Tatsuniya Mai Taken Marainiya

0
5

TASKAR TATSUNIYOYI”. Babi Na Daya: Marainiya

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wata yarinya marainiya, watau wadda take ba uwa ba uba; kuma ita kaɗai ce a wurin mahaifiyarta, lokacin da mahaifanta suka rasu suka bar ta. Ta sha wulaƙanci a wurin kishiyar uwarta, wadda take da ‘ya’ya maza da mata, waɗanda duka suka taru a kanta suka rika yi mata wulaƙanci.

A cikin wannan yanayin kullum da sassafe takan je gindin wata bishiyar kurna ta zauna, ta yi ta kuka. Wannan kurna tana yin ‘ya’ya masu yawa, ga kuma zaƙi zaƙwai. Abincinta ke nan daga safe har yamma, kuma idan za ta koma gida sai ta ɗebo waɗanda za ta ci da dare.

To akwai wani dan sarki kyakkyawa, mai suna Aminu, wanda ‘yar kishiyar uwarta take so, to amma shi kuma ba ya son ta. Shi ma kuma yakan je shan iska, ya hau kan wannan bishiyar kurna da marainiyar take zama a gindinta, ta sha ‘ya’yanta, yana kallon kowa, amma babu wanda zai gan shi don ganyen bishiyar ya ɓoye shi.

Shi ke nan, wata rana marainiya tana zaune sai ɗan sarki ya sauko daga bishiya sai ya ce: “Sannunki ‘yan mata.” Sai ta ce: “Yauwa samari.” Aminu ya ce: “Me ke damun ki ne? Kullum sai in zo in gan ki a gindin wannan bishiya, har ma domin tunanin da kike yi ba ki sanin zuwana, kuma ga shi kikan riga ni zuwa don ni sai da la’asar nake zuwa, har in hau bishiya ba ki gan ni ba.”

“To yaya kake zama a kan bishiyar kurna mai ƙaya?” Ta tambaye shi. Sai ya ce: “Ni na san dabarar da nake yi.” Haka dai suka ci gaba da hirarsu har ya kawo ga maganar aure, sai ta ce: “Ni dai marainiya ce, ba ni da uwa, ba ni da uba.” Sai ɗan sarki Aminu ya ce: “Yau na zama uwa da uba a wurinki.” Suna nan yana kiran ta, har ya fara zuwa gidansu marainiya.

Da ‘yar kishiyar ta gane dan sarki ne yake zuwa wurinta, sai ta ce ta san makircin da za ta yi. Sai ta sayo allurai da yawa ta je ta sossoka a inda Aminu yake zama idan ya zo wurin marainiya. Da zuwansa sai ya zauna a kan alluran nan, kuma gaba ɗaya alluran suka shiga jikinsa.

Nan da nan ya fara jin zazzaɓi, ya tashi ya tafi gida. Ciwonɗan sarki dai ya gagara warkewa, babu irin maganin da ba a yi ba. Wata rana marainiya ta tafi ɗiban ruwa a rafi, sai ta ji aljanu suna maganar ɗan sarki ba shi da lafiya, amma da an samo kashin tsutsotsi masu cin mutane a bayan wani gari mai nisa, aka jiƙa masa ya sha to zai warke.

Da marainiya ta ji sai ta yi maza ta ɗauki goranta, ta je gida, ta aske kanta ta shafe jikinta da baƙin tukunya, ta sa kayan maza, ta ɗauki kwano, kamar almajiri zai je bara. Ta kama hanyar wancan gari mai nisa, inda za ta samo kashin tsutsa mai cin mutum, har sai da ta yi tafiyar shekara biyu kafin ta isa wurin tsutsotsin.

Sai ta je wurinsu a hankali, ta kwanta don in sun ji motsin tafiyarta za su cinye ta. A hankali ta yi ta lulubawa dai -dai. Bayan ta sami abin da ta je nema, sai ta kama hanyar garinsu, ta isa lafiya. Bayan ta ɗan huta, sai ta kama hanyar gidan Sarki, ta tarar
mutane maƙil sun cika fada suna jiran mutuwar Aminu.

Da zuwa fada sai ta fara bara, mutane sun ɗauka namiji ne, suka ce: “Kai kana ganin ɗan sarki babu lafiya amma sai ka zo ka yi mana bara don ba ka da kunya?” Sai ta ce: “Ku bar ni in duba shi ko zai warke. Akwai wani magani da nake tafe da shi.” Sai suka daka wa ɗan almajiri tsawa, suka ce: “Duk duniyar nan babu wanda zai warkar da shi sai kai?”

Sai ta ce: “Abar ni mana in ɗan gwada.” Da ƙyar aka bar shi ya shiga. Da shiga sai ta ciro wannan kashin tsutsa, ta jiƙa, ta ba ɗan sarki, ya sha. Cikin ikon Allah nan take sai ya fara amai, duk ya amayar da ciwon da ke damunsa, ya warke sarai. Kowa yana mamakin ɗan almajiri. A cikin farin ciki Sarki ya ce: “Zan ba ka gida da dawakai da dukiya mai yawa.” Shi ma Sarki bai san da mace yake magana ba.

Sai ta ce: “A a ba na son wannan.” Sai Sarki ya ce: “To me kake so?” Ba tare da ɓata lokaci ba, marainiyar da ake zato namiji ce tace: “Ni dai babu abin da nake so kamar zoben hannunsa.”Ɗan sarki Aminu bai taɓa zaton zai rabu da wannan zobe ba, amma sai ya cire ya ba ta.

Ta karɓa ta tafi. Bayan kwana biyu sai ya je gidan su marainiya a cikin fushi, yace da ita: “A duk garin nan babu wanda bai san da rashin lafiyata ba, amma ke ba ki taɓa zuwa gani na ba.” A cikin tattausar murya ta kalle shi ta ce: “Zauna ka ji labari.” Ya zauna ta fara gaya masa yadda ta yi.

Da ta gama sai ya ce: “Ƙarya ne, idan maganarki gaskiya ce, to me aka bai wa ɗan almajirin?” Ya ce: “Zobe.” Sai ta ce: “To idan ke ce, nuna min zoben. Ya duba zobe, ya tabbatar zobensa ne. Daga nan ya fara mamaki. Ya ɗauke ta suka je gaban babansa, suka gaya masa labarin kome.

Ya sa aka ɗaura musu aure, aka yi gagaruimin biki, kuma aka basu kyautar gari guda da dukiya mai tarin yawa, suka ci gaba da cin duniyarsu da tsinke. Kurunkus.

> Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Rabon kwaɗo ba ya hawa sama
  • Mai nema yana tare da samu
  • Mai rabon ganin baɗi ko ana ha-maza ha-mata sai ya gani.
  • Hassada ga mai rabo taki ce.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar ‎Gizo Da Giwa

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMaƙala Mai Taken Kasuwanci A Duniyar Intanet: Ƙalubalen Hausawan Ƙarni na 21
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.