Tatsuniyar Gizo Da Ɓaure

0
26

‎Ga ta nan ga ta nan ku.

‎Wata rana ne dai wani sarki yana zance a zuci, yana cewa, ‘Gonata ta ɓaure ta yi kyau. Ɓauren yanzu duk ya nuna. Gara in sami wani ya je ya tsinke mini duk ɓauren, kar in bar shi ya ruɓe a banza. Amma fa wanda zai tsinke ɓauren ba zai sha ba, ko da ɗaya ma.

Idan ya gama bai sha ba, zan ba shi ‘yata tare da gararta baki ɗaya’. ‎Shi ke nan. Kashegari sai sarki ya sa duk a yi shela a gaya wa mutanen gari sarki yana kiran su a ƙofar fada.

‎Mutane suka taru a ƙofar gidan sarki. Sai sarki ya ce, ‘Da ma ba wani abu ya sa na yi kiran ku ba. Gonar ɓaurena ce na ke so a tsinke min, amma ba za a sha ko ɓaure ɗaya ba. Sai dai zan ba wanda ya tsinke ɗin ladan tsinkewar. Watau zan ba shi ‘yata da gararta baki ɗaya.’

‎Sai kowa ya ce ba zai iya ba, domin bauren ya cika kyau, ga kuma ƙanshi da zaƙi. Ba wanda zai iya ba tare da ya sha ba. Can, sai Gizo ya zo; ya ce wa sarki, ‘Zan iya. ‎Shi ke nan, sai sarki ya ce, ‘To. Gobe ka yi shiri ka tafi’.

‎Da gari ya waye, sai Gizo ya dura ruwa a jallo, ya ɗauki madubi da kuma tsinkensa na sakace. Ya je gonar sarki ya kama tsinkar ɓaure. In yana cikin yi mutane suka zo suka ce, ‘Gizo barka da aiki’; sai ya tsiri tofar da yau, yana cewa, ‘Tuf! Kai wannan ɓaure! Ko warinsa ba na so’.

‎Idan sun wuce, sai ya ci gaba da tsinkar ɓauren, yana sha yana zubo wani a ƙasa. Shi ke nan, ashe bai sani ba, wata ‘yar tsuntsuwa tana kallon sa. Da ya gama tsinkar ɓauren tas. Ya sauko zai tafi gida, sai ya ɗauko jallon ruwansa ya kurkure bakinsa, ya ɗauko madubin nan da tsinken sakace, duk ya ciccire ɓauren da ya maƙe masa a haƙorinsa.

Bakinsa ya yi tas, kamar bai ci kome ba. Sai sarki ya aiko mutane don su debe ɓauren da Gizo ya tsinke. Suka zo suka sami Gizo suka ce, ‘Sannu da aiki, Gizo’. ‎Ya ce, ‘Yauwa’. ‎Suka ce, ‘Har ka gama? Sai ya ce, ‘I. Amma da ƙyar’.

‎na gama. Kamar na yi amai, saboda warin ɓauren nan. Warin duk ya cika mini ciki’. ‎Sai suka zuzzuba ɓauren a buhunhuna suka tafi su kai wa sarki. Da suka je gida, sai sarki ya tambaye su labarin Gizo da tsinkar ɓaure. Suka ce, ‘Ai, yallaɓai, Gizo bai sha ɓauren nan ba, domin mun ga muna zubawa a buhu yana tofad da yau..

Kuma da muka ce da shi, ‘Me ya sa ka ke zubad da yau?’ Sai ya ce warin ɓauren ne ya cika masa ciki. Sun gama faɗin haka ke nan, sai ga Gizo ya zo gidan sarki. Sarki ya ce da shi, ‘To, Gizo. Ka yi aiki mai kyau. Sai kuma ka je gida ka gyaggyara, za a kawo amarya da gararta.’

‎Shi ke nan. Gizo ya je gida ya gyaggyara sarai. Aka ɗauko amarya da gara aka zo da ita gidan Gizo. Kafin ‘yan ɗaukar amarya su tafi gida, sai suka ji tsuntsuwa tana waƙa tana cewa: ‘Kai Gizo, kai Gizo, A can ka ci ɓaurenka, Har ka kurkure bakinka, Har ka manto jallonka…’

‎Tana ta faɗar haka har sai mutanen suka ce, ‘Kai, ku tsaya mu ji abin da tsuntsuwar can take faɗa. ‎Sai Gizo ya ce da su, ‘Kai, ku rabu da ita don Allah, shirmenta ta ke yi’. ‎Sai mutanen suka ce, ‘Wane irin a rabu da ita? Kai! Mu tsaya mu ji’.

‎Shi ke nan, sai ‘yan kawo gara da amarya suka ji tana cewa: ‘Kai Gizo kai Gizo, A can ka ci ɓaurenka, Har ka kurkure bakinka, Har ka manto jallonka…’‎Sai suka ce, ‘La’ila! Ashe da ma ka ci ɓauren ka ce ba ka ci ba?’

‎Sai suka yi ta surutu da hayaniya. Shi ke nan. Sai suka mayad da amarya da gararta gida su ka gaya wa sarki abin da ya faru.

‎Shi ke nan. Ƙurunƙus

‎Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

Danna nan don karanta ‎Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuce‎Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum
Labarin na GabaTatsuniyar Ɗankaɗafi
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.