Tatsuniyar Gizo Da Matarsa Ƙoƙi

0
30

Ga ta nan, ga ta nanku.

Wata rana Koƙi matar Gizo ta fito fili ta matsa masa a kan zancen gona da amfanin yin noma. Gizo ya yi fushi, amma duk da haka ya je kasuwa ya auno tiya biyu ta irin gujiya ta shukawa. Da damina ta faɗi aka yi isasshen ruwa, sai ya ce da Koƙi ta je ta soya irin. Ta so ta yi masa musu, amma sai ta kanne, watau ta danne zuciyarta, ta je ta soya da gishiri
kaɗan.

Kamar da gaske, tun da asubar fari Gizo ya ɗauki sunguminsa da goransa cike da fura, sai gona. Yana isa gona sai ya je ya sami itaciya babba, mai cikakkiyar inuwa sansanya, ya zauna, ya buɗe burgamin irin gujiya da aka soya masa, ya dumbuzo, ya sa abinsa a gaba ya ci har ya yi nak.

Sai ya ɗauki goran fura ya kaɗa, ya kwankwaɗi abinsa, ya yi gyatsa, ya yi rigingine, sai barci. Yana ta sharar barci har la’asar sakaliya ta yi. Da ya farka daga barcinsa, sai ya je kogi ya yi wanka, ya koma gida. Haka ya yi ta yi har gujiyata ƙare, matar tana ta yi masa sannu da aiki.

Da kaka ta yi, kowa ya fara kai amfanin gona gida, amma Gizo bai kawo ko da ƙwaya ɗaya ba, sai matar ta tambaye shi zancen amfanin gona. Sai ya fara zuwa gonar Sarki yana ta labto gyaɗa yana kawowa gida suna ta tsinke ’ya’yan shi da matarsa Koƙi. Kowa a gari ana ta yin mamakin amfanin gonar da ya samu.

Ana nan, sai rannan Sarki ya hau ya je gonarsa gewaya, amma sai ya ga gona kusan ba komai a cikinta. Da ya tambayi bayin da ke kula da gonar da maƙwabtansa na gona wane ne ya farɗe masa gyaɗa, sai suka ce ba su ga kowa ba. Sai ya nemi shawararsu a kan yadda za a gane mai ɗibar amfanin gonar Sarki ba izininsa.

Kowa ya kawo shawara da dabararsa, amma Sarki ya ga duk ba wadda ta dace. Sai ya kawo tasa dabarar, suka amsa. Shawarar kuwa ita ce, ya sa aka tara ɗanƙo mai yawa, kuma aka yi masa mutum-mutumi irin ta kyakkyawar budurwa, kamar ka ce tashi mu tafi. Aka je aka sa mutum-mutumin nan a tsakiyar gona. Da safe Gizo ya je gona kamar yadda ya saba, ya ɗebi gyaɗa, ya tsaya yana gyaran gammo, can sai ya hangi mutum-mutumin.

Sai ya jefar da gammo ya je wurinta, ya ga budurwa tana yin murmushi, zato yake tana yi masa ne. Cikin murmushi ya matsa kusa da ita ya yi mata magana, ba ta kula ba. Gizo dai sai ya ga kamar araha ta samu, sai ya matsa ya kai hannu ya taɓa mamanta. Nan take hannunsa ya maƙale, ya kai mari da na hagun, sai shi ma ya maƙale.

Ya kai shuri da ƙafa, ita ma ta maƙale, ya rungume ta da ƙirji ya maƙale, suka faɗi rigingine ba damar tashi, ga shi ba a fara zafi ba, balle ɗanƙo ya narke. Can sai ga Biri ya iso, sai ya ce: “Yaya ne Gizo?” To, ga shi nan dai, Biri ya ga halin da Gizo yake ciki, tarko ya kama shi sai ya ce: “Tsiyarka Gizo, na san halinka in an yi maka rana, sai ka yi wa mutum dare.”

Gizo ya yi ’yan rantse-rantsensa na ba zai cuci Biri ba, sai Biri ya kuɓutar da shi ya ɓalle shi amma shi ya manna kansa a jikin budurwar ɗanƙo. Da Gizo ya sami kansa sai gidan Sarki, ya durƙusa yace da shi, “Ranka ya daɗe, na kama maka ɓarawo”. Aka je aka kama Biri. Shi
kuma ya yi ya yi, ya faɗi yadda aka yi, amma ina, an hana shi damar yin magana.

Amma da yake Allah yana bayan mai gaskiya, sai wani Zagodo ya zo ya gaya wa Sarki yadda aka yi domin a gaban idonsa aka yi komai. Sarki ya ce Zagodo ya je ya kira Gizo. Zagodo ya je gidan Gizo ya tarar yana cin abinci, sai ya yi masa tayi, ya zauna kuma sai da ya yi ƙat, aka ƙara masa har ba ya iya magana. Gizo ya yi masa magana, sai kaɗa kai kurum yake iyayi.

Da Gizo ya tabbatar ba ya iya magana sai ya ce su tafi wajen Sarkin. Da suka isa, sai Sarki ya ce wa Zagodo, ya faɗi maganarsa. Zagodo ya kasa magana, sai kaɗa kai yake yi kurum. Sarki ya yi fushi ya sa a je a yanka Zagodo da Biri. Gizo kuwa ya ci bulus, sai kawai ya yi ban kwana da Sarki, ya koma gidansa, inda shi da matarsa Koƙi suka yi ta amfani da gyaɗarsu. Duniya ke nan. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Duk wanda ya daka ta Gizo sai ya kwan ciki.
  • Illar yin katsalandan ga abin da bai shafi mutum ba.
  • Ƙarancin bincike kan jawo rashin adalci a shari’a.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Zomo Da Damo

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Ake Addu’ar Barka Ga Wanda Aka Yi Wa Haihuwa
Labarin na GabaYadda Ake Addu’ar Nema Wa ‘Ya’ya Tsari
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.