Taron Makon Hausa FCE Bichi 23 Oktoba 2025

0
29

A ranar Alhamis 23 ga watan Oktoba 2025, Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Bichi (FCE Bichi) ta gabatar da taron makon Hausa karo na biyu don tunawa da shahararren mai karanta littattafai a radiyo, marigayi Ahmad Isah Koko. Taron ya gudana ne a babban ɗakin taro da ke Kwalejin.

Taron ya samu halartar manyan marubuta ƙagaggun labarai irin su Ɗan Azumi Baba Ceɗiyar ‘yan gurasa, Nasir NID, Abdul’aziz Sani Madakin Gini, da sauransu. Haka kuma manyan malaman da masu gabatar da shirye-shirye a gidajen radiyo daban-daban sun samu halarta.

Bayan gabatar da taƙaitaccen tarihin rayuwar marigayi Ahmad Isah Koko da na shirinsa na Rai Dangin Goro, an gudanar da shirye-shirye na al’adun Hausawa sannan wasu daga cikin marubuta sun yi sharhi a kan wasu daga cikin rubuce-rubucensu.

Farfesa Isa Mukhtar daga jami’ar Bayero Kano, Ya gabatar da maƙala mai taken Gudunmawar Ƙagaggun Labarai Wajen Koyar da Tarbiyyar Al’umma.

A ƙarshe an ba da ƙyaututtukan girmamawa ga iyalan marigayi Ahmad Isah da kuma sauran mashahuran mutane.

RMK

 

labarin da ya wuceBaɗi Ba Rai Kashi Na Biyu
Labarin na GabaFassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya Daga Masallaci Mai Alfarma 31st Octoba 2025