Ga ta nan ga ta nan ku.
Wani mutum ne dai ya ba wani malami kuɗi don a yi masa asiri. Sai malamin ya ce sai an samo hauren giwa domin ya haɗa maganin da shi. Sai mutumin ya je cikin jama’a ya ce, ‘Wa zai iya samo min hauren giwa in ba shi kuɗi? ’Aka rasa wanda zai iya. Sai Gizo ya ce shi zai iya.
Sai mutumin ya ce, ‘To shi ke nan sai ka samo ka kawo.’ Shi ke nan, sai Gizo ya je gida ya daka nakiya mai zaƙin gaske. Sai ya je gidan giwa da ɗan ƙunshin nakiyar a hannunsa, ya ce, ‘Gafaya dai.’ Sai giwa ta ce, ‘Maraba da Gizo.’
Ya ce, ‘Yauwa. Wata nakiya ce na kawo miki da na samo a pa.’ Shi ke nan sai giwa ta ce, ‘To’. Ta gutsiri nakiya ta kai bakinta. Da ta ji zaƙin nakiyar, sai ta ce, ‘Don Allah Gizo, ni ma ka raka ni in je in samo?’
Sai ya ce, ‘Haba yaya! Me zai hana? Ki zo gobe in kai ki.’ Shi ke nan, sai ta zo washegari suka je wajen kan pa. Sai ya ce da ita, ‘Idan kika doka bakinki sau ɗaya, kika doka sau biyu, a na ukun sai ki ga nakiya rubus a bakinki.’ Shi ke nan, sai giwa ta doka bakinta sau ɗaya fas a kan pa. Ta kuma dokawa.
Da ta doka na ukun sai haƙorinta ya balle ya faɗo ƙasa. Sai jini shar. Sai Gizo ya ce, ‘Assha, assha. Yaya aka yi haka kuma?’ Ya yi maza ya ɗauki haƙorin giwar ya sa a aljihunsa. Ita ba ta gani ba. Tana ta kanta.
Shi ke nan sai gizo ya bar giwa a nan. Ya yi sauri ya kai wa mutumin nan haƙorin. Mutumin ya ba shi ladansa. Sai gizo ya je daji ya tattara namun daji suka je gidan da giwa ta ke a kwance. Suka tarar kanta ya kumbura, suntum.
Sai gizo ya gaya wa namun dajin, ‘In na ce, “Babbanmu da giɓi,” ku ce, “Ɓurum ɓaɓurka.”’ Sai ya fara waƙar: Babbanmu da giɓi. Sai suka amsa: Ɓurum ɓaɓurka. Shi ke nan sai suka gama, suka koma. Gizo ya bar giwa a wahala. Shi kuwa ya karɓe kuɗinsa.
Shi ke nan. Kurunk us.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum
Edita@rumasau-kallamu









