Ga ta nan ga ta nan ku.
Da gero da dawa da maiwa da duk dai kayan abinci haka, su shinkafa, acca, iburu, alkama da burtuntuna, sai suka shirya za su tafi gun wani saurayi wanda ya ce duk wata wadda ta faɗi sunansa, ita zai aura.
Shi ke nan. Ko wacce ta ci kwalliya. Ita kuwa burtuntuna ba ta yi kwalliya ba don ba ta da kayan ado. Suka kama hanya suna tafiya. A kan hanyar da su ke wucewa sai suka ga wata ‘yar tsohuwa a tsugunne da ruwan wankanta.
Sai tsohuwa ta ce da dawa, ‘Don Allah yarinya, zo ki cuɗa ni mana? Sai dawa ta ce, ‘A, don Allah ku ji tsohuwa? In yi kwalliyar tawa haka sannan ki ce in zo in cuɗa ki? Sai ta wuce ta ki cuɗa ta.
Sai kuma shinkafa ta zo, tsohuwa ta ce da ita, ‘Don Allah yarinya zo ki cuɗa ni mana? Sai shinkafa ta ce, ‘Duk wannan kwalliyar tawa in tsaya in cuɗa ki?’ Sai ta ki cuɗa tsohuwa, ta shige abinta.
Sai su maiwa, su gero, su alkama suka zo da dai dai, kowacce tsohuwa ta tambaya ta cuɗa ta sai ta ki, ta yi wucewarta. Daga nan sai ga burtuntuna ta zo. Sai tsohuwa ta ce da ita, ‘Yarinya don Allah zo ki cuɗa ni mana?’
Sai burtuntuna ta ce da ita, ‘To.’ Ta shiga cuɗa ta. Tana cikin cuɗa ta, sai bayan ‘yar tsohuwa ya burme Yarinya ta ce, ‘Yau na shiga uku, na lalace. Sai ‘yar tsohuwa ta ce, ‘Mene ne?’ Burtuntuna ta ce, ‘Bayanki ne ya ɓurme.’
Sai ‘yar tsohuwa ta ce, ‘Me kika gani a ciki?’ Ta ce, ‘Na ga kwatashi guda biyu, babba da ƙarami. Ta ce, ‘To, ɗauko ƙaramin.’ Burtuntuna ta ɗauko ƙaramin kwatashi. Sai tsohuwa ta ce, ‘To, ajiye nan.’ Burtuntuna ta ajiye.
Can sai tsohuwa ta haɗiye burtuntuna. Ta mai da ita fara, ta fito da ita waje, ta duba ta ta ce, ‘Kai, ba haka na ke son ki ba. Sai ta sake haɗiye ta, ta mai da ita ja zur kamar tsada, ta fito da ita waje ta duba ta ta ce, ‘Yauwa, haka na ke son ki.’
Sai ta buɗe ɗan kwatashin nan, ta ba burtuntuna kayan ado irin na mata kamar su zannuwa, su fatala, su yari, su awarwaro. Burtuntuna ta ci ado da su. Da ta gama adon, sai tsohuwar ta ce, ‘To, ga shi na shirya ki. Kin san sunan yaron da za ku wurin sa?’ Ta ce, ‘A a, ban sani ba.’
Sai tsohuwa ta ce, ‘Sunansa Daskin-da-riɗi.’ Sai ta ce, ‘To. Sai ta yi godiya, suka yi sallama. Shi ke nan. Sai burtuntuna ta tafi ta sami sauran ‘yan’uwanta a hanya. Da suka gan ta sai suka dinga cewa, ‘Kun ga waccan shegiyar.
Wa ya ba ta aron kaya ta ɗaura?’ Sai kuma su ce, ‘Wa ya sani ne? Mu yi maza mu je kada ta riga mu. Ko da ya ke ma ko ta je me zai yi da ita? Shi ke nan. Da suka je, sai suka jajjeru. Dawa ta fara zuwa kofar gidan saurayin. Ta ce:
‘Assalam alam ɗan yaro.
Assalam alam.’
Sai ya ce:
Wane ne nan ya ke mana,
Assalam alam?
Sai ta ce:
Dawarku ce ta ke maka Assalam alam.
Mai tuwo da daɗi, ni dawa Mai tuwo da daɗi
Sai ya ce:
Na ji naki suna yarinya, Ba ni nawa suna.
Sai ta ce:
Ban san ka ba, ɗan yaro. Ban san ka ba.
Sai ya ce:
Da ba ki san ni ba, yarinya, Koma da baya ki sha kuka.
Dawa sai ta koma da baya ta yi ta kuka saboda ba ta san sunan saurayin ba, kuma babu damar ta aure shi ke nan.
Sai kuma ga su maiwa, da gero, da iburu, duk dai suka zozzo. Kowacce ya ce ta faɗi sunansa, sai ta ce ba ta san shi ba. Suka yi ta kuka. Shi kuma ya ce sai wadda ta san sunansa zai aura.”
Shi ke nan, nan sai ga burtuntuna ta zo: Sai suka ce da ita; ‘Ke don Allah, mu ma ba mu san sunansa ba, balle ke! Sai ta rabu da su. Sannan sai ta je kofar gidan saurayin ta ce:
Assalam alam, dan yaro.
Assalam alam.
Sai ya ce:
Wace ce nan ta ke mini Assalam alam?
Sai ta ce:
Burtuntunarku ce ta ke maka Assalam alam.
Burtuntuna, ai ni ce, Mai ɓata kaya.
Sai ya ce:
Na ji naki suna, yarinya. Ba ni nawa suna.
Sai ta ce:
Daskin-da-riɗi dan yaro Daskin-da-riɗi.”
Sai ya ce:
“Buɗe ki shigo, yarinya, Buɗe ki shigo.”
Shi ke nan sai ta buɗe ta shiga. Sai kuma sauran su dawa, su gero, su iburu su ke cewa, ‘Ni zan yi miki wanka.’
‘Ni zan yi miki wanke-wanke.’
‘Ni zan yi miki alwala.’
‘Ni zan yi miki shara.’
Da sauran abubuwa dai na barance. Sai burtuntuna ta yarda suka zama barorinta. Shi ke nan. Ƙurunƙus.
Wannan tatsuniyar an ciro ta ne daga littafin Tatsuniyoyi da Wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Budurwa Marar Tabo
Edita@rumasau-kallamu










