Ga ta nan ga ta nan ku.
Kaza ce dai ta ce ba ta son kowa a cikin duk ‘yan uwanta zakaru masu nemanta. Ta dage ita sai muzuru kawai ta ke so da aure. Iyayenta ma suka ce ba za su ba ta shi ba. Ita kuma ta ce shi take so.
Da suka ga ta dage, sai suka ce, ‘To, mu dai babu ruwammu. Kada ki je ki jawo mana abin da zai hallaka mu baki ɗaya. Kaza kuwa ta ce ita dai shi ta ke so, ba za ta sake ba.
Sai aka kirawo ƙawayenta suka rarraba goron biki. Shi ke nan, aka yi biki. Sai ‘yammatan amarya suka je suna waka suna cewa:
Ke kaza kar ki jawo mana tserereninya da muzuru.’ Sai kaza ta ce: ‘Shi ba ya cin kaji, mhn. Shi ba zai ci kaji ba, mhn. In ji dai ni na kai kaina, mhn.’
Shi ke nan, sai suka ce da makaɗin ya sauya musu kiɗa. Shi kuwa makaɗin zakara ne, saboda a dangin amarya ya ke. Sannan ga kuma angwaye muzurai sun jeru, suna jin waƙa.
Shi ke nan, sai ‘yar ƙaramar kaza ta shiga fage ta ce:
‘Ni auta, autar kaza,
In waiwaya haka,
In muskuta haka,
Sai na kan ji kiɗan da daɗi.’
Sai ta fita. Wata kuma ta shiga ta ce:
‘Ni wake-waken kaza,
Kazar da ba a duka,
Kazar da ba a zagi,
In waiwaya haka,
In muskuta haka,
Sai na kan ji kiɗan da daɗi.’
Shi kuma makaɗin zakara, yana cewa:
’Daga baya-baya nake tsaya, In na ji kaya-kaya in naƙe.’
Sai kuma kaza ta uku ta shiga ta ce:
‘Ni ja-ja ja-jar kaza,
Kazar da ba a duka,
Kazar da ba a zagi,
In waiwaya haka,
In muskuta haka,
Sai na kan ga idon muzuru!’
Daga nan fa sai angwaye muzurai suka yiwo kan ‘yan biki kaji radadada. Muzurai suka fara ciran su kai, su fafa, su fukafiki na kaji. Ita kuwa amarya sai cewa ta ke yi, ‘Kar ka cire mini fukafiki. Kar ka cire mini kai.’ Suka isa gida da ƙyar, suna cewa: Ga shi ta jawo mana tsiya. Wanda bai ji bari ba, zai ji hoho. An ce ta bari ta ƙi.
Kurunkus kan ɗan kusu.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin Tatsuniyoyi Da Wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya Ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Kura Da Zomanya
Edita@rumasau-kallamu









