An haifi Labaran Adamu Shu’aibu a ƙofar Arewa Gidan Malam Tanko Kudan, a Ƙaramar Hukumar Kudan jihar Kaduna, ya fara karatun allo a wajen Alaramma Aliyu Labaran Ƙofar Arewa Kudan, sai kuma ya wuce jihar Kano wajen Alaramma Hamisu wanda yake Ƙaramar Hukumar Nassarawa Tudun Murtala a wannan makarantar ne ya samu damar sauke Alƙur`ani mai girma, sai kuma ya koma gida ya fara karatun littattafai a wajen malam Magaji na-umma wanda yake ƙofar Arewa, ya yi aure yana da ‘ya mace mai suna Nazifa, amma kuma Allah ya yi wa matarsa ta farko rasuwa bayan ta haifa masa waccan ɗiyar.
Bayan waɗansu lokuta ne sai kuma ya dawo jihar Kano ya kama harkar kasuwanci a ƙaramar hukumar Kumbotso jihar Kano. Sai kuma ya ci gaba da karatun addini a wajen marigayi Malam Adamu Azare limamin Juma’a na Panshekara da kuma Alaramma Misbahu Tsaure. Sannan kuma ya yi karatun boko a Yakubu firamare school wacce take jihar Kaduna a shekara 2001-2007, ya yi karatu a Annur Institute for Islamic education Shahuci a shekara ta 2011, yana yin waƙar bege da waƙar siyasa da dama ga kaɗan daga cikin su;
1. Gari mai albarka (bege)
2. Nana Aminatu (bege)
3. Hajiya Mariya (waƙa ga mahaifiyar Ɗangote)
4. Farin gani Kumbotso (waƙar siyasa ga Sadau)
5. Isah Ashiru (waƙar siyasa ga Rt. Hon. Isah Ashiru Kudan)
6. Mudassir (waƙar siyasa ga Ɗanmajalisa Mudassir) da dai sauran su.
(Mun samu wannan bayani ne daga Labaran Adamu wanda ya rubuto min a ranar Laraba 24/06/2020 da misalin ƙarfe 11;30 na safe).
Domin karanta tarihin Dakta Alhaji Gambo Kudan danna nan
Edita; Rumasa’u M. Kallamu