Ga ta nan ga ta nan ku.
Wata yarinya ce dai mai tsananin kyau, duk garinsu babu mai kyanta, ta ce ba ta son kowa sai maras tabo. Sai dodanni suka ji labari. Sai suka yi wanka a gidan tururuwa. Sai suka zama samari kyawawa da su.
Da ta gan su, sai ta ce ta sami mazan aure. Sai duk ta dube jikinsu, sai ta ga jikin wannan da ɗan tabo ɗan mitsitsi, sai ta ce ba ta son sa. Da ta duba jikin ɗayan ta gan shi sumul ba ko ɗigon tabo a jikinsa, sai ta ce shi ta ke so.
Shi kenan, sai aka shirya aka yi biki. Sai suka ce za su tafi da ita garinsu, su ba mazauna ba ne, Sai aka ce to za a ba ta ƙanwarta ta taya ta zaman ɗaki. Sai ta ce ita ba ta so, ta zauna ita kaɗai. Shi kenan, aka yi aka yi su tafi da ƙanwarta ta ƙi. Sai ƙanwar ta zama ƙuda ta maƙale mata.
Shi ke nan, da suka je gidan dodanni, sai dare ya yi suka shiga ɗaka suka rufe ƙofa. Sai ta ga ƙanwarta, sai ta rufe ta da faɗa, ta ce, ‘Ke wa ya kawo ki nan? Ita kuwa ƙanwar sai ta yi shiru. Shi ke nan sai yar ta ƙyale ta.
Ita yar kamar sokuwa ta ke. In dare ya yi, sai ta yi ta shirga barci. Ita kuwa ƙanwar sai ta zauna tangar har gari ya waye. Sai uwar mijinta ta zo da tsakar dare ta ce:
Sarma-sarma duf-duf.
Sai ƙanwar ta ce:
Wane ne nan ya ke mana Sarma-sarma duf-duf?
Sai uwar mijin ta ce:
Uwar miji ce ta ke mu ku Sarma-sarma duf-duf.
Sai yarinya ta ce:
Me ki ke so ki ke mu ku Sarma-sarma duf-duf?
Sai ta ce:
Wuta na ke so na ke muku Sarma-sarma duf-duf.
Sai yarinya ta ce: Iya ga wuta nan.
Ki bar mana Sarma-sarma duf-duf.
Sai yarinya ta watso mata wutar. Tsohuwa ta je ta kashe wutar ta kuma dawo musu. Nan kuwa ashe ba wuta ta ke so ba. So ta ke yi ta cinye su idan ta tarar sun yi barci. Kullum haka, kullum haka. Duk sa’ad da yarinyar ta gaya wa yarta game da uwar mijin mai zuwa ɗiban wuta da daddare, sai yar ta ce ƙarya ta ke yi.
Ana nan a haka sak, ran nan yarinya ta ce da yarta, ‘To, yau dai ki zauna kada ki yi barci don ki ji yadda mu ke yi da tsohuwar da kunnenki. Shi ke nan, ya ta zauna. Sai ita uwar mijin ta zo ta yi musu irin yadda ta ke yi kullum. Shi ke nan, sai ya ta ji da kunnenta.
Shi kuma mijin nata yana wani ɗaki suna kwance tare da abokansa. Idan an yi abinci na aikin gona an kai musu, sai su yi haka su bunne. Sai su yi ta cin kwaɗi. Ita kuwa ƙanwar, wadda ta kai musu abincin, sai ta ce da su:
Mijin yata, ci kwaɗi.
Mijin yata, ci kwaɗi.
Mazan-wazata, ci kwaɗi.
Sha da kwaɗi, ci kwaɗi.
Sha da kwaɗi, ci kwaɗi.
Su kuma idan sun ji wannan waƙar, sai su yi ta rawa suna cin kwaɗi. Shi ke nan. Da sun ga ƙanwar ta dawo daga gida, sai su zama mutane su ce, ‘Ga kwanukanki nan.
Ki ce muna yi mata sannu da aiki. Shi ke nan. Da sun ga ƙanwar ta dawo daga gida, sai su zama mutane su ce, ‘Ga kwanukanki nan. Ki ce muna yi mata sannu da aiki. Shi ke nan, sai yarinya ta ɗebi kwanuka ta tafi da su gida. Kullum haka, kullum haka.
Sai rannan yar ta yi shawara da ƙanwarta don su gudu gida. Sai suka yi ta haƙa rami, tun daga nan gidan har ya zuwa hanyar ƙofar garinsu. Suna ta bin rami da ita da ƙanwarta har suka je gida.
Iyayenta suka ce da ita, ‘Lafiya?’ Sai ta ce wa iyayenta, ‘Ashe dodanni ne? Ni ca na ke mutane ne.’ Shi ke nan. ƘurunƘus kan ɗan ɓera. Ba don ƙarya ƙarya ce ba, wa zai zuba ruwa a jallo, jallo ya fashe kuma ruwan bai zube ba?
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.
Danna nan don karanta Labarin Kalala Da Kalalatu
Edita@rumasau-kallamu






