An haifi Salmanu Faris A. Shu`aibu a garin Kudan a ƙofar Arewa Gidan Malam Tanko, a Ƙaramar hukumar Kudan wacce take jihar kaduna, sunan mahaifinsa shi ne Alhaji Adamu Shu`aibu Kudan ya rasu a ranar talata 05/08/2008 dai-dai da 1439 bayan hijra da misalin ƙarfe 05:30 na yamma.
Haka kuma sunan mahaifiyarsa ita ce Fatima Mahmud Kudan ‘ya ce ga Maryam sarki Yakubu (wacce aka fi sani da ɗango), sannan kuma su goma sha ɗaya ne a cikin ɗakin su, akwai yayyan sa guda huɗu su ne Rahinatu da Murtala da Umar da Bilkisu, sai kuma ƙannan sa guda shida su ne Saratu da Hamisu da Hajara da Mahmud da Zahariyya da kuma Zulaihat, sai kuma waɗanda suka haɗa mahaifi ɗaya daga cikin su akwai Talatuwa da Labaran da Isah da kuma Lawan.
Karatunsa Da Rayuwarsa
Ya fara karatun allo a hannun Alaramma Malam marigayi Aliyu Labaran Kudan (Damo sarkin haƙuri) a shekara ta 1998 har zuwa Shekara ta 2008, a inda ya samu damar sauke Alƙur’ani mai girma na farko, sannan kuma ya cigaba da sauka ta biyu, ya yi karatun littattafai na addini a hannun malamai da dama kamar su Marigayi Alaramma Malam Surajo Yunusa Kudan da Malam Shitu Bashir Kudan da marigayi Malam Adamu Azare Panshekara da Alaramma Malam Misbahu Tsaure Panshekara da Malam Nura Yahaya Panshekara da kuma Sheikh Umar Sani Fagge Kano.
Sannan kuma ya fara karatun zamani (boko) ne a makarantar Model Primary School Kudan a Shekara ta 2001-2007, sai ya wuce makarantar gaba da Firamare ƙarama ta garin Kudan wato J.S.S Kudan a Shekara ta 2007-2010, sai ya tsallaka zuwa Unity School ƙaraye, amma kuma ya kamala karatun sa ne G.S.S ƙayi Panshekara a Shekara ta 2013.
Sai ya wuce makarantar koyar da Ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computer), wato Troubleshooting and Information Technology (T.I.T) Kano, a inda ya samu damar karanta Data and Information Technology (Professional Diploma) da News Reporting and Photographic (Professional Diploma) da Networking and Maintenance (Higher Professional Diploma) da Web Designing (Higher Professional Diploma).
Sai kuma ya tsallaka zuwa jami’ar Bayero, a inda ya samu shaidar shiga (Admission) a Shekara ta 2015 wanda ya karanci Ilimin nazarin halittu {Bsc (Ed) Biology}. Bugu da ƙari kuma, ya yi karatu a ɓangaran kiwon dabbobi (Poultry farming) a makarantar Directorate Youth Development & Economic Empowerment Kano state 2016.
A lokacin da yake ƙarami har zuwa tasowarsa ya ɗan yi sana’o’i daban-daban kamar su tallan attarugu da albasa da ƙosai da Tibani da Youghout a ranakun da babu makaranta ko kafin ya tafi makaranta ko kuma bayan an taso daga wata makaranta, domin samun abun sawa a baka.
Haka kuma, a lokacin da yake J.S.S yana zuwa daji ,domin yin ƙwadugo ko kwandilo (bushashshan kashin shanu) ko Tushiya (bushashshiyar tushen dawa) ko ciyawa a lokacin da babu karatu, domin biyan kuɗin makaranta da samun abin sa wa a baka wai ya fi a rataya, saboda a lokacin mahaifinsa ya rasu.
Har ila yau, a lokacin da yake S.S.S Two (2) Yana zuwa aikin kwana masana’anta, sannan kuma da safe sai ya wuce makarantar boko da yamma kuma sai ya ɗan yi karatun allo da na Fiƙihu kafin dare ya yi, sai ya tafi wajen aikin sa, ga kaɗan daga cikin guraren da ya yi aiki kamar haka;
1. Ya yi aikin matsen man gyaɗa a kamfanin matsan gyaɗa na Alhaji Gambo wanda yake Zuwaciki (2010-2013).
2. Ya yi aiki a kamfanin samar da lemu na kwalba (coka-cola 2013-2014).
3. Ya yi aiki a Wreca Staff School Challawa (2015- 2019).
3.Ya yi aiki a Vital Academy bayan janare a Zuwaciki (2019- 2021).
4. Ya yi aiki a Madrasatun Nuruddin Islamiyya wa tahfizul ƙur’an Panshekara a matsayin mataimakin shugaban makaranta (2015-2019).
5. Ya yi aiki a Madrasatun Imamu Malik Bin Anas Islamiyya Panshekara a matsayin ma`ajin kuɗi (Treasure 2015-2017).
6. Ya yi aiki a Madrasatun Darussunnah Firamare School Islamiyya Panshekara a matsayin shugaban musabaƙa (2014-2015).
7. Ya yi aiki a Madrasatul Irshadul Aulad Islamiyya Panshekara (2013-2024).
8. Ya yi aikin ƙwarewa(IT) na gidan rediyon Kano (Kano Radio 89.3 FM) na tsawon watanni uku.
9. Ya yi aikin sakai (Voluntary) a Express Rado 90.3 FM Kano daga 2019-2022.
10.Ya samar da ƙungiyar marubutar Arewa ta ƙasa Nijeriya (AWAN) a 2019.
11. Ya zama shugaban ƙungiyar marubutan Arewa, wato “AREWA WRITERS ASSOCIATION of NIGERIA(AWAN)” na ƙasa daga 2019-Yau.
13. Ya yi aiki da makarantar Cradle to Career Academy (C2C) Zuwaciki, Kano daga 2021-yau.
14. Ya zama mataimakin shugaban tashar “Use Your talent Tv” daga 2022 – yau.
Ya yi waɗancan karatu na na’ura mai Ƙwaƙwalwa (Computer) ya kuma shiga jami’ar Bayero Kano da ‘yan sana’o’isa na hannu.
Fara Rubutunsa
Ya fara rubutu ne a Shekara 1435 bayan hijira dai-dai da 2013, a lokacin yana karatu a Unity School Ƙaraye, bisa dalilin ganin irin matsalolin mace-macen aure da ya gani haɗi da gori da waɗansu mutane musulmi suke yi wa waɗanda suka musulunta ko kuma suke aikata wani abu mara kyau, sai kuma daga baya suka tuba suka koma ga Allah (Subhanahu Wata’ala). Sai ya rubuta wani littafi mai suna “KAMBUN MA’AURATA” da kuma “NASIHA GA MUSULMI AKAN SON ZUCIYA”. Daga cikin littattafan da ya rubuta su ne kamar haka:-
1.Kambun Ma’aurata 1&5.
2.Nasiha ga musulmi akan son Zuciya 1&4.
3. Ramadan Mubarak.
4. Khulasatu Siratun Nabiyyi.
5.Ɗarikul Hudah.
6. Ina Ma’aurata.
7. Babban Kundi (Alƙur’ani mai girma).
8. Righteous path to Islamic education 1.
9. Salmanu da Salma.
10.Kambun masoya.
11.Mace ikon Allah.
12.Kyauta ko Rance.
13.Abincinka maganinka.
14.Miskilar mace.
15.Yar islamiyya
16.Gwarazan Kudan (ya koma tsani).
17. Tarkon ƙauna.
18.Hausa ba dabo ba 1&2.
19.Muguwar ƙaya 1.
20.Shugabanci ko mulki ?
21. Na duƙe tsohon ciniki (Agriculture).
22. Mata hasken rayuwa.
23. Duniyarka A Hannunka (Computer)
Da Dai sauran su.
Muƙalolin sa
1.Influence of student’s learning difficulties in Biology on Academic achievement in Gwale local government area of Kano state (Bsc{Ed} Project 2019).
2. Aure tushen arziki.
3. Alƙu’ani jigon rayuwa.
4. Sanadiyar soyayya.
5. Matsalolin mutuwar aure.
6. Alamomin shigar so.
7. Magani a gonar yaro.
8. Falalar da Allah ya yi wa mace.
9. Amfanin shayar da jariri nono zalla.
10. Dokin tsira.
11. Wacece mace.
12. Hukuncin jinin haila.
13. Illar rubutu/karantun batsa ga marubuta da makaranta; Takardar da aka gabatar da ita a majalisar marubuta ta jahar Yobe 07/01/2021.
14. Rayuwar Manzon Allah (S.W.A) ita ce abin koyi: Takardar da aka gabatar da ita Madrasatul Darul Haƙ Islamiyya Zawaciki Panshekara, ƙaramar hukumar Kumbotso, jihar Kano.
15. Wacece mace ta gari.
16. Hikimar yin zance (soyayya).
17. Lokutan da soyayya ta fi daɗi.
18. Illolin yin tsafi ga al’umma.
19. Amfanin taimako.
Lambar Yabo
Ya samu lambobin girmamawa daga wurare daban- daban kamar su;
1.Kainuwa Authors Kano, wanda suka koma Kainuwa Authors Forum a yanzu 2020 (2019).
2.Darussunnah Firamare Islamiyya School Panshekara (2016).
3.Irshadul Aulad Islamiyya Panshekara (2016).
4.Nuruddin Litahfizul ƙur’an Islamiyya Panshekara (2015).
5.Imamu Malik bin Anas Islamiyya Panshekara (2015).
6.Wreca Staff School Challawa Panshekara (2016).
7.Nigeria Universities Education Students Association (NUESA) Bayero University, Kano Chapter (2019).
8.Yobe Writers Association (YOWA) a (2020).
9. Majalisar Marubuta 2021 (akan illar rubutu da karantun batsa).
10. Arewa Writers Association of Nigeria (AWAN).
11. Cradle to Career Academy (C2C) Zawaciki, Kano (The most active extra-curricular activities and the effective student learning support teacher).
12. Hadiza Ibrahim Aliyu School of Festival (HIASFEST) a matsayin wanda ya lashe gasar kimiyyar halittu (Biology) zuwa ga harshen Hausa (Hausa science book/biology) na shekara ta 2023.
14. Hadiza Ibrahim Aliyu School of Festival (HIASFEST) a matsayin wanda ya zo na biyu a gasar kimiyyar kwamfuta (Computer) zuwa ga harshen Hausa (Hausa science book/computer) na shekara ta 2024.
Danna nan don karanta tarihin Dakta Ado Zakari Kudan
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
[…] Domin karanta tarihin Salmanu Faris Adam danna nan […]