaman gado da wanzaman ƙoƙo. Wanzaman gado su ne waɗanda suka gaji yin sana’ar wanzanci a wajen iyayensu da kakanninsu, kuma suna yin dukkan ayyukan wanzanci waɗanda suka haɗa da yin aski da kaciya da cire belun-wuya da cire angurya da bayar da magungunan gargajiya da yin tsagar gado da ta magani da ta kwalliya.

Ire-iren waɗannan wanzamai ne suke gadon gidajen da za su riƙa yin ayyukan wanzanci. Haka kuma daga cikin irinsu ne ake naɗa Sarkin Aska ko Magajin Aska. Idan buƙatar aikinsu ta tashi a mafi yawancin lokaci a gidajensu ake zuwa don a sanar da su wuri da lokacin da ake bukatar su je don yin ayyukansu.

Kuma a mafi yawancin lokaci ire-iren waɗannan wanzamai ba su da rainuwa domin kuwa duk abin da aka ba su a matsayin ladar aikinsu, sai su karɓa suna masu yin murna da godiya. An bayyana cewa dalilin haka shi ne suna yin waɗannan ayyuka ne don gado ba don ladar da ake biyan su ba.

Su kuma wanzaman ƙoƙo ba sa yin dukkan ayyukan wanzanci, iyakar ayyukan da suke yi sun haɗa da aski da gyaran fuska. Wanzaman ƙoƙo barorin wanzaman gado ne. A wani lokaci irinsu na yin ƙaho, kuma irinsu ne suke yawo da zabira rataye a kasuwanni da cikin garuruwa suna neman wanda za su yi wa aski ko gyaran fuska ko ƙaho.

Haka kuma ire-iren waɗannan wanzamai ne suke yin rumfuna a kasuwanni da shaguna a cikin garuruwa domin yi wa mabuƙata aski da gyaran fuska. Idan suka yi wa mutum ayyukansu suna gaya masa adadin kuɗin da zai biya ba kamar wanzaman gado ba. Hausawa na yi wa ire-iren waɗannan wanzamai kirari kamar haka:

Wanzaman ƙoƙo a ci tuwo a yi aski,

                                 Cire belun-wuya da belun-mata sai ‘yan gado”.

Ba a tsakanin Hausawa kaɗai ake yin sana’ar wanzanci ba, akwai al’ummomi da ƙabilu masu yawa waɗanda ake yi masu ire-iren ayyukan wanzanci. Wasu ana yi masu dukkan ayyukan ne, wasu kuwa ana yi masu waɗansu ne daga cikin ayyukan kawai.

Wannan dalili ne ya sa kowace al’umma ko ƙabila tana da sunan da take kiran wanzami ko mai yin ayyuka irin na wanzanci. Misali, Larabawa suna kiran wanzami da sunan al-Hallaƙ. Fulanin da suke zaune a ƙasar Hausa suna kiran sa da sunan wanzamijo, su kuma Fulanin da suke zaune a gabacin ƙasar Hausa a Yola da Gwambe suna kiran sa da sunan wanjam ko wanjamjo.

Turawan Ingilishi suna kiran sa da sunan barber, su kuma na Faranshi suna kiran sa da sunan coiffure ko coifere. Barebari suna kiran wanzami da sunan diyeji ko wanzama, shugaban wanzamai kuma suna kiran sa da sunan Zanna Ɗambusuma. Buzaye kuma suna kiran wanzami da sunan aghachaou, su kuma Adarawa na kiran sa da sunan wanzami. Su kuma Yarabawa na kiran wanzami da sunan bonjamo, wanda yake yin aski kawai kuma suna kiran sa da sunan fari-fari ko akola. ’Yan ƙabilar Ekoi waɗanda suke zaune a Jihar Cross Riɓer suna kiran wanzami da sunan anu-uka.

Nufawa kuma suna kiran sa da sunan gozan. Su kuwa ‘yan ƙabilar Ibo suna kiran mai yin aski da sunan okpa-isi, wanda yake yin kaciyar maza kuwa suna kiran sa obe-ugwu, wanda yake yin tsagen gargajiya kuma suna kiran sa da sunan ogbu-ichi. Dakarkari waɗanda suke zaune a ƙasar Zuru da kewaye a Jihar Kabi na kiran wanzami da sunan sah’pana ko u’oro.

Idan muka ƙetara a ƙasashen da suke Afrika ta Gabas za mu ga akwai wasu ƙabilun waɗannan ƙasashe waɗanda suke aiwatar da ire-iren ayyukan wanzanci da ake yi a ƙasar Hausa kamar yadda Hausawa suke yi. Wasu daga cikin al’ummomin waɗannan ƙasashe na cire belun-wuya da belun-mata da yin askin suna ga jarirai da dai sauran ayyuka irin waɗanda wanzaman Hausawa suke yi.

An ce kamar yadda wanzaman Hausawa suka gaji yin wannan sana’a, al’ummomin waɗannan ƙasashe masu yin waɗannan ayyuka suna yin gado ne a wurin mahaifansu. Akwai waɗanda suke koyon yin waɗannan ayyuka bayan sun girma, ire-irensu suna bayyana cewa iskoki ne suka sanar da su hikimomin yin waɗannan ayyuka (Hira da JMT da PMT da KMK da AGU a ranar 20/12/2004 da MEHT a ranar 22/12/2004). A Uganda ƙabilun Sabiny da Kapchori, a Kenya kuwa ‘yan ƙabilar Kisii, a Tanzania kuma ‘yan ƙabilar Wakurya ne suke yin ire-iren ayyukan wanzanci na Hausawa.

A gabacin Afrika ana amfani da harshen Swahili a matsayin harshen ƙasa a ƙasashen Uganda da Kenya da Tanzania don yin hulɗoɗin gwamnati da harkokin yau da kullum a tsakanin al’ummomin waɗannan ƙasashe. A saboda haka akwai sunayen da ake kiran wanzami ko mai yin ayyuka irin na wanzami a waɗannan ƙasashe. Misali, ana kiran mai cire belun-wuya da sunan kukata-kilimi, mai yin aski kuma kinyozi.

Shi kuma mai yin kaciyar maza ana kiran sa da sunan tohara ya wanaume, mai yin kaciyar mata kuwa tahora ya wanawake ko ngariba. Shi kuma mai yin tsagar gado ana kiran sa da sunan ndonya ko makonde, mai yin tsagar kwalliya kuwa alama za nyuso (Hira da AGU, a ranar 20/12/2004 da kuma MEHT], a ranar 22/12.2004).

Bayan waɗannan sana’o’i waɗanda mafi yawancinsu maza ne suke aiwatar da su, akwai waɗanda mata ne kawai suke yin su kamar kaɗi wanda ake yi don samar da zare da abawa ga masana’antar saƙa. Haka kuma mata ne suke yin sana’ar kitso ga ‘yan uwansu mata. Suna yin salon kitso iri-iri don yin kwalliya ga kan mata wanda suke ƙara masu kyau da jawo hankalin maza.

Akwai kuma sana’ar tauri ko koda wadda mata suke amso hatsi don yin dakau na fura ko garin da za a yi amfani da shi don yin abinci. Waɗannan sana’o’i waɗanda mata suke yi suna taimaka wa matan yin hidimominsu na yau da kullum da kuma yin bikin dangi ba tare da sun dogara da wani ba.

Shigowar baƙi ƙasar Hausa wato Larabawa da Turawa sun taimaka wa tattalin arzikin ƙasar Hausa ya ƙara bunƙasa.Wannan kuwa ya faru ne ta yadda aka sami shigowar wasu sababbin sana’o’i waɗanda wasun su ci gaba ne ga waɗanda Hausawa suke yi kafin zuwan waɗannan baƙi.

Ire-iren waɗannan sana’o’i sun haɗa da ta makanikanci don yin gyaran kekuna da babura da motoci da rediyo da rikoda da talabijin da kwamfyuta da wayar hannu da dai sauransu. Akwai kuma masana’antar kafinta wadda ci gaba ce ga sana’ar sassaƙa ta gargajiya. Kafintoci na sassaƙa kujerin zama na zamani da tebura da tagogi da ƙofofin ɗaki da yin rufin ɗaki wanda ake amfani da katako da kwanon rufi da dai sauran ayyuka don a ƙara sauƙaƙa rayuwar yau da kulllum.

Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAddinin Mutanen Ƙasar Hausa
Labarin na GabaƘaura Da Shigowar Baƙi Ƙasar Hausa
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.