Tag: yadda ake

  • Tarihin Malam Ɗankwandarai

    Tarihin Malam Ɗankwandarai

    An haifi Malam Isa Ɗankwandarai a garin Sankara a Ƙauyen Kwandarai. Ya yi tafiye-tafiyen neman karatu har Ubangji Maɗaukakin Sarki Ya hore masa Alƙur’ani; kuma ya yi fice tsakanin makaranta a wannan fage.

    Ya je ƙasar Bima neman karatu har ya kwashe wani lokaci a can. A lokacin da shahararren masanin Alƙur’ani nan Gwani Hamad ya bayyana a birnin Kano; Malam Isa Ɗankwadarai na cikin malaman da suka zama almajiran sahun gaba a wurinsa.

    Wannan ya sa shi yin fice a fagen karatun Alƙur’ani bisa ƙa’i’doji karatu da ilimi Tajwidi har sai da mahaddata suka riƙa zuwa gari da gari don naƙaltar wan nan ilmi a wurinsa.

    Malam Ɗankwandarai ya shahara wajen sanin girman malamai, domin shi ne ya yi wa Gwani Hamad kyautar doki da kayan abinci da sauran hidima akai-akai har sai da ya samu matsayi a wurinsa Ya kasance mutum ne mai taushin hali, ba ya fushi, ga yawan ciyarwa ga almajirai. Ya kasance yana yawan yiwa ‘ya’yansa da almajiransa wasiyya da riƙe Alƙur’ani.

    Saboda kyakkyawar dangantakar sarakuna da makaranta Alƙur’ani kuwa an ce Sarki Sunusi ne ya dawo da shi Kano; ya ba shi wuri don ya gina tsangayarsa.

    Cikin manyan almajiransa akwai Gwani Ɗanbirni da Gwani Saleh Ɗanzarga Ya rasu a zamanin mulkin Sarkin Kano Ado Bayero a shekara ta 1984.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Gwani Ɗanbirni danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Kamilu Almajirin Mawaƙa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Abubakar Malami SAN

    Tarihin Abubakar Malami SAN

    Abubakar Malami SAN, wanda aka haifa a ranar 17 ga watan Afrilu, 1966 a kauyen Gwari dake jihar Kebbi, Najeriya, yana daga cikin shahararrun lauyoyi da masu gudanar da harkokin gwamnati a Najeriya. Ya karanci shari’a a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu digirin farko a fannin shari’a (LL.B). Haka zalika, ya kammala karatunsa na digirin biyu a fannin shari’a (LL.M) daga jami’ar Abuja.

    Malami ya fara aikinsa a matsayin lauya mai zaman kansa sannan daga bisani ya shiga cikin harkokin gwamnati, inda ya kasance babban mai ba wa gwamnatin tarayya shawara kan harkokin shari’a. Ya zama mai ba shugaban kasa shawarwari a kan lamuran shari’a da kuma matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka a fannin shari’a.

    A shekarar 2015, Abubakar Malami ya zama Ministan Shari’a (Attorney General of the Federation) a ƙarƙashin shugabancin Muhammadu Buhari. A wannan muƙami, ya gudanar da wasu muhimman ayyuka ciki har da gyaran dokoki da kuma kawo sauye-sauye a tsarin shari’a na Najeriya.

    Malami ya kasance babban jigo a wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, inda ya ba da gudummawa wajen tabbatar da gudanar da bincike da gudanar da shari’a kan manyan masu laifi.

    Malami sananne ne a fannin shari’a da kuma gudanar da mulki, kuma an ba shi lambar yabo ta SAN (Senior Advocate of Nigeria), wadda take nuni ga manyan lauyoyi a ƙasar. Har yanzu yana ci gaba da taka rawar gani a fannin shari’a da kuma mulkin Najeriya, inda ya kasance cikin waɗanda suke kariya da tabbatar da haƙƙin ɗan Adam a Najeriya.

    Kodayake yana da tasiri sosai a harkokin gwamnati da shari’a, Abubakar Malami yana fuskantar ƙalubale kan wasu batutuwa na zamantakewa da siyasa, suna mai bayyana aikin da ya ke yi a matsayin wanda ke da tasiri ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

    Danna nan don karanta Faɗakarwa A Kan Cin Hanci Da Rashawa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Shiga Wata Karkara Ko Wani Gari

    Addu’ar Shiga Wata Karkara Ko Wani Gari

    اللهم رَبَّ السَّمَوَاتِ السَّبْع وَمَا أَظْلَلْنَ، وَرَب
    الأَرَضِينَ السَّبْعِ وَمَا أَقْلَلْنَ ، وَرَبَّ الشَّيَاطِينِ وَمَا أَضْلَلْنَ ، وَرَبَّ الرِّيَاحِ وَمَا ذَرَيْنَ ، أَسْأَلُكَ خَيْرَ
    هَذِهِ الْقَرْيَةِ وَخَيْرَ أَهْلِهَا وَخَيْرَ مَا فِيهَا ، وَأَعُوْذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ أَهْلِهَا وَشَرِّ مَا فِيهَا.

    Allahumma rabbas-samawatis-sab’i wama azlalna, warabbal- aradeenas-sab’i wama aƙlalna, warabbash-shayateeni wama adlalna, warabbar-riyahi wama zarayna, as-aluka khayra hathihil-qaryah, wakhayra ahlilha wakhayra ma feeha, wa- a’oozu bika min sharriha washarri ahliha, washarri ma feeha.

    Ya Allah! Ubangijin sammai bakwai da abin da suka rufe, kuma Ubangijin ƙassai bakwai da abin da suke ɗauke da shi, kuma Ubangijin shaiɗanu da waɗanda suka ɓatar, kuma Ubangijin iska da abin da ta yayyaɗa! Ina roƙon Ka alherin wannan alƙarya, da alherin mutanen da ke cikinta, da alherin abin da ke cikinta. Kuma ina neman tsari da Kai daga sharrinta, da sharrin mutanenta, da sharrin abin da ke cikinta.

    Karanta Addu’a Idan Mutum Ya Ga Wani Abu Mai Ban Mamaki

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’a Idan Mutum Ya Ga Wani Abu Mai Ban Mamaki

    Addu’a Idan Mutum Ya Ga Wani Abu Mai Ban Mamaki

    Addu’a idan mutum ya ga wani abu mai ban mamaki, ko na farin ciki

    سُبْحَانَ اللهِ

    Subhanallah

    Tsarki ya tabbata ga Allah.

    الله أكبر

    Allahu akbar

    Allah ne Mafi girma.

    Danna nan don karanta Addu’a Ga Wanda Yace Maka: Allah Ya Yi Maka Albarka

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’a Ga Wanda Yace Maka: Allah Ya Yi Maka Albarka

    Addu’a Ga Wanda Yace Maka: Allah Ya Yi Maka Albarka

    وَفِيكَ بَارَكَ الله.

    Wa fi ka  barakallah

    Kai ma Allah ya yi maka albarka.

    Karanta Addu’a Ga Wanda Aka Zo Biyansa Bashinsa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Shigowar Ƙananan Ƙabilu Ƙasar Hausa

    Shigowar Ƙananan Ƙabilu Ƙasar Hausa

    Sauran Ƙabilu

    Bayan waɗannan al’ummomi da aka yi bayani kan shigowarsu ƙasar Hausa akwai wasu ƙananan ƙabilu waɗanda suke maƙwabtaka da suka shigo. Misali, a kudancin Jihar Kaduna akwai ire-iren waɗannan ƙananan ƙabilu waɗanda suka haɗa da Katab da Morwa da Kaje da Kagoro da Jaba da Kaningkon da Ninzam da Ayu da Kadara da Gwari da Gwandara da Kagoma da sauransu.

    Akwai wasu kuma a yankin Filato waɗanda suka haɗa da Birom da Angas da Ganawuri da Sayawa da sauransu. A jihohin Bauchi da Gwambe akwai wasu ƙananan ƙabilun kamar Gerawa da Terawa da Jerumawa da Ganjuwa da Denawa da Kanakuru da Tangale da Waja da dai sauransu. A ƙasar Hausa ta yamma akwai wasu ƙananan ƙabilun da suke zaune a yankin Yawuri da Kwantagora waɗanda suka haɗa da Dakarkari da Kambari da Kamuku da dai sauransu.

    Shigowar Ƙananan Ƙabilu Ƙasar Hausa

    Akwai daɗaɗɗiyar dangantaka a tsakanin Hausawa da waɗannan ƙananan ƙabilu masu maƙwabtaka da ƙasar Hausa. Mafi yawa daga cikin waɗannan ƙananan ƙabilu sun zauna a ƙarƙashin mulkin sarakunan ƙasar Hausa waɗanda suke maƙwabtaka da su. Misali, ƙabilun da suke kudancin jihar Kaduna sun zauna a ƙarƙashin mulkin Sarkin Zazzau tun cikin ƙarni na goma sha takwas, wanda shi ya sa a yanzu ake kiran su da sunan ƙabilun kudancin Zariya (Adeleye, 1975:593).

    Ta wannan hanya ce al’ummomin waɗannan ƙananan ƙabilu suka riƙa hulɗoɗi da Hausawa. Ta hanyar waɗannan hulɗoɗi mafi yawa daga cikin al’ummomin waɗannan ƙabilu da suke maƙwabtaka da ƙasar Hausa koyon harshen Hausa wanda ya zama harshe na biyu gare su bayan harshen da suka gada.

    Haka kuma harshen Hausa ya zama harshen da kowa da kowa daga cikin su yake amfani da shi wajen sadarwa da kasuwanci da addini da sauran ma’amalolin rayuwa na yau da kullum a tsakaninsu da sauran al’ummomin da suke cikin ƙasar Hausa da kuma waɗanda suke maƙwabtaka da su. A sakamakon wannan dangantaka ne, a yanzu harshen Hausa yake ƙoƙarin mamaye waɗannan ƙananan harsuna da suke maƙwabtaka da ƙasar Hausa.

    Idan muka juya kan shigowar al’ummomin waɗannan ƙananan ƙabilu cikin ƙasar Hausa, za a ga mafi yawancinsu sun shigo a cikin ƙarni na ashirin. Wannan kuwa ya faru ne a sakamakon kafuwar mulkin mallaka wanda ya haɗa waɗannan al’ummomi wuri ɗaya a ƙasa ɗaya.

    Kamar yadda wasu daga cikin waɗannan al’ummomi suka shigo cikin ƙasar Hausa, akwai wasu Hausawa da suka yi ƙaura daga ƙasar Hausa suka shiga ƙasashensu. Misali, a sakamakon samun kuza da kwaranda a ƙasashen da suke kudancin Zariya da yankin Filato tun cikin shekarun 1920, an sami Hausawa waɗanda suka yi ƙaura daga Kano da Katsina da Zariya da Sakkwato suka koma waɗannan ƙasashe.

    A wuraren da suke zaune sun riƙa yin hulɗa da al’ummomin wuraren, wannan ya sa sun auri mata ‘yan ƙasar suka mayar da su Hausawa (Hira da GMW, a garin Godo- Godo da kuma MIM, a garin Kafanchan, a ranar 24/8/2004).

    Nason Al’adun Sauran Baƙi Kan Wanzancin Hausawa

    Sauran baƙi a nan ana nufin ƙananan ƙabilu waɗanda suke maƙwabtaka da Hausawa daga kudu da kudu-maso-gabas da kuma kudu-maso-yamma da ƙasar Hausa. Dangane da wannan bincike an duba ƙabilun Dakarkari da na kudancin jihar Kaduna da kuma ƙabilar Tera a jihar Gwambe.

    A nazarin da aka gudanar a waɗannan ƙabilu an fahimci nauyin al’adunsu cikin wanzanci ba shi da yawa. Wannan kuwa ya faru ne saboda yadda al’adun Hausawa suka taushe al’adunsu ta yadda a wannan zamani wasu daga cikin al’adunsu sun fara ɓacewa na Hausawa na maye gurbinsu. Amma duk da haka ga ɗan abin da aka samu.

    Magungunan da Wanzamai Suka Samo Daga Wurin Dakarkari

    Hausawa sun sami wasu magunguna daga wurin Dakarkari mazauna ƙasar Zuru a cikin Jihar Kebbi. Ire-iren waɗannan magunguna sun haɗa da na ƙarin ƙarfin azzakari. A wannan magani ana samo sauyoyin wani icce da ake kira jan yaro, sai a taho da su gida a sanya aska ko wuƙa a kankare su sosai.

    Daga nan sai a ɗebo gero daidai gwargwadon wanda idan an yi kunu da shi mutum zai iya shanye shi, sai a sanya wannan bayan sauyoyin jan yaro da aka ɗebo a cikin tukunya a tafasa a dama kunun salala. Wannan kunu ne mutum zai yi ta sha sannu a hankali zai ji azzakarinsa ya yi ƙarfi sosai.

    Wani magani da Hausawa suka samu daga Dakarkari shi ne, na nuna buwaya. Ana samun ƙanzon tuwo da aka yi a gidan wanda zai yi amfani da maganin, sai a ɗebo sassaƙen iccen gamji a daka shi.

    Daga nan sai a haɗa garin wannan magani da ƙanzon tuwo a sa a ruwa a cakuɗa su a yi mulmule uku, za a riƙa cin mulmule ɗaya a kullum har zuwa kwana uku. Idan aka yi haka mutum zai buwaya a duk duk wurin da yake. Idan aka yi kuskure aka ci sau huɗu, to mutumin zai zama maye (AGMSAZ, 21/5/2005).

    Magungunan da Wanzamai Suka Samu Daga Wurin Terawa

    Tera wata ƙabila ce wadda ake samu a wuraren da suka haɗa da garuruwan Gwani ta gabas da Gwani ta Yamma a Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba a Jihar Gwambe. Al’ummar Tera tana tafiyar da al’adun wanzanci kamar yadda Hausawa suke tafiyar da nasu. Wannan dalili ya sa aka sami kamanci da bambanci dangane da yadda suke tafiyar da wannan sana’a a tsakaninsu.

    Haka kuma akwai fahimtar juna a tsakaninsu wadda ta haifar da musayar al’adu. A saboda wannan dalili ne wanzaman Hausawa suka sami maganin ƙurajen aski daga wurin Terawa.

    A lokacin da aka yi wa mutum aski don maganin ƙurajen aski, sai ya sami buri na hura-hura wadda ‘yan mata suke talla, ya shafa a wurin da aka yi masa aski. A duk lokacin da aka yi masa aski idan ya shafa wannan gari ƙurajen aski ba za su fito masa ba (MYHW, 13/8/1998).

    A taƙaice kamar yadda aka gani wannan babi an yi bayani ne kan nason da al’adun baƙi na kusa waɗanda suka haɗa da Fulani da Barebari da Buzaye da Nufawa da Yarabawa da ƙananan suka yi a kan wanzanci.

    An duba rawar da al’adun waɗannan baƙi suka taka wajen kawo wasu sauye-sauye dangane da yadda Hausawa suke gudanar da al’adunsu waɗanda suka shafi aski da cire belun-wuya da na mata da kaciya da tsaga da kuma magungunan gargajiya.

    Karanta Nason Al’adun Yarabawa A Kan Wanzancin Hausawa

    Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU ya wallafa WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

    MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

    Edita@rumasau-kallamu

  • Zubar Da Ruwa A Farko Da Kuma Ƙarshen Juna Biyu

    Zubar Da Ruwa A Farko Da Kuma Ƙarshen Juna Biyu

    Zubar da ruwa ga farkon ciki da kuma ƙarshen ciki musamman daga wata 8 zuwa haihuwa ba cuta ko matsala ba ce ga mace.

    Lokacin da mace ta samu ciki wasu matan na samun wannan zubar ruwan saboda canje-canje da jikin su ya samu a karon farko, da kuma matan da cikin su ya kusa haihuwa sukan samu wannan alamun na ganin ire-iren waɗannan ruwan a gabansu suna zuba to wannan ba sunanshi da akwai infection ko matsala ba.

    Normal vaginal discharge during pregnancy is called leukorrhea and is thin, white, milky, and mild smelling. Leukorrhea is normal and nothing for you to worry about.

    Sai dai daga lokacin da aka ga ire iren waɗannan ruwa na zuba a tsaya a fahimci kalar su don tantance irin ruwan da ke zuba wanda zai jadda ba na matsala ba ne. Lokacin da aka ga irin wannan ba a buƙatar amfani da Tampons ga mace mai tsohon ciki don kaucewa shigar ƙwayoyin halitta na micro organism.

    Karanta Menene Ƙaiƙayi? (ITCHING)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Faɗakarwa A Kan Cin Hanci Da Rashawa

    Faɗakarwa A Kan Cin Hanci Da Rashawa

    Majalisar Tarayya da Zargin Naira Miliyan Uku

    Ƙungiyar SERAP ta fito fili ta buƙaci EFCC da ICPC su binciki Majalisar Tarayya kan zargin cewa ana buƙatar naira miliyan uku kafin a gabatar da ƙuduri. Wannan magana ba ƙaramin abin damuwa ba ne.

    Abin Da Ya Jawo Cece-kuce

    Majalisar Tarayya ta daɗe tana fuskantar tuhuma. An taɓa zargin budget padding a shekarar 2016, wato ƙara wasu abubuwa a cikin kasafin kuɗi domin aljihun wasu. Haka nan ana yawan sukar constituency projects, inda kuɗi ke ɓacewa ba tare da an yi ayyukan da ya kamata ba. Wannan sabon batu na naira miliyan uku ya zo ne ya ƙara girgiza martabar majalisa.

    Illar Idan Gaskiya Ne

    Idan har wannan zargi gaskiya ne, to abin yana da matuƙar haɗari. Domin ya nuna cewa ba za ka iya gabatar da ƙuduri ba sai ka biya kuɗi. Wannan ba wai kawai cin hanci ba ne, har ma zalunci ne ga jama’ar da suka zaɓi wakilan su da fata cewa za su kare muradunsu. A irin wannan yanayi, ƙudurin da zai gabata ba lallai ya zama na amfani ga jama’a ba, sai dai na masu kuɗi.

    Hukumomin Yaki Da Cin Hanci

    Idan aka ce EFCC da ICPC za su binciki batun, wannan dama ce gare su su nuna cewa suna aiki ba tare da nuna bambanci ba. Amma idan suka yi shiru, jama’a za su ƙara yanke ƙauna daga gwamnati da tsarin doka.

    Darasi Ga Jama’a

    Dimokuraɗiyya tana hannun jama’a. Idan aka ci gaba da zaɓen ‘yan majalisa da ake zargi da rashawa, to jama’a za su ci gaba da fuskantar wahala. Kuri’a ce kawai makamin talaka.

    Kammalawa

    A yau, Majalisar Tarayya na fuskantar sabon jarabawa. Idan ta kasa kare kanta daga wannan tuhuma, martabarta za ta sake raguwa. Amma idan hukumomin bincike suka tashi tsaye suka tabbatar da gaskiya, hakan zai taimaka wajen dawo da ɗan ƙaramin imani ga al’umma.

    Cin hanci shi ne cutar da ta fi kowace lalata Najeriya. Duk wani batu da ya shafi majalisar dokoki ya kamata a yi masa duba sosai, domin a can ne ake tsara makomar jama’a.

    Tarihin Dr. Yusuf Bala Usman danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’a Ga Wanda Aka Zo Biyansa Bashinsa

    Addu’a Ga Wanda Aka Zo Biyansa Bashinsa

    Addu’a ga wanda ya ba da bashi idan aka zo biyan sa bashinsa

    بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي أَهْلِكَ وَمَالِكَ ، إِنَّمَا جَزَاءُ السَّلَفِ الْحَمْدُ وَالأَدَاء .

    Barakallahu laka fi ahlika wa malika. Inna ma jaza’u salafil hamdu wal’ada’i

    Allah ya yi maka albarka a cikin iyalinka da dukiyarka. Haƙiƙa sakamakon bashi shi ne godiya da biya.

    Karanta Addu’ar Ƙin Shu’umci

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Ƙin Shu’umci

    Addu’ar Ƙin Shu’umci

     

    اللهُمَّ لاَ طَيْرَ إِلا طَيْرُكَ وَلَا خَيْرَ إِلا خَيْرُكَ وَلاَإِلَهَ غَيْرُكَ

    Allahumma la ɗaira illa ɗairuka wala khaira illa khairuka wala ilaha gairuka

    Ya Allah! Babu shu’umci sai abin da Ka halitta, kuma babu alheri sai alherinka, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba.

    Ƙarin Bayani; Shu’umci shi ne mutum ya kudurce cewa wani abu mummuna zai faru gare shi saboda ganin wani abu ko jin sa. Wannan haramun ne, saboda abin da ke cikinsa na jingina tasiri ga wanin Allah, da kuma munana zato ga Allah. To wanda irin wannan ya afku gare shi, kar ya bar aikata abin da ya yi nufin yi; sai ya tuba ga Allah, sannan kaffararsa ita ce ya faɗi wannan addu’ar. [Bayanin mai tarjama].

    Don karanta Addu’ar Wanda Ya Ji Wani Ciwo A Jikinsa danna nan

    Edita@rumasau-kallamu