Ga ta nan ga ta nan ku.
Wata barewa ce, sai ta rikiɗa, ta zama mace kyakkyawa. Sai ta ɗauki ɗan kwatashinta ta ɗora a ka ta tafi tsakiyar karofi ta ajiye. Da ta ajiye, sai ta ce duk wanda ya jefa ’yar tsakuwa ta buɗe kwatashin nan, shi ne mijinta.
Sai wannan ya ɗauki tsakuwa ya jefa bai buɗe ba, wancan ya jefa tsakuwa bai buɗe ba. Sai aka sami wani ya jefa ’yar tsakuwa, sai ya buɗe. Sai ta ce ta sami miji, shi za ta aura. Sai suka tafi garin ita yarinyar, wurin iyayenta za a ɗauro mata aure da wannan mutumin.
Sai aka ɗaura musu aure ta zo ta tare gidan mijin. Kullum ranar girkinta sai a ce ta je ta ciro kuɓewa a gonar mijin ta yi miya. Da ta je gonar, sai ta yar da zanenta ta yi birgima a ƙasa ta zama barewa ta yi kiran ’yanuwanta, ta yi waƙa ta ce:
Cinkalkal, cinkalkal kalaya,
Turmin ’yan kale ya yi fure, ceɗiya.
Tudu na korar Tudu, Marina.
Tudu na korar tudu da ƙaho.
Ban da kwatsa-kwatsan.
Ban da ƙanƙan.
Sai ’yan uwanta su zo su taru su ciccinye kuɓewa. Sa’an nan in sun gama sai su tafi gida. Ita kuma sai ta yi birgima ta komo mutum ta ɗauki zanenta ta ɗaura. Sai ta koma gida ta dinga cewa, ‘Ni da gangan aka tura ni. Ga shi nan ban samo kome ba.’
To, ran nan sai mijinta ya bi ta gonar. Sai ya gan ta tana birgima. Da ta gama birgimar, sai ya ga ta rikiɗe ta zama barewa. Sai ya ga ta yi kiran ‘yan’ uwanta bareyi da waƙa. Bareyi suka taru a gonar jingim. Duk suka cinye kuɓewa.
Suna cikin ci sai ya fasa su. Sai ya ga matarsa, ta gan shi. Ya komo gida. Sai ta ɗauko kuɓewar ta biyo shi. Ta tarad da shi a gida. Ya ce, ‘Wace ce?’ Ta ce, ‘Ni ce.’ Ya ce, ‘Ina za ki?’ Ta ce, ‘Ɗaki za ni.’ Ya ce, ‘A a, koma daji.’ Sai ta ce ta ƙi. Sai ya biyo ta a guje ya kora ta daji.
Daga nan ba ta sake dawowa ba. Shi ke nan. Kurunkus.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin tatsuniyoyi da wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Gizo Da Namun Daji
Edita@rumasau-kallamu







