Ga ta nan, ga ta nanku.
Wani Sarki ne mai mata uku, amma Allah bai taɓa ba shi haihuwa ba. Ana nan, ana nan wata rana sai ya nemi shawarar fadawansa a kan abin da ya kamata ya yi saboda wannan rashin haihuwa. Sai suka ce ya kamata ya ƙara aure. Shi ko ya ɗauki shawararsu, ya sa aka nema masa budurwa kyakkyawa ya aure ta.
Bayan wasu ‘yan watanni sai Allah ya ba ta ciki, labari kuma ya gama ko ina, matar Sarki tana da ciki. Su kuwa kishiyoyinta sai suka shiga baƙin ciki, don sun daɗe a gidan Sarki ba tare da ko ɗaya daga cikinsu ta sami ko da ɓatan wata ba. Daga nan sai suka shiga neman hanyar da za su bi su zubar da cikin, amma abu ya gagara, har lokacin haihuwa ya zo.
Lokacin da suka tabbatar ta kusa haihuwa, sai suka je wurin Sarki suka nemi izini su je shan iska da saran itace a jeji tare da bayinsu. Ba tare da wani mugun zato ba, sai Sarki ya ba su izini, amma da sharaɗi, ba za su je da amaryarsa mai juna biyu ba. Sai suka ce ai za su kula da ita, kuma babu abin da zai same ta.
Da suka nace, sai Sarki ya bar su suka tafi jeji da ita. A dajin nan naƙuda ta kamata, suka kai ta gindin bishiya, suka kwantar da ita, ta haihu. Da suka ga ta haifi ‘ya kyakkyawa, kuma ba ta cikin hayyacinta, sai suka ɗauki jaririyar suka jefa a kan bishiya. Can da rana ta yi sanyi, sai su da bayinsu suka kama hanyar gida, tare da mai jego.
Lokacin da suka isa gida, sai matan Sarki suka je turakarsa, suka gaya masa wai matarsa ta haifi wani ɗan itace ne, ba mutum ta haifa ba. Da jin wannan bayani sai ya fusata, domin ya ɗauka gaskiya suka gaya masa, ya sa aka kai amaryarsa wani gida ita kaɗai inda ba kowa, sai abin tsoratarwa, aka bar ta a can.
Bayan wasu ‘yan watanni sai bayin Sarki suka je daji yankowa dawakin Sarki ciyawa. Suna cikin yankan ciyawa sai wata ‘yar tsuntsuwa ta zo ta sauka a kan bishiya, ta tarar da ‘yar yarinya. Sai ta fara waƙa tana cewa: “Ɗan tsuntsu kar ka faɗa kan ‘yar Sarki, Wadda kishiyoyi suka ce, Wai ɗan itace uwarta ta haifa, Suka jefa ta kan bishiya, Ba ɗan itace ba ne, ‘Yar Sarki ce.
“Ta rinƙa maimaita wannan waƙa, har bayin Sarki suka ji wakar ‘yar yarinya ta kan bishiya. Wannan ya sa suka fita da gudu, suka koma gari. Washe-gari ma da suka koma yankan ciyawa sai suka ji waƙar. Da suka kasa kunnuwansu da kyau, suka kuma saurari waƙar ‘yar yarinya, sai suka koma gida suka gayyaci mutanen gari masu yawa, domin su ma su je jejin su ji.
Mutanen gari suka saurari waƙar da tsuntsuwa ke yi wa yarinya. Daga nan fa suka koma gari, suka je suka sanar da Sarki abin da suka ji. Sarki ya tashi da kansa ya nufi jeji inda yarinyar take, yasa aka hau bishiya a ga ko me yake yin wannan waƙa. Da aka hau bishiya sai ga yarinya kyakkyawa mai kama da Sarki, sai ka ce kakinta ya yi.
Bayan an sauko da ita Sarki ya gan ta, nan da nan ya rungumi ‘yarsa, yana ta salati irin na godiya ga Allah, yana sumbatar yarinyar nan, don ƙauna irin ta ‘ya da mahaifi. Bayan wannan nuna murna ta Sarki da amsar barka da arziki daga jama’arsa da ke wurin, sai ya sa aka kawo masa doki ya hau, aka miƙa masa ɗiyarsa, suka hau doki tare, shi da ɗimbin jama’a suka kama hanyar gari.
Da suka isa gida sai ya aika aka kawo masa uwar yarinyar da aka kai can wani gida da ke bayan gari, yana cike da nadama, amma kuma a cikin muryar bayyana farin ciki, ya ba amaryar haƙuri, ya nemi ta yafe masa horon da ya yi mata ba tare da laifin ta ba, a sakamakon makircin kishiyoyinta.
Bayan fada ta cika ta batse da mutanen gari, sai aka bayyana musu miyagun halaye da makircin sauran matan Sarki, da yadda suka sa Sarki ya hori matarsa ba tare da ta yi masa laifi ba, da kuma yadda suka jefa da ‘yar Sarki a daji. Nan take Sarki ya umarci
Hauni da ya fille musu kawuna, aka je aka zuba su a rami, aka binne. Sarki kuma ya ci gaba da sabuwar rayuwa shi da amaryarsa da’yarsa. Da ba domin Gizo ba da na shara muku ƙarya. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Mugun nufi ba ya kashe ɗan kurciya.
- Ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Ƙawancen Kyanwa Da Bera
Edita@rumasau-kallamu







