Tarihin Mawaƙi Salahuddeen Sani Kudan

0
28

An haifi Salahuddin Sani a gidan limamin juma’a na garin Kudan, wanda ke ƙofar Arewa Kudan a cikin ƙaramar hukumar Kudan a ranar 01/01/1989, ya yi karatu a Model Primary school take Kudan a shekara ta 1995-2000. Ya yi karatu G.G.S.S Kudan a 2000-2006, ya yi karatu a makaranatar gaba da sakandire ta Maƙarfi wato Shehu Idris Collage of Health a 2014-2017. Ya yi aikin asibitin kuɗi da ke Kaduna Tudun Wada mai suna AITAM.

Yanzu kuma yana aiki a asibitin Gwamnati wanda ke garin Kudan a cikin ƙaramar hukumar Kudan, jihar Kaduna. Sannan kuma ya fara karatun addininsa ne a makarantar Hayatul Islam ƙofa, wacce take bakin kasuwa Kudan, amma kuma ya yi saukarsa ne a makarantar Irshadul Aulad wacce take ƙofar Arewa Kudan, haka kuma ya fara bege ne a Irshadul Aulad a 2003 waƙar da ya fara yi ita ce “Mubar cuta”, sannan kuma ya yi karatun fiƙihu a wajen marigayi malam Suraj Yunusa Kudan, ya yi karatun allo a wajen Alaramma malam Iliya na tsawon shekara biyu kafin ya kuma zuwa islamiyyah.

Shaharar sa

Shi ne wanda ya assasa ƙungiyar sha’irai a garin Kudan mai suna Raudatul shu’ara’ul Islam Kudan a shekara ta 2015, wanda a yanzu tana da mutane guda ashirin. Bugu da ƙari kuma, ya iya sana’ar kafinta wanda ya koya a wajen ‘ya’yansa wato Ahmad Gaddafi, ya kuma iya sana’ar nona da kiwo, sannan kuma shi ne wanda ya buɗe makarantar Taufiƙil Islam, wanda take Furoja a garin Kudan, jihar Kaduna.

Ya kuma rubuta ƙasidu da dama , ga kaɗan daga cikin kamar haka;

1. Raddi.

2.Shu’ara’u ‘yan Kudan.

3. Raudatul Shu’ara’ul Islam.

4. Ta’aziyyya (Rabi’u).

5. Ƙololuwar matsayi.

6. Ranar murna.

7. Maulidin muke yi.

  1. (Mun samu wannan jawabin ne daga bakin Salahuddin Sani wanda ya rubuta ya turo min da shi ta waya (Message) a ranar Asabar 25/12/2020) da misalim ƙarfe 7;30 na safe).

Domin karanta tarihin Salmanu Faris Adam danna nan

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceTarihin Salmanu Faris Adamu
Labarin na GabaTarihin Hassana Abdullahi Hunƙuyi