Ga ta nan, ga ta nanku.
Zomo da Damo suka yi abota, kowa na zuwa gidan abokinsa ya yini ko su yi hira. Rannan Zomo ya je gidan Damo ya tarar yana cin doya, suka ci tare suka ƙoshi. Bayan ‘yan kwanaki sai Zomo ya shirya tasa doyar, ya sa matarsa ta shirya manya-manyan, ya kira Damo cin doya.
Damo ya zo ya ga irin doyar Zomo manya ba ƙanana, ga kuma gari. Da suka gama cin doyar, sai Damo ya tambayi Zomo yadda ya yi doyarsa ta zama manya haka? Zomo ya ce idan lokacin shuka ya yi, ya zo zai gaya masa yadda zai yi. Da lokacin shukar ya yi, sai Zomo ya gaya wa Damo ya kawo irin doyar da zai shuka gidansa duka, kada ya bar ko daya.
Kuma ya tabbatar an dafa doyar duka, kuma ya ɗauki babba daga ciki ya ci. Kada ya ba kowa sai ya je ya shuka. Damo ya yi yadda Zomo ya shawarce shi. Da kaka ta yi kowa yana kawo doya gida, amma Damo in ya je ya haƙa sai ƙasa. Ya rasa yadda zai yi da ƙyar ya nemo musu abincin da zai kai su shekara shi da matarsa.
Damo ya rantse sai ya sha fansar abin da Zomo ya yi masa. Sai ya shirya da uwarsa cewa zai haƙa ƙabari ya sa uwar a ciki kamar ta mutu, kuma za a binne ta, a bar ‘yar ƙofa inda za ta rinƙa miƙa wa ɗanta Damo kayan daɗi irin na lahira. Aka shirya kaf, bayan kamar sati biyu, sai Damo ya je ya gaya wa Zomo yau gyatumarsa za ta kawo masa kayan daɗi daga lahira, saboda haka yana gayyatar sa domin a yi komai tare da shi.
Suka zo wajen ƙabarin uwar Damo, sai ya ce: “Iya ina soki aiko mini babbar riga mai aska takwas da rawani ɗan Kura da dara mai tunta da takalmi ɗan Zariya don za mu biki.” Sai ga dukkan kayan da ya ambata sun fito. Zomo ya yi ta al’ajabi, ya tambayi Damo yaya ake irin wannan abu.
Sai Damo yace da shi, ai da man duk wanda uwarsa take lahira za ta riƙa aiko masa duk irin abin da ya nema. Da Zomo ya ji haka, sai ya fara tunani shi ma me yake jira tunda ga tasa uwar ta tsufa, ba ta yin amfanin komai a nan duniya, gara ta je ta dinga aiko masa da duk abubuwan da yake so daga lahira.
Tun a hanyar komowa gida ya sami kulkin da zai kashe uwarsa. Da Zomo ya je gida ba ko sallama sai kawai ya sami uwarsa ya dinga kwaɗa mata kulkin nan. Nan take ta faɗi ta mutu. Yasa aka yi jana’iza. Bayan an yi bakwai sai ya aika wa Damo ya zo su je wurin gyatumarsa domin ya ga abin da za ta aiko masa daga lahira. Damo ya zo suka je wajen ƙabari.
Zomo ya ce: “Mama, ina so ki aiko mini riguna shuɗiya da fara masu aska shida-shida.” Shiru ba wani abu da ya fito daga ƙabari. Sai Damo ya dubi Zomo ya ce, “In ba hauka ba, wa ya taɓa gani an mutu an dawo?” Ya ƙara da cewa: “Ka manta da abin da ka sa na yi da doyata? “To a cikinsu wa ya fi ƙwaruwa? Zomo ko Damo?
Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
* Ramuwar gayya, ta fi gayya ciwo
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Wata Mata Mai ’Ya’ya Biyu
Edita@rumasau-kallamu









