Tarihin Ranar Damokuraɗiyya A Najeriya

1
65

Alhamdulillah yau ranar damokuraɗiyya, tun lokacin da Mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ayyana cewa duk ranar 12 ga Yuni ita ce ranar damokuraɗiyya a Najeriya, domin girmama gwagwarmayar da masu rajin tabbatar da tsarin damokuraɗiyya suka yi, na kawo wannan tsari har zuwa yanzu. Yana da kyau  a yi waiwaye kuma a duba menene ita kanta damokuraɗiyyar da kuma , me yasa muke cikin matsayin da muke ciki a Najeriya. Saboda maganar tattalin arziƙi da wasu abubuwa da suka shafi rayuwarmu. Da kuma ƙalubalen da muke ciki, har ya sa wasu suke ganin ai damokuraɗiyyar ba ma cin gajiyarta. 

Za mu yi waiwaye a kan wannan mu duba mu wane yanayi ne ya fi dacewa da mu, sannan mu bibiyi ƙalubalen da fahimta ta wasu mutane irin su tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da yake cewa ai mutanen Afirka sun ƙirƙiro tasu damokuraɗiyyar. Duk wannan suna cikin abin da yake ƙalubale a kanmu, kuma a matsayin mu na masu bibiyar al’amura, ya kamata mu yi nazari a kan wannan.

Na farko, kamar yadda muka sani damokuraɗiyya mutane daban-daban suna da fahimta iri-iri a kanta. Ba wai a nan ƙasar tamu ba har a faɗin duniya baki ɗaya. Ana da fahimta daban-daban da ta shafi damokuraɗiyya hatta a ƙasashen yamma da suke ganin su ne asalinta, kuma ita ce aƙidarsu. Haka kuma ƙasashen mu na Afirka da ƙasashen Musulmi, wasu na ganin damokuraɗiyya kafirci ce ba musulunci ba ne. Da dai maganganu daban-daban. Wannan abu ne mai zurfi, kuma mai faɗi amma za mu taƙaita a kan misalai ƙalilan; domin samun haske a kan ma’anar damokuraɗiyya.

MA’ANAR DAMOKURAƊIYYA

Ita dai damokuraɗiyya ana ganin cewa gwamnati ce wadda mutane suka zaɓe ta. Wannan ita ce fasasara mai sauƙi, amma wasu suna ƙalubalantar wannan. Damokuraɗiyya wani tsari ne da zai kawo gwamnati mai inganci, kuma wanda mutane suke da damar faɗin albarkacin bakinsu, domin nuna sakamakon abin da aka yi musu, su fitar da ra’ayinsu, kuma su yanke hukunci ba tare da an tilasta musu ba. 

Mutane za su yi zaɓe, su yi abin a cikin lumana, kuma kowacce ƙasa da irin nau’in gwamnatin da ta ɗauka na tafiyar da gwamnati mai adalci ko da ba a yi zaɓe ba. Bisa haka ne ma mutane irin su Muhammad Gaddafi yake ganin shi damokuraɗiyya yake yi saboda ya ba wa al’ummarsa duk irin abinda suke bukata, shi ma damokuraɗiyya ce. Kamar ƙasar Rasha da suke yi abubuwansu mai inganci, su ma suna ganin damokuraɗiyya ce. Ita damokuraɗiyya ta banbanta da yanayin da mutane suka ɗauki kansu. 

Misali kamar mutanen China, suna ganin ƙasarsu ma tana bin damokuraɗiyya duk da cewa ba zaɓe suke yi ba da za a ce duk gari mutum ɗaya a zaɓe shi, a a sai dai ‘yan jami’yya ne  kawai suke yin zaɓe tare da bin ƙa’idoji na tabbatar da tsarin gwamnati, saboda China sun fi shekara dubu uku(3000) sun yi gwamnati mai inganci, wadda kafin a ɗauke ka aiki, sai ka nuna ƙwarewa (meritocracy), sun daɗe suna irin waɗannan abubuwan tarihi da ya ba su damarsu fito da tsarin da zai amfane su. 

Saboda haka a ko’ina za ka ga mutane suna da irin nasu tsarin na damokuraɗiyya ta yadda za su aiwatar da ita. Tun da haka kenan za a ce irin damokuraɗiyyarsu ba za ta zama irin ta ƙasashen turawa ba. A zaɓi shugaban ƙasa, da gwamna da ‘yan majalisa. In dai aka samu gwamnati mai inganci, mai adalci, mai kulawa da haƙƙin jama’a, shi kenan su wasu suna ganin cewa wannan damokuraɗiyya ce.

Saboda haka, amana ce idan aka ɗauketa aka auna ta za a ga cewa wasu mutane ne suke damfarar jama’a su juya akalar gwamnati, duk da kana zaɓe amma ba ka da tasiri sai wasu mutane ƙayyadaddu da suke da kuɗi da ɗaurin gindi na wasu ƙungiyoyi, kamar yadda yake yanzu a Amurka take fuskantar barazanar yahudawa (Zionists) sun karɓe ƙasar sai yadda suke so, saboda suna da yadda za su yi, ba ka da damar cewa komai saboda suna da kuɗi da jaridu da abubuwa da za su iya hanaka samun wannan zaɓe, tun da ba kowa zai tsaya a zaɓe shi ya ci ba, sai ace damokuraɗiyya ce.

Kuma akwai yawancin mutane da suke ganin cewa damokuraɗiyyar nan turawa ne suka ƙirƙireta kuma ya saɓa da tsarin musulunci. To amma shi fa tsarin musulunci nan ya danganta da wanda yake magana, misali, musulmin ƙasar India kimanin mutum miliyan ɗari biyu (200 miliyan) fiye da yawan musulmin ƙasashen Afirka, babu inda ya fi su yawan musulmi a duniya sai ƙasar Indonesia. 

  Shi wannan musulmin sai ya ce maka shi ya fi son tsarin damokuraɗiyya, saboda idan ba tsarin damokuraɗiyya ba, babu yadda zai iya gudanar da addininsa na musulunci. Saboda haka a ba wa kowa ‘yancin ya gudanar da addininsa yadda yake so shi musulmin India yake buƙata.  

Amma kuma idan ka je ƙasar da musulmi ke da rinjaye, za su  ce mu a bar mu mu yi tsarin musulunci mu ɗabbaka shari’a, domin shi ne  zai yi mana dai-dai da yadda muke so. Don haka,  a nan an samu bambanci da damokuraɗiyya da yadda za a yi aiki da ita.

Damokuraɗiyya kamar riga ce ko mota da za ka yi amfani da ita, ba lallai sai an bi tsarin yadda turawa suka kawo ba. Su turawan sun kawo wannan tsarin (liberal democracy) ne da a zo a yi zaɓe kuma duka abin da mutane suke so shi za ayi, kenan babu haƙƙin Allah. Tun da farko Kent ne ya zo da tsarin wayar da kai a kan babu Allah (enlightment) da suka ce kada mutum ya yarda da abin da ba ya ganinsa. 

Tun daga nan turawa suka daina tunanin Allah cikin al’amuransu saboda waccan aƙidar ta (Enlightment philosophy). Allah da suke bauta masa shin “son zuciyarsu”, duk abin da zai tabbatar musu  da wannan son zuciyar da jin daɗi. Shi kuwa musulmi ai ba za su yarda da wannan ba. 

 Idan ka ba da zaɓi za a yi wannan, a misali ƙasar Misra, idan  ka zo ka ce za a yi damokuraɗiyya a yi zaɓe, mutanen Ikhwan su ne za su ci zaɓen, saboda haka turawa ba za su yarda a yi damokuraɗiyya a Egypt ba. Sun fi son a dinga mulki irin na soja ko sarakuna (mulukiyya) , wanda da wannan za su yi amfani su juya mutane yadda suke so. 

Amma idan aka ce za ayi damokuraɗiyya to, tsari irin na Ikhwan ne zai tabbata. Musulmi da ‘yan ideology sun fito sun ce wai ‘yan Ikhwan ba mutanen kirki ba ne, saboda haka a nan za ka zaɓi Musulmi ‘yan Ikhwan ne ko maƙiya addinin Allah irin su Sise. Sai ka ga shugabannin larabawa suna goyon bayan Sise sun ƙi su goyi bayan Ikhwan, waɗanda za su tabbatar da adalci, su ba da dama a yi addinin gaskiya. Amma sai su goyi bayan Zionists don biyewa son zuciya, kawai.

 

Ita damokuraɗiyya ba ya danganta da yadda ka ɗauketa, wanne tsari ka shigo da shi don ka tabbatar. Shi yasa ƙasar China da suka fi kowaɗanne mutane yawa, sun tafiyar da damokuraɗiyyarsu a kan tsari na tafiya da gwamnati mai kyau, kuma za a dauki mutane waɗanda suke da inganci su yi aiki. 

Yanzu shi shugaban ƙasar China sai da ya yi shekara 30 yana aiki, tun daga kan matsayin Kansila ya fara, sai sun tabbatar da kai kwararre ne kafin ya zo kan shugaban ƙasa. To ka ga China da suka zo da ‘yan gurguzu (communist) ɗinsu dole ne ka ba su wannan matsayi na damokuraɗiyya, idan aka zo za a yi aiki ko na makaranta ne ko asibiti ko kwashe shara, sai sun fito da abubuwa an tambayi mutane domin a ji ra’ayinsu tare da bin diddigi a kan aiki. 

Shi yasa masana ilimin kimiyyar siyasa suke cewa, ba za a ce China ba ta bin tsarin damokuraɗiyya ba, domin kowanne aikin gwamnati sai an tabbatar da ingancinsa, kuma sai an tambayi ra’ayin jama’a amma ba haka ba ne a ƙasar Amurka, ba ruwansu da wannan, kawai idan an yi zaɓe bayan shekara hudu an kori wannan an kawo wannan haka dai. To amma su China a tsarin damokuraɗiyyarsu da manufarsu shi ne ta yaya tattalin arziƙinsu zai juya ƙasar. Shi ya sa daga 1978 zuwa yanzu mutum sama da miliyan 500 sun fitar da su daga talauci. 

 Wane abu ne za su fito da shi da za su taimakawa mutane. Shi ya sa su a wurinsu duk wanda ya ce tsarinta ba ingantacce ba ne ya yaudari kansa. Domin sun ɗora sha’anin al’adunsu da tarihinsu. 

Da wannan za mu fahimci cewa ita damokuraɗiyya nan da ake magana ba tsarin da za a ce don kana da gwamnati da aka yi zaɓe wai ka yi damokuraɗiyya, haka ne  ka yi demokuraɗiyya, amma akwai abubuwa da yawa da suka shafi wannan. Kamar irin abin  da yake faruwa a India, ga shi nan Indian tun 1940 suka samu ‘yancin kai ba a taɓa gwamnatin soja ba, amma yanzu india ta lalace, saboda ‘yan Hindu masu aƙidar bambancin addini, waɗanda su ne mafi yawa suke tsangwamar musulmi saboda ƙiyayya. 

Idan zaɓe ne , to an yi zaɓe a India, kuma abin da suke so masu rinjaye (majority) su kashe mara rinjaye (minority). Wannan bai shigo cikin tsarin damokuraɗiyya ba, domin yadda aka ce, amma ana amfani da dangwalen masu rinjaye domin a cutar da marasa rinjaye (musulmi). Ya nuna cewa India duk maganar da suka yin a damokuraɗiyya ba haka ba ne. 

Bisa wannan, idan za ka yi maganar damokuraɗiyya, sai ka yi bibiya, menene ya shafi rayuwar al’umma, an samu ci gaba ko ba a samu ci gaba ba?

DAMAKURAƊIYYA A NAGERIYA

Lokacin da turawa suka zo sun tarar da mutane, suna da tsarin rayuwarsu da tsarin gudanar da mulkinsu a wuraren da ake da shi, sun samu Daular Usmaniyya (Shehu Ɗan Fodio) duk suna da tsarin rayuwarsu da ƙabilu ma da ba su da tsarin shugabanci, amma suna da irin tsarinsu, na zaman lafiya da na rashin zaman lafiya da na tattalin arziƙi da zamantakewa.

Daular Usmaniyya ta ƙasar Sokoto ta haɗa gaba ɗaya ƙasar Hausa da Nupe da Ilori da can ɓangaren Adamawa da wasu a Kamaru da Benin da Nijar da Burkina Faso. Ƙasa ce amma da sarakuna a kowanne garuruwa. Bayan jihadi aka kafa Daula mai ƙarfin tattalin arziƙi a nahiyar Afirka ta baƙar fata a ƙarni na goma sha tara (Q-19).

Turawa da suka zo sai suka haɗe mu da yankunan Arewa da Kudu, a shekara ta 1914, domin samun dunƙulalliyar Najeriya. Bayan kowanne yanki da irin al’adunsa da addininsa daban, ta yaya za a yi wannan zamantakewar? Wannan dai bature ya haɗa ne saboda ya yi cinikayya ya samu kuɗi saboda a wannan nahiya ta savannah har zuwa kurmi akwai arziƙi ta yadda zai dinga fitar da amfanin gona, ya gyara sannan ya dawo da shi don ya samu kuɗi, wato dai saboda ƙarfafa arziƙin turawa. 

Saboda haka suka haɗe waɗannan ɓangarori, don ya yi amfani da su wajen mulkinsa bisa samar da umarni ta ƙarƙashin sarakuna (indirect rule). Da bature ya zo zai tafi bayan shekara 60, babu wani abu da ya sani sai tsarin mulkinsa irin na nasara, wanda suka ɗora kansu a kai tun bayan da suka yi Industrial revolution a ƙasashen yammacin turai, da ƙasasahen da suka kafa.

Wannan ya dogara da irin tsarinsu da zamantakewarsu da suka zo da su. A nan sai suka lura da cewa tun da kuɗi suka zo nema, sai su yi amfani da irin tsarin mulkinsu amma su hana waɗannan sarakuna wani iko, sai abin da suka ga dama za su yi da su, cewa haraji idan za ka biya sai da kuɗin nasara. Shi kuma kuɗin nasara ba a samunsa sai an yi aikin leburanci , ko a yi noma irin nau’in abin da za su saya. Wannan ya jefa ƙashin bayan tattali arziƙinmu cikin talauci, kuma har yanzu ana cikin wannan yanayin talauci. 

Saboda haka aka kawo ilimin Boko wanda idan babu shi babu wani abin da za ka yi. Ya zama dole ta sa, sarakuna da mutanensu suka shiga wannan karatu, daga bisani suka ce sai an kafa jam’iyyu da tsarin siyasa. Aka yi jam’iyyu a Arewa da jam’iyyu a Kudu. Wannan shi ne ya samar da jamhuriyya ta farko kowanne larduna yana da nasa tsarin da yadda za a tafiyar da su.

Akwai babbar matsala a wannan lokaci na wasu rukunin ƙabilu da aka rufe su ba a ma jin labarinsu, misali kamar a jihar yamma an samu matsala da tashe-tashen hankali, sai jihar Arewa suka haɗa baki da jihar Gabas suka rinjayi ‘yan majalisa na jihar Yamma domin samar da  jihar  Yamma ta Tsakiya (Mid west). 

Abubuwa suka yi ta faruwa ana ta rikici wanda da ma tsarin ƙarfin iko daga majalisa (parliament), inda shugaban gwamnati za a zaɓo shi daga mazaɓarsa ba duk ƙasa ce take zaɓarsa ba, kuma jami’yya ce take gaba da shi, da jam’iyya za a yi amfani da jam’iyya za a yi mulki da jam’iyya ake haɗa kai da wasu aka yi wannan wake- da- shinkafar aka yi zaɓe, zaɓenma an samu maguɗi da kashe-kashe da rigingimu, har manyan kudu( waɗanda sun san abin da suke yi) suka yi ta ba da matsala a majalisa (parliament)

Sir Abubakar Tafawa Balewa ya yi fama da ita wajen neman haɗin kan mutane. Har Antony Enahoro yake cewa; idan babu wannan mutumin ƙasar nan ba za ta zauna lafiya ba, haka Tafawa Balewa ya sha wahala. ‘Yan kudu da suka ga idan zaɓe za a yi ba za su iya kai labari ba. 

Sai sojoji suka zo suka kifar da wannan gwamnati, suka kashe Tafawa Balewa da Sardauna da Akintola da sauransu. Domin sun ce idan ba su da yawan mutane a majalisa, to su  bi ta hanyar maguɗi a  ƙidayar jama’a (Census) wanda aka yi a shekara ta 1963 har aka sake a 1964, suka ga maguɗinsu bai ci ba. Sun fahimci zaɓe, ƙato-bayan- ƙato da ƙuri’a bayan ƙuri’a, to ɗan kudu ba zai yi mulki ba. Sai suka ce maganin wannan shi ne su zuga sojoji su yi juyin mulki.

A wannan lokacin mafi yawan sojoji ‘yan ƙabilar igbo ne, amma ainihin jam’iyyar AG ta Awolowo ita ce ta saka su. Duk waɗannan abubuwan saboda rashin kyakkyawan nazari da ba mu da shi a ƙasar nan sai aka dinga cewa ai Inyamurai ne  suka shirya juyin mulki da wannan kisan gillar. Amma dai babbar manufar an yi shi ne don a hana mutanen Arewa mulkin Najeriya.

 Don haka akwai maganar ƙabilanci , akwai maganar bambancin addini, saboda  Sardauna mai riƙo da addininsa ne kuma yana son ƙabilarsa da addininsa su fi kowacce al’umma a Najeriya. Lallai akwai wannan amma ba shi kaɗai ba ne, abubuwa suna wuce haka. ‘Yan kudu abin da suke so a wannan lokaci shi ne, yadda zasu karɓi mulki, tun da ba su samu ta hanyar dangwale ba sai suka ƙaro rigima, inda suka kawo soja ya ƙwace mulki.

  Wannan yana da muhimmanci mu fahimce shi. Kuma Mr. SG Ikoku ya faɗa a wani taro (conference), ya ce sun yi magana da sojoji domin su fahimtar da su maganar siyasa. Shi ya ce ‘yan siyasa ne suka zuga soja aka yi juyin mulki a Najeriya.Tun bayan mutuwar Tafawa Balewa ƙasar nan ta kasa zama lafiya, kamar yadda Tony Enahoro ya faɗa cewa, idan babu Tafawa Balewa ƙasa ba za ta zauna lafiya ba.

 Haka kuwa aka yi da aka yi wannan, abin da ya biyo baya shi ne yaƙin Biafra aka zo aka kashe mutane, abubuwa da yawa  a ƙasa , aka shiga rigingimu. A daidai wannan lokaci sojojin Arewa suka hamɓarar da gwamnatin Ironsi, suka saka Gowon ya zama shugaban ƙasa. A dalilin haka da sauran abubuwa suka  ce za su yi ƙasar Biafra, wannan ya haifar da yaƙi domin tsare ƙasa daga masu ƙoƙarin ɓallewa. 

Shi Yakubu Gowon yana tare da mutanen Arewa aka zo  yin yaƙi na Ojukwu aka shafe kusan shekaru uku ana yaƙi (1967-1970).  Gowon ya yi shekaru tara yana mulki, a lokacin manyan ‘yan siyasa, suna nan  waɗanda ba a kashe su ba, irin su Awolowo da Azikwe da malam Aminu Kano da Shagari da sauransu. Su ma waɗannan ‘yan siyasar  suka yi ta ƙoƙarin a basu mulki.

 Gowon ya yi ta yaudararsu, yau ya ce wannan gobe ya ce ya canja. Saboda ya ga irin yadda aka yi a ƙasashen Afirka, sojoji suna ta yin mulki. Kuma babu maganar yin zaɓe. Saboda haka  daga cikin sojoji Kanal  Shehu Musa ‘Yar Adua ya jagorance su , suka yi juyin mulki  suka kawo Janar Murtala Muhammad wanda dama shi ne shugabansu tun bayan da aka yi yaƙin Basasa.

 Wanda yake tsayyaye ne a kan batun rashin cin hanci da rashawa. Nan da nan suka ce za su mayar da mulki a hannun farar hula domin ƙasa ta zama ɗaya. Za a yi mulki damokuraɗiyya, wanda za a kawo tsarin shugaba mai cikakkken iko ba irin na jamhuriyya ta farko ba wato parliamentary.

Yanzu Allah ya kawo zamani wanda mutane ba wani nazari suke yi ba da har suke kawo maganar wai a koma wancan tsari na ƙarfin iko daga majalisa (parliament). Saboda ba ma yin ƙoƙarin fuskantar abubuwa bisa nazari. 

Shin menene matsalar Najeriya? Ta ƙarfin iko daga majalisa (parliament) ne ko kuma ta shugaba mai cikakken iko (presidential), ko ta wani abun ce daban? Sai suke ganin cewa wai a koma baya. Wannan jamhuriyar fa ita ce ta wahalar da mutane da rarrabuwar kai, wadda ta haddasa yaƙin basasa. Ita ce suke son ta dawo kawai a nan ma suna ganin idan ba haka suka yi ba, ba za su samu mulki ba daga hannun ɗan Arewa. Shi kuma ɗan Arewa gani yake, idan babu mulki ba zai cigaba ba.  Wannan matsala ce da take fuskantar ‘yan Najeriya.

Da aka zo gwamnatin Murtala, suka kashe shi. Sannnan Obasanjo ya zo a matsayin shugaban ƙasa, gwamnatin ta yi ƙoƙari waje shirya zaɓe domin mayar da mulki a hannun farar hula, aka zaɓi Alhaji Shehu Shagari daga Jam’iyyar NPN.

Sun zo da tsarin shugaba mai cikakken iko saɓanin tsarin jamhuriya ta farko na ƙarfi daga majalisa (parliament), wanda ba duk ƙasa ce take zaɓen shugaban ƙasa ba. Shi kuwa wannan tsari na shugaba mai cikkaken iko, duk ƙasa ce take zaɓen shugaban ƙasa da mataimakinsa. Idan za a duba magana ta hankali, ya kamata a ce wanda zai jagoranci mutane gabaki ɗaya suka zaɓe shi da hannunsu da amincewarsu ya zama shugaban ƙasa, sauran jama’a suna da ta-cewa a kansa.

 Don haka wannan fa ya fi wancan. Wancan kawai, mazaɓar shugaba ce za ta zabo shi sannan ya zo zauren majalisa, su kuma ‘yan majalisa su zaɓe shi shugaban gwamnati. Domin jam’iyyar da ta fi kowacce karɓuwa a Najeriya baki ɗaya NPC ita ce ta ci zaɓe. Tana da mutane daban-daban daga kowanne sashe na ƙasa, ba wai kawai mutanen Arewa ba ne a cikinta, da mutanen kudu da mutanen tsakiyar Najeriya.

 Wannan ce ta sa jamiyyar ta samu karɓuwa ta kafa gwamnatin tarayya. A dalilin wannan ya sa, ana tafiya har wannan gwamnati ta lalace, ana ta rigima daga baya soja ya sake dawowa ya karɓe mulki ta hanyar juyin mulki a 1983. Matsalar da gwamnatin Shagari ta fuskanta shi ne na ‘yan jaridar kudu da suka saka shi a gaba. Wannan suka da jaridun kudu suka dinga yi wa gwamnatin har mutane suka karɓa suna ganin gwamnatin babu inganci ga cin hanci da rashawa a tsakanin ministoci da sauran laifuffuka, ‘yan kudu sun sa su a gaba, saboda su suke da bakin magana. Allah dai ya kawo qarshen gwamnatin, to ita ma ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba sojoji a tsakaninsu suka tumɓuke Muhammadu Buhari, sai Babangida ya hau.

Daga nan ne aka fara tunanin ranar damokuraɗiyyar nan, menene ya kawo 12 ga watan Yuni? Shi Janar Babangida ya kawo sauye-sauye da yawa a cikin harkar Najeriya, kuma duk da cewa soja ne shi amma yana da ra’ayin ba wa mutane dama su yi Magana da kuma ra’ayi tattalin arziƙi da cewa ba wai lallai sai gwamnati ce zata riƙe ba, wato abubuwa za su koma hannun ‘yan ƙasa da ‘yan kasuwa.

 Wannan ya sa ya bambanta da sauran sojoji, kuma ya ba wa mutane dama su yi magana. Ya gabatar da tsare-tsare na siyasa da suka haɗa da taron makomar siyasa da cibiyar tattauna batutuwan siyasa. Da farko ya ba wa mutane damar su yi jam’iyyu suka kasa, ya zo ya yi jam’iyya guda SDP wadda ta karkata ga hagu, masu ra’ayin ci gaba da sauri da NRC wadda ta karkata dama, mai ra’ayin cigaban ‘yan mazan jiya (jari hujja). 

Bayan da aka yi zaɓe na cikin gida a jam’iyyun sai aka ga duk ‘yan Arewa ne za su fito takara, domin Janar Shehu Musa Yar Adua shi ne ya ci a SDP sannan Malam Adamu Ciroma ya ci a NRC, wanda duk daga Arewa suka fito, aka ce wannan zaɓen fitar da gwanin yana da matsala domin an yi magudi , Babangida ya soke.

Bayan gwamnatin Babangida ta soke zaɓen, sai ta sake ba da dama a zo a sake. Bayan sun gudanar da zaɓe, sai SDP ta fitar Chif MKO Abiola, ita kuma NRC ta fito da Alh. Bashir Othman Tofa, abokin Babangida, ɗan Arewa kuma ɗan Kano ne. Aka yi ta rigima, zaɓen ba a kammala shi ba, amma mutanen Abiola suka ce shi ya ci.

 Gwamnatin Babangida ta soke zaɓen a ranar 12 ga watan Yuni 1993. Wannan ya sa a ka cigaba da rigima daga ƙarshe dai Babangida, ya ce ya tafi (ya zakuɗa) daga shugabanci Najeriya. Ya sauka ya ba wa wata gwamnatin riƙon ƙwarya ta Chif Earnest Shoniken. 

Sai gwagwarmayar sai an dawo damokuraɗiyya, sai an dawo da zaɓen da aka soke a Yuni tare da nuna cewa Abiola ne ya ci zaɓe aka hana shi saboda ba ɗan Arewa ba ne. Wannan rana aka mayar da ita kamar ranar sallah. Bayan da aka ba wa Shoniken shi kuma ya kasa, saboda tsangwamar mutane NADECO, sai Janar Sani Abacha ya karɓe mulkin ya shekara biyar, ya yi abin da zai yi, har Allah ya karɓi ransa yana shugaban ƙasa a 1998.

Daga nan sai Janar Abubakar Abdussalam, ya karɓa, ana tunanin yadda za a saki Abiola bayan an tsare shi saboda ya ayyana kansa shugaban ƙasa. 

Abdussalam ya sako shi. Ya yi ta ƙoƙari ganin an rantsar da shi ta hanyoyi daban-dabani, ya  haɗu da mutane  a wata tattaunawa da wani jami’in gwamnatin ƙasar Amurka (mataimakin minister) da wata jakadiyar majalisar ɗinkin duniya da wasu ‘yan fadarsa, Ya sha shayi a gabansu, Allah ya yi ikonsa rai ya yi halinsa. Daga nan wutar rigima ta cigaba, inda suke cewa dole mulki sai ya koma kudu. Abdussalam ya ga cewa abin da zai yi shi ne, ya miƙa mulki a hannun farar hula, inda ya shirya yin zaɓe tare gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa. 

Ya tuntuɓi manyan ƙasa irinsu Babangida, suka shawarta cewa, idan za a ba da mulki, sai a ƙyale mutane su yi jam’iyyu, kuma lallai a saka ‘yan kudu guda biyu su fito takara. Don haka tun da Shehu Musa ya mutu yana gidan kurkuku tun lokacin da Abacha ya tsare shi, sannan Abiola shi kuma yana raye, sai a fito da shi a ba shi tikitin takara a jam’iyyar PDP. 

Sannan jam’iyyar APP da kuma AD wanda yarabawa ne mafi yawancinsu aka ce su haɗe wuri ɗaya, su fito da ɗan takara guda ɗaya, suka fito da Chif Olu Falaye. Aka yi zaɓe domin a ba wa ‘yan kudu damar shugabanci, ‘yan arewa suka marawa jam’iyyar PDP ta Olusegun Obasanjo baya ya zama shugaban qasa a shekara ta 1999. 

Obasanjo ya yi mulkinsa amma kullum tunanin June 12 suke yi, a yi ta nanatawa, duk shekara sai sun yi taro na nuna goyon baya a Lagos da sauran jihohin Yarabawa a ƙarƙashin ƙungiyarsu ta NADECO, wasu kuma sun shiga jam’iyyar AD har suka ci zaɓe kamar Bola Ahmed Tinubu a jihar Lagos. Wannan shi ne asalin gwagwarmayar June 12 da ta kawo har aka mayar da ita ranar biki mulkin damokuraɗiyya a Najeriya. Shugaba Muhammadu Buhari yace ya mayar da ranar demokuradiyya ta koma sha biyu ga watan Yuni.

RIBAR DAMOKURAƊIYYA GA ‘YAN NAJERIYA 

Yau an samu kimanin shekaru ashirin da biyar ana bikin ranar damokuraɗiyya a Najeriya tun daga 1999-2024, amma mutanen Najeriya suna cewa su har yanzu ba su ci gaba ba. Me yasa kuma har yanzu wasu suna ganin tsarin da ake tafiya bai kamata a yi shi ba? Tsarin baya a dawo da shi, kwan-gaba-kwan baya, waɗannan abubuwa su ya kamata mu yi nazari a kansu.

Akwai abubuwa da yawa da suka kawo rashin cin ribar damokuraɗiyya a Najeriya. Zamu kalli abu biyu zuwa uku, da farko tushe, cewa Najeriya ta samu matsaloli na siyasa, wato ko ta soja ko ta farar hula. 

Ba ta samu dama ta kafa tattalin arziƙi a lokutan farar hula ba, haka kuma a lokutan soja, da ya zauna da gindinsa ba. Idan ba a samu kafuwar tsarin tattalin arziƙi da ya kafu da gindinsa ba, duk abin da aka ɗora masa ba zai zauna ba. Mutane kawai abin da suke hanƙoro shi ne su shiga gwamnati su samu kuɗi. 

Idan muka duba daga 1960 tun lokacin da Najeriya ta samu ‘yanci, mutane suna ganin Najeriya zata zama wani abu a duniya, saboda duk abin da ake tunani da akwai shi a ƙasar; akwai mutane da albarkar ƙasa. Ya kamata a ce an samu cigaba.

  A jamhuriya ta farko ‘yan siyasa babu abin da ke gabansu sai yaya za a cigaba da mulki, kowanne sashi yana hanƙoro sai ya riƙe mulki, kuma sai sashin ya samu kaso mafi yawa na madafan iko a mulkin Najeriya. Wannan ne yasa a wannan jamhuriyar ba a iya assasar da wani abu ba, da ma sojojin da suka biyo baya.

Idan ka dubi duk waɗannan ƙasashen masu hanƙoron cigaba, a wancan lokaci Najeriya ta fi su, hatta China ballantana ka yi maganar irin su Korea da Indonesia da Malaysia amma rashin shugabanci nagari ya haifar da koma baya. Shi kuma shugabanci nagari ya gagara ne saboda ‘yan siyasa ba su ɗauki za su jagoranci mutane da adalci a tsakaninsu ba.

 Kowa kallo yake yi, yaya zai samu abin da zai samu ko ƙabilarsa su samu. Duk ƙasar da ta zama tana da irin wannan ba za ta samu cigaba ba. Muddin ‘yan siyasa ba su yi hakurin cewa za su yi mulki ba tare da cin dunduniyar wani ba, to ba za a samu cigaba ba. Kamar yadda muka faɗa Sir Abubuakar Tafawa Balewa yana ta wannan ƙoƙari amma abu ya gagara.

A lokacin da duk ƙasashen duniya suke samun cigaba, mu kuma ‘yan Najeriya muna faɗa a tsakanin mu. A shekara ta 1968 ƙasar South Korea ta fara yin masana’antar ƙarfe (steel industry), wanda a sannan suna fama da yunwa babu abinci. Amma saboda suna da jagoranci ga abin da suka sa a gaba, cewa idan ba su da ƙarfe ba za su samu cigaba a duniya ba. Suka mayar da hankali suka yi. Duk wanda ya je ƙasar aka kai shi kamfanin mulmula ƙarfensu zai ga irin abin da suka yi.

Mutanen Malaysia suna da matsala ta ƙabilanci a cikin tsarin zamantakewarsu, amma sun yi tunani a tsakaninsu cewa ku Malay tun da ku ne kuka fi yawa zamu bar muku shugabanci a ƙasar nan amma yaya za a yi kowa ya samu ‘yanci a yi kasuwanci don kowa ya amfana. Haka suka hakura suka yi, saɓanin Najeriya sai yaƙar juna ake yi, ba a samu wannan dacewar ba.

 Idan ba a samu wannan yarjejeniyar ba, ba za a samu zaman lafiya ba. Shi ya sa duk abin da waɗannan ƙasashen suka yi mu mutanen Najeriya muka kasa yi. Yanzu Malaysia suna fitar da kaya na sama da Dala biliyan 200-300, yayin da Najeriya muna fita da kaya ne kawai na Dala biliyan 63, South Korea wajen Dala biliyan Dari biyar ($500Billion). 

Yanzu ƙasar da take fitar kaya na dala biliyan 63 ina take da ƙarfin tattalin arziƙi da zai kai ta har a samu cigaba, har a haɗ a su da irin waɗancan ƙasashe. Saboda haka ko ance za a yi zaɓe, ko za a yi damokuraɗiyya ko mulkin soja, idan ba a lalubo hanyar tattalin arziƙi da zai riƙe ƙasar ba, ba za a samu cigaba ba.

Duba da yanayi tattalin arziƙinmu , yanzu duniya ta canja, baka da wani siddabaru da zaka yi, idan ba za ka yi abubuwa ba a kasarka, na kamfanoni da za a yi amfani da su a cikin gidanka. Ba ka da sinadari (chemicals) ko sumunti, ko tama da ƙarafa. To yanzu a Najeriya babu ɗaya da ake da shi. 

Sai yanzu da ance za a samar da sumunti da fetur. Maganar gaskiya ba ka da wani siddabaru idan ba ka da waɗannan kayayyaki, sannan ka ce za ka cigaba. Tattalin arziƙinmu ba zai gyaru ba saboda ‘yan siyasa abin da ke gabansu mulki, ba sa tunanin su haɗa kai don mutanen ƙasarsu. 

 Saboda rashin haɗin kai ya zama babu wata jam’iyya a Najeriya, yanzu abin da muke da shi, taron mutane kowa yana son ya yi mulki ko ya haɗa kai da wasu ya yi damfara, ya yi cuta a zaɓe ya zama shugaban ƙasa. 

Shi yasa zaka ga wani ya yi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyu daban- daban, ya yi PDP, ya yi ACN, ya yi a APC, ya sake dawowa PDP, wani ya yi takara a jam’iyya wani ya fito takara sosai. Duk irin wannan babu aƙida ta siyasa da manufa da tsayawa a kan kyakkyawan ƙudiri na tsari ko na shekara takwas, ko shida ko ma hudu duk babu.

Yanzu jam’iyyar PDP ta yi mulki a Najeriya tsawon shekara goma sha shida, amma babu abin da ta aiwatar, saboda ba ta da tsari maje-gaba, na maganar tattalin arziƙi, wanda zai fitar da ‘yan Najeriya.  Tun lokacin Obasanjo daga 1999-2015 ba a yi wani abu na tattalin arziƙi mai dogaro da abincin da zamu iya ciyar da kanmu, za mu samu lantarki, za mu samu wasu abubuwan more rayuwa dasu ba. 

Jam’iyyar PDP ba ta samar ba haka suka gama mulkinsu. APC ta zo a 2015, ita ma ta ƙare baragadarta, sai ya zamo ‘yan siyasa, wani ne zai fito ya ce zai yi takara yana son zai zama shugaban ƙasa, ya zo ya yi abin da zai yi ya ci shugaban ƙasa, ya debo mutanensa su yi abinda suka ga dama, ta yaya zaka ce zaka ci ribar damokuraɗiyya a nan. 

Wai wannan ma ya zama labari, shi yasa za mu yi ta zama a wuri ɗaya, idan wasu ƙasashen suna yin ƙere-ƙeren nan dole a samu mota, dole a samu jirgin sama. Wane irin tunani ne za ka haɗa Najeriya da Malaysia da ba su wuce mutum miliyan talatin ba. Amma suna fitar da kaya na sama da dala biliyan dari biyu, mu kuma muna fitar da kaya na dala biliyan sittin. Ka ga daga ji ka san wannan ƙasar ba a ɗora ta a kan gaskiya ba. Idan za a shekara dubu a Najeriya ba za a samu damar ɗora tattalin arziƙi ba, ba za a samu cigaba ba. 

An raba kan mutane, an ce wannan ƙabilarsa daban, wannan addininsa daban , wannan sashensa daban. Ana amfani da wannan don su karɓi mulki su yi abin da suka ga dama. Ya zama cewa babu inganci a yadda rayuwa take. Duk tsarin da ake bi na tabbatar da abubuwa, haka ne. 

idan kana maganar jam’iyya haka suke, idan kana maganar ƙungiyoyi haka suke. Mutane sun kasa ganewa cewa abin da ya kamata mu yi a Najeriya, mu haɗa kanmu, mu yi maganin matsalolin da suke damunmu, ba tare da maganar ɓangaranci ba.

Ya kamata ko mu mutanen Arewa, ɓangaranci a siyasa ba zai kaimu ko ina ba, an yi amfani da ɓangarancin nan an kawo gwamnati ta shekara takwas, me ta yi wa mutanen arewan? Kuma a arewan nan babu wasu da za su ce idan an zo siyasa ga abu kaza da abu kaza da muke so, a matsayinka da kake takara ko ɗan Arewa ne ko ɗan kudu, mu sai ka yi mana wannan zamu zaɓeka.

 

Babu wannan, mutane ma ba su damu da hakan ba, waɗanda suke da ikon yi ba su da damar da za su iya. Saboda ga yadda jam’iyyun suke, idan kana maganar sadarwa da kafofin yaɗa labarai, duk ba mu da su. Yanzu ko kafofin sadarwa na zamani (social media) har sai sun samu labarai daga kafofin sadarwa na ainihi, sannan suke yin wani tasiri. 

Yanzu a gidajen talabijin guda shida da su ka yi fice a Najeriya, AIT, Arise, Channels, TVC, Trust TV , a cikinsu idan ban da Trust duk na ‘yan kudu ne. Haka idan ka zo ka ɗauki jarida, ana yin jaridu guda goma sha shida kullum, guda biyu ne kawai na ‘yan Arewa kawai na Arewa. 

Saboda haka Arewa ba su da kafafen yaɗa labarai da za su dogara da su wajen nemowa Arewan ‘yanci da neman goyon bayan da suke buƙata. Kuma ‘yan siyasa wannan ba shi ne a gabansu ba, kowa hanƙoro yake yi a ba shi takarar gwamna ko ɗan majalisa, ya je ya yi ya dawo kuma da ma mutanensa duk yunwa suke yi. 

Tunda yanzu, gwamnati ba ta ba da ilimi kyauta, ta yaya za a yi mutane kansu ya waye, tun da babu ilimi. Sun cutar da al’umma, sun mayar da su almajirai da ‘yan ta’adda da ‘yan banga saboda rashin ilimi. Ga shi kuma babu aikin yi, haka kuma dama idan siyasa ba ta zama daidai ba, ba yadda za a yi ta tabbatar da tattalin arziƙi, ya zama daidai. 

Ana ta zagayawa a wuri ɗaya (cycling) idan wannan zagaye ba a dakatar da shi ba babu maganar cewa za a zo a yi zaɓe, ko za a yi damokuraɗiyya dai-dai ko za a samu shugabanni nagari. Duk wannan sai dai ya zama labari, kuma duk abin da da zai faru a duniya, mu ne koma-baya, sai dai a bar mu muna suɗi.

 Idan motoci sun mutu a kawo mana daga Korea, daga Amurka, daga inane? Tun da lantarki ma mun kasa samu, balle har ace za mu yi masana’antu, ɗan Arewa ma ya riƙe ya ƙasa. 

Saboda haka, dole mutane su ce ai damokuraɗiyya ba ta zamar mana alheri ba! Duk da cewa mutane sun samu ‘yanci da sauran abubuwa amma tun da babu tsayayyen tattalin arziƙi, damokuraɗiyya ba ta samar musu ba. kuma ba za ta samar musu ba, a dai wannan tsari da ake yi saboda ‘yan siyasar nan suna yin siyasa ne saboda biyan buƙatunsu.

 Idan za ka tsaya takara ko na jiha ko ɗan majalisa, sai kana da ubangida nasu amma yanzu har sun fara caccanza su. Sai dai kuma wani yanayi daga Allah Ya kawo juyinsa, ko wani juyi ya zo a wani zamani, a samu mutane nagari, ya zama abin ya tabbata.

 Mu daina tunanin cewa Najeriya ko tsarin gudanar da mulki ne, wato ko ƙarfin iko daga majalisa (parliament) ko na shugaba mai cikakken iko (presidential) duk ba haka ba ne, mutane ne da matsalar. Idan an samu wasu da zasu maye gurbinsu ba, wanda hakan yana da wahala.

Mun gani a ƙasar Turkiyya zuwan Erdugon, duk wahalar da ƙasar ta sha, sai da aka samu wasu suka kutsa, amma idan ba haka aka yi ba, waɗannan mutanen ko suna PDP ko suna APC, jam’iyyu haruffa ne kawai ya banbanta su. 

Shi ya sa za ka ji  mutum yau APC gobe kuma ka ji shi a PDP jibi ya koma Labour, haka dai za ka ga suna ta yi. Kuma abubuwan nan da suke faruwa a duniya ba wai maganar tafiya sama ba ce. 

Ya gagara a ce gwamnatin Najeriya shekara sittin ba za ta iya ciyar da kanta ba, shekara sittin an samu ‘yancin mulki kai, amma Najeriya ba za ta iya fitar da kaya ba, kai ko da zama muke muna ciyar da kanmu da sauran abubuwa kamar yadda China take yi da yanzu mun cigaba.

Ɗan siyasar Najeriya abin da ke gabansa, ya samu mulki amma ba yadda zai ciyar da ƙasar gaba ba. Waɗanda suke zama suke magana a kafofin yaɗa labarai ko a ina ne, sai ka yi ta shan mamaki, su kuma ‘yan siyasar sun fi son waɗanda za su fito suna zagin wane ko su ce wane ɓarawo ne, ko wanda zai zo bambaɗanci. 

 To wannan shi ne ya sa muke da matsala. Idan ba mu canja siyasar mu ‘yan arewa ba, ba za mu samu cigaba ba. Dama su ‘yan kudu tafiya suke bisa tsari, don haka za su yi ta samun cigaba. Saboda mu ba mu fahimci inda duniya ta sa gaba ba. Muna fatan Allah ya bamu zaman lafiya a ƙasa, ya magance mana fitintinun da suka addabe mu, amin, Subuhanakallahumma… 

 

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

 

                            

labarin da ya wuceTARIHIN ZANGA ZANGA A NAJERIYA: MAFITA KO MAHALLAKA
Labarin na GabaYadda Ake Sabulun Wanka Da Wanki
Dr. Ibrahim Ado Kurawa
An haife ni, a ranar 10 ga Agusta, 1963, a Kano. Na yi karatu a fannoni daban-daban, tun daga kimiyyar halittu har zuwa karatun Larabci da ilimin addinin Musulunci. Na wallafa littattafai da takardu masu yawa kan tarihi, siyasa, da al'adu, wanda hakan ya ba ni damar samun kima a duniya, har ma na zama ɗaya daga cikin masu zama a Rockefeller Villa Serbelloni a Italiya.

SHARHI ƊAYA