Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wata yarinya kyakkyawa, wadda ko tabo ɗaya babu a jikinta. Shi ke nan, sai ta ce ita fa ba za ta auri wanda yake da tabo ko da ɗaya ne tak a jikinsa ba. Manema wannan ya zo, wancan ya zo, amma duk suna da tabo.
Ana nan, sai ga wani saurayi wai shi Ɗandisheri wanda ba shi da tabo a jikinsa, in ban da wani ƙarami a kan ɗan yatsansa, shi ma ya je saran itace ne ya yi sartse. Da ya je, sai ta ce ba ta son sa. Ya haƙura.
Rannan sai wani maciji ya ji labarin halin wannan budurwa, ya gayawa abokansa, suka rikiɗa suka zama mutane samari kyawawa, waɗanda ba ɗaya daga cikinsu wanda yake da tabo ko ɗaya a jikinsa. Sai suka je wurinta, ta bincike kowannensu sarai, ta ga babu tabo a jikinsa.
Nan take ta ce ta yarda ɗayansu ya aure ta. Aka taru aka ɗaura aure da ɗayansu. Shi ke nan ta tattara kayan ta suka tafi da amaryarsu. Da suka je jeji sai suka ce: “Yawwa mun iso gida.” Ita ko tace: “Ina gidan a nan?” Sai suka ce da ita: “Ai nan ne gidan. Amarya ta yi zuru-zuru, babu yadda za ta yi domin ta riga ta auri ɗayansu.
Kuma ga shi sun kai ta dokar daji, inda ba za ta iya komawa gari ba. Daga nan suka saka ta a kogon bishiya, suka rikiɗe macizai suna lasar jikinta har ta zama fara fat, babu kyan gani, kuma abin ƙyama. Ana nan kwanci-tashi har ta sami ciki. Bayan wani lokaci mai tsawo, sai wata rana Ɗandisheri suka yi ƙarancin ciyawar akuyarsu, sai ya tafi can cikin ƙungurmin jeji yana yankan ciyawa.
Sai matar macizai ta hango shi, ta fara rera masa waƙa tana cewa:
“Ɗandisheri – Ɗandisherina,
Ɗandisheri ƙanin Babati.
Idan ka je gida ka gai da iyata,
Idan ka je gida ka gai da Babati.
Ni mai zaɓar maza babu tabo,
Ga ni yau a kogon kukati,
Maciji na lasa ta mulai,
Kunama na harbi na mulai.
“Sai Ɗandisheri ya ɗau waƙa, ya amsa mata yana cewa:
Ina ruwan Ɗandisheri,
Daga fari ke aka bai wa ni,
Daga gani sai kika raina ni,
Domin tabon ɗan yatsana.
Da ya je gida sai ya gaya wa iyayenta halin da take ciki. Da suka ji labari, sai suka yi shiri domin su je su gani. Da suka je sai suka same ta a cikin kogo. Suka rasa yadda za su fito da ita. Dole aka sare bishiyar, aka fitar da ita, iyayen suka tafi da ita gida.
Daga baya ta haifi ɗa namiji, rabin jikinsa ɗan mutum, rabi ɗan maciji. Da mazanta macizai suka ji ta haifu sai suka ƙara zama mutane, suka zo karɓar ɗansu. Da suka isa gidan, sai danginta suka tona makeken rami, aka shimfiɗa musu tabarma a kai, aka kuma hura wuta a ƙarƙashi, aka yi wa ɗansu wanka aka yi masa kwalliya aka kira su, suka zauna suka karɓi ɗansu.
Suna cikin hira sai su ji ‘nyas-nyas,’ sai suka ce: “Kai akwai abin cizo a gidanku?” Masu gida suka ce: “E wallahi. Jim kaɗan sai tabarma da yayin suka kama wuta, su da shimfiɗar suka faɗa cikin wutar. Yayin da suke ƙonewa sai suka wurgo yaron sama, aka cafe shi, aka ƙara wurga musu, haka dai suka yi ta yi har suka ƙone rumus da su da ɗansu.
Da ba domin Gizo ba da na yi muku ƙarya. Ƙurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Mai ruwan ido gama kasuwa da yawo.
- Jiki magayi.
- Ƙarya fure take ba ta ‘ya’ya.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Jarumin Sarki
Edita@rumasau-kallamu









