Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana ’ya’yan Kura sun je yawo gidan Kurege sai suka tarar an yi farfesun Biri. Sai aka ba su suka ci. Da babban cikinsu ya ji daɗin farfesu sai ya ɗebi romon ya shafa a kan gashin kansa ya tafi gida. Da suka koma gida, sai ya je wurin babansa Kure ya ce: “Baba ka dafa kaina mana. ”Da uban ya ji haka sai ya dube shi ya ce: “Ka taɓa jin an cewa uba ya dafa kan dansa ne?
”Sai ɗan ya nace shi dai uban ya dafa kansa. Sai ya dafa kan, ya ji danshin romo, ya sa harshe ya lashe. Da ya ji zaƙin romo, a nan take ya tambaye su a inda suka sami wannan abu mai daɗi. Suka amsa masa da cewa a gidan abokinsa Kurege aka ba su. Sai Kure ya sa takalminsa ya tafi gidan Kurege ƙwalama. Da ya isa gidan Kurege sai ya tarar saura kaɗan a tukunya.
Kurege ya zuba masa ya ci. Da ya ji daɗi sai ya ce da Kurege: “Ina kake samo wannan nama mai daɗi haka?” Sai Kurege ya amsa masa da cewa: “Muna wasa ne a ruwa kullum tare da birrai, sai in daura tarko a ƙafata. Idan mun shiga mun fara kurme a ruwa sai in kama ƙarami a cikinsu, in danne a ruwa har sai ya sha ruwa sosai ya mutu. In sun tafi sun bar shi, sai in ɗauka in yanka mu yi farfesu a gidana.
”Da Kure sarkin kwaɗayi ya ji haka sai ya ce: “To in gari ya waye gobe zan bi ka.” Sai Kurege ya amince. Da Kure ya tafi gidansa sai ya kasa barci, ya ƙagara gari ya waye. Can dai da ya ga kamar gari ya ƙi wayewa, sai ya hura wuta ta haske ko ina. Daga nan ya je ya faɗa wa Kurege wai gari ya waye, sai Kurege ya ce: “Haba Kure, ka hura wuta a kan dakinka ka ce gari ya waye?
Ai gara ka koma gida sai gari ya waye.” Bayan ya koma gida ya ɗan jima gari bai waye ba, sai ya kama zakara ya rinƙa matsa shi har ya rinƙa yin cara. Da Kurege ya fito sai ya ce: “Haba Kure yaya kake damun kanka haka ne? Na gaya maka sai gari ya waye.” Haka dai Kure ya haƙura ala tilas har sai da gari ya waye. Da sassafe ya shirya ya nufi ƙofar gidan Kurege.
Suka kama hanyar rafi har suka isa, suka tarar da birrai a bakin rafi. Sai Kure da Kurege suka yanke shawarar su shiga cikin ruwa su yi wasan kurme. Da suka shiga tare da birrai sai Kurege ya faki ƙarami daga cikinsu ya danne a ruwa. Shi kuma Kure maimakon ya faki ɗan ƙarami, sai ya nufi kan babba, ya sa masa igiya ya danne shi. Da ya ji Kure zai halaka shi, sai ya yi ƙara, har sauran suka ji, suka watse da gudu.
Kure da Kurege dai kowa ya kaso Biri daya, amma sai Kuregeya ce: “Kai kuma Kure da muka yi da kai za ka kama karami donkada su gane, sai ka kama babban cikinsu?” Sai Kure ya dubi Kurege ya ce masa ai ƙarami ba zai ƙosar da shi ba, shi ya sa ya kama babba wanda idan ya yi farfesu da shi zai sha ya ƙoshi ya more.
Washe-gari da suka koma tun safe har yamma suna jira a bakin rafi babu Birin da ya fito bakin rafi. Sai Kurege ya dubi Kure yace da shi: “Kai ka yi mana wannan ɗanyen aiki.” Rannan dai haka suka koma gida, ba su sami nama ba. Sai Kurege ya gaya wa Kure gobe da safe za su je unguwar birrai su gaishe su domin rashin da suka yi na babbansu.
Da ma birrai sun aika wa Kurege da Kure za su yi taro domin ba su sani ba cewa ko Kure da abokinsa Kurege ne suka kashe musu’yan’uwa. Da gari ya waye suka shirya, sai Kurege ya ce zai hau doki, shi kuma Kure ya hau ɓera. Sai Kure ya ƙi, ya ce tun da shi ne babba shi zai hau doki shi kuma Kurege ya hau ɓeran.
Haka aka yi; suka kama hanya, kafin su isa sai Kurege yace in sun je shi zai ɗaure abin hawansa a jikin bishiya, sai Kure yace shi ne zai ɗaure a jikin bishiya, domin shi ne babba. Sai Kurege yace to shi zai ɗaure nasa a jikin ciyawa. Da suka isa garin birrai aka yi musu maraba, aka ba su masauki, shi Kure ya ɗaure abin hawansa a gindin bishiya, shi kuma Kuregeya ɗaure nasa abin hawan a jikin ciyawa.
Suna zaune a masauki aka ce za a kawo musu giya don liyafar baƙunta. Kafin a kawo sai Kurege ya ce ya kamata su yi waƙa. Suka fara waƙa. Kurege yana rerawa yana cewa: “Ni da ƙananan nake wasa, Da ƙananan nake abota.” Shi kuma Kure yana waƙa yana cewa: “Ni da babban nake wasa, Babba na kama, A wasan ruwa mai daɗi” Sai manyan birrai suka ji abin da Kure yake faɗa, sai suka kawo musu giya a ƙwarya.
Kure yana ta sha, Kurege kuma ya yi kamar tare suke sha amma in ya zuba a ƙoƙo sai ya kwara a jikin shinge, shi kuma Kure ya yi ta shan giya har ya yi tilis. Su kuma manyan birrai suna ta shiri don su rama abinda Kure da Kurege suka yi musu. Nan take birrai suka ƙwala ihu, suka ce a kawo sanduna za su ɗauki fansa. Suka ɗebo sanduna suka nufi kan Kurege da Kure.
Shi kuma Kure ya riga ya yi tilis da giya ta yadda ba ya jin abinda ake faɗa. Sai ya tambayi Kurege ko me suke cewa a waje? Sai Kurege ya gaya masa cewa an ce a kawo musu farfesun ƙashi da nama. Da Kure ya ji haka sai ya gyara zama, yana dariya da murna wai za a kawo musu nama da ƙashi. A daidai lokacin da birrai suka shigo da sanduna za a fara ma Kurege da Kure, sai Kurege ya kutsa ta jikin shinge, inda yake kwarar da giya, ya gudu.
Kure kuwa ba zai iya gudu ba, saboda haka suka yi ta jibgar sa. Bayan Kurege ya fita ta baya, kafin su biyo shi har ya hau kan ɓera. Yana taɓa shi sai ya fara gudu. Shi kuma Kure kafin ya fito ya kwance dokinsa daga jikin bishiya, ya rigaya ya sha sanduna har ya faɗi ya suma. Suka ɗauke shi, suka ɗora shi a kan dokinsa, suka kora shi gida. Ya isa gida a galabaice, ya yi ta jinya da kyar ya warke. Ƙurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Kwaɗayi mabuɗin wahala.
- Son zuciya, ɓacin zuciya
Wannan tatsunya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Daya)
Edita@rumasau-kallamu







