Tag: yadda ake

  • Mijin Marigayiya Babi Na Ɗaya

    Mijin Marigayiya Babi Na Ɗaya

    ‘Hey Babe.’ Ta faɗa tana wani rangwaɗa kai tare da juya ƙwayar idonta kamar dai ga Babe ɗin a gabanta tana kallonsa. ‘Mai kyau, ya kike?’ Ya faɗa daga ɗaya ɓangaren. ‘Lafiya. Yanzu nake dawowa daga school gashi nan na kusa shiga gida.’

    ‘Oh, ni ma yanzu na mayar da su Afaf gida wajen Hajiya. Mun je shopping ne and I bought a few  things for you nake so na kawo miki later. Is that ok? ‘Yes Babe, kai ma ka san ina nan idan dai kai ne kake son ganina. Ya yarana? Hope suna lafiya?’

    ‘Alhamdulillah ga su nan. I just can’t wait to have you so we can all live in one place na huta da  visiting yarana.’ ‘Aww! Kada ka damu, very soon in sha Allah. We will talk more about it idan ka zo in sha Allah  don yanzu zan shiga gida ka san Mommy ta hanani waya a kan hanya.’

    Ya yi ‘yar dariya yace ‘Kuma fa haka ne, to sai mun haɗu.’ Suka yi sallama suka ajiye wayar. Da sallama ta shiga gidan tana ta fara’a kamar wadda aka yi wa wani babban albishir. Babu kowa  a parlor ɗin sai Mommy tana shirin tashi ta shiga sallar Magriba. Bayan ta amsa sallamarta tace  ‘Yau kuma haka kike tafe kina tallan macleans?’

    ‘Kai Mommy! I’m just Happy.’ Ta faɗa tana dariya. Ta wuce ɗakinsu yayin da Mommy ta shige nata ɗakin. Tana sane da yanda take tafiya tana murmushi ɗin kuma tana jin daɗin hakan. Idan dai a kan  Mustapha ne fiye da haka ma za ta yi. Muryarsa kawai take buƙatar ji ta shiga farin cikin da ba ya  misaltuwa. Wata bakwai da suka wuce suka haɗu, amma saboda yanda ya iya soyayya da  tarairaya ya shiga zuciyarta kamar wanda suka yi shekaru a tare.

    Da ya sami yanda yake so ma da tuni an ɗaura musu aure don shi a shirye ya zo, ita ce take ɗan dakatar da shi don tana so ta gama level 1 kafin a yi mata auren. Sai dai a daren jiya Baffanta ya sanar da ita cewa ta gaya  masa ya turo maganar aurensu. Ta jefa Jakarta a kan gadonsu wadda ta faɗa kan ƙanwarta Nabila. Nabila ta make jakar ta ja  tsaki tace ‘A a, must you be stubborn?’

    Tayi dariya tana cewa ‘A tashi dai a yi sallah.’ Ta matsa gaban wardrobe ta fara kokarin cire kayan jikinta.

    Kamar yanda ya yi mata alƙawari ana idar da sallar isha’i ya iso gidan nasu. A tsakar gida suka  zauna inda ta saka musu kujerun roba a rumfar mota, ta ajiye ƙaramin tebur a tsakanin kujerun  wanda ta ɗora ruwa da lemon roba masu sanyi a kai.

    Bayan sun gaisa suka ɗan taɓa hira, hirar da a mafi yawancin lokuta ita ce take yi shi bin ta kawai yake da kallo yana murmushi yana ba ta gajerun amsoshi. Mustapha kenan; haka yake kamar wani basarake, komai nasa a hankali sannan kuma bisa tsari.  Wannan ya sa yake ƙara burge ta.

    Ta ɗauki ruwan robar da ta ajiye ta buɗe ta miƙa masa tana cewa ‘Ko ruwan ba ka sha ba Yallabai.’ Ya yi murmushi yayin da ya karɓi ruwan yana cewa ‘Kuma kin san ƙishirwan nake ji ba, don tun  daga gida muke waya da su Afaf har na zo nan suna ta surutu duk sun gajiyar da ni.’

    ‘Kai haba, surutun na su nawa yake?’ Ta faɗa tana dariya. Suka cigaba da hirarsu har zuwa lokacin da ya tashi tafiya wajen ƙarfe tara. Sai da ta raka shi bakin motarsa kafin ta yi masa sallama sannan tace ‘Baffana yace na gaya maka mutanen  gidanku za su iya zuwa maganar aurenmu ranar Asabar mai zuwa.’

    Take fara’ar sa ta ƙara faɗi, ya dube ta kamar ya rungume ta yana ta murmushin da ita ma yake saka ta murmushi. Yace ‘Allah Khadeeja! Kai amma na ji daɗi wallahi, in sha Allah ranar Asabar ɗin kuwa za su zo da kuɗin aure da sadaki gaba ɗaya.’ Ta yi dariya ‘Kai garaje, saurin me kake?’

    ‘To ai na kula ba kya tausayina, so kike ki yi ta ja min rai kina bari na sauro yana cinye ni saboda  zance.’ ya faɗa da murya kamar ta mai shagwaɓa. Ta yi dariya ‘To kwanan nan za ka huta in sha Allah.’ Suka yi sallama cike da farin ciki bayan ta sanar da shi gidan kakanta inda nan ne za su je maganar  auren nata.

    Cikin walwala yake tuƙin lokaci zuwa lokaci yana yi wa kansa murmushin jin daɗi saboda wannan labarin da Khadeeja ta sanar da shi. Watansu bakwai kacal da haɗuwa amma ya nutsu da hankalin yarinyar kuma ya yaba da tarbiyyar gidansu, ya tabbatar za ta kular masa da su Afaf kuma za ta tsaya a kan tarbiyyarsu ba tare da wata mugunta ba.

    Wata takwas kenan da rasuwar matarsa Asma’u, wadda ita ce ta haifa masa yara huɗu; Afaf mai  shekaru goma sha ɗaya, Habib mai shekaru tara, Nasreen mai shekaru shida sai Shukra mai shekaru uku. Ba wani rashin lafiya ta yi ba, haka kawai da daddare tace kanta yana ciwo don haka a gaba ya saka ta sai da ta sha ƙwayar Panadol sannan ta kwanta; sai dai da yake kwananta sun ƙare haka aka wayi gari sai gawarta. Ya yi matuƙar baƙin cikin rasuwar Ma’u kuma ya ji tausayin  kansa da yaransa, gaba ɗaya rayuwarsa ta tsaya saboda rashin Ma’u.

    Tunda aka kwana uku da rasuwar Asma’u mahaifiyarta ta tattara yaran ta tafi da su gida aka cigaba da kula da su. Can yake zuwa kullum ya ɗauke su ya kai su makaranta idan an tashi ya mayar da su. Ana kula da su sosai kuma suma suna jin daɗin zaman gidan sai dai shi ya fi so ya  rayu tare da yaransa.

    Da farko ya so ya kwashe su ya kai su gidan yayarsa; tunda mahaifiyarsa ta tsufa da yawa ba za su sami kulawa ba a wajenta. Amma sai mahaifiyar Ma’u tace ba za ta bayar  da yaran ba. Sun so su sami matsala domin da kwashe su ya yi ba tare da izininta ba ya mayar da  su gidan Yayar tasa, sai da manya suka shiga cikin maganar aka yi yarjejeniya a kan idan ya yi  aure zai je ya ɗebi yaransa. Don haka ba ƙaramin daɗi ya ji ba da Khadija tace an ba shi izini ya turo.

    Ya riga ya sanarwa Khadija idan ta tare zai dawo da yaransa kuma tayi na’am da hakan. Shi yasa ma wasu lokutan yake kwaso su ya kai mata su har suka saba sosai. Ya yi mata bayanin irin ƙaunar da yake musu da kuma yanda yake so ta dinga kula da su kamar ita ta haife su; kuma ta yi na’am  da hakan. Don ko a yanzun ma tana ƙoƙari wajen hidimarsu da jansu a jiki ga kyaututtuka, gashi  wata ran da kanta take masa waya ya kawo mata su.

    Duk da ya riga ya je gidan mahaifinsa da safe amma a daren ma haka ya koma cike da farin ciki  ya sanar da mahaifinsa cewa iyayen Khadija sun ba shi damar ya turo. Mahaifinsa yana zaune a  kan kafet a dakinsa ya dube shi bayan ya gama sanar da shi inda za a kai kuɗin yace ‘Shikenan  rigimar yara ta ƙare ko, ga amarya ga yaranka sai ka sami natsuwa.’

    Ya yi dariya ya sunkuyar da kai. Daga baya ya yi musu sallama ya wuce gidansa cike da farin ciki.

    Karanta Yadda Ake Lefe A Auren Hausawa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tarihin Kafuwar Ƙasar Qatar

    Tarihin Kafuwar Ƙasar Qatar

    Daga Ottoman Empire zuwa Mulkin Mallaka da Bayan ’Yancin Kai

    Gabatarwa

    Qatar ƙasa ce da ke Tekun Farisa (Persian Gulf), wadda ta samo kanta daga ƙarƙashin mulkin dauloli daban-daban har zuwa samun cikakken ’yancin kai a shekarar 1971. Tarihinta ya haɗa da tasirin Ottoman Empire, mulkin mallakar Birtaniya, da kuma gwagwarmayar da ta yi wajen bunƙasa tattalin arzikinta ta hanyar mai da iskar gas na halitta.

    1. Qatar a Zamanin Daular Ottoman

    Tun daga ƙarni na 16, yankin Qatar ya kasance a ƙarƙashin tasirin Daular Ottoman, bayan sun ƙwace ikon Tekun Farisa daga Mamluks a 1517. Duk da haka, ikon Ottoman bai yi ƙarfi sosai a yankin ba, musamman saboda nisan ƙasa da kuma tsananin tasirin ƙabilu na cikin gida.

    A ƙarni na 19, Sheikh Mohammed bin Thani, wanda daga baya ya zama uba ga gidan Al Thani, ya nemi tallafin Ottoman domin kare Qatar daga mamayar Bahrain da sauran makwabta.

    2. Mulkin Mallaka da Tasirin Birtaniya

    Bayan raunin da Daular Ottoman ta shiga a farkon ƙarni na 20, Qatar ta shiga ƙarƙashin tasirin Birtaniya. Yarjejeniyar Anglo-Ottoman ta 1913 ta tabbatar da janyewar Ottoman daga yankin.

    A 1916, Sheikh Abdullah bin Jassim Al Thani ya rattaba hannu kan yarjejeniyar da Birtaniya, wadda ta sanya Qatar ƙarƙashin kariya (protectorate). Wannan ya ba Birtaniya ikon kula da tsaro da hulɗar ƙasashen waje, yayin da gidan Al Thani ya ci gaba da sarauta a cikin gida.

    3. Durƙushewar Tattalin Arziki da Gano Mai

    Qatar ta dogara da kamun kifi da nemo lu’u-lu’u (pearling industry) har zuwa shekarun 1930. Rushewar kasuwar lu’u-lu’u saboda synthetic pearls daga Japan da kuma bala’in tattalin arziki na duniya ya jefa ƙasar cikin fatara.

    Sheikh Abdullah ya rattaba hannu da Anglo-Persian Oil Company a 1935, amma haƙar mai ta fara ne a hukumance a 1949 saboda Yaƙin Duniya na II. Wannan ya fara sauya tattalin arzikin Qatar daga talauci zuwa samun kuɗaɗen shiga.

    4. Hanyar Samun ’Yancin Kai

    A shekarun 1950–1960, kuɗaɗen mai sun fara canza tsarin rayuwa a Qatar. Bayan Birtaniya ta sanar da janyewarta daga yankin Gulf a 1968, Qatar ta fara tunanin shiga cikin United Arab Emirates, amma ta janye saboda sabani da Bahrain.

    A ƙarshe, a 3rd September 1971, Qatar ta ayyana ’yancin kanta kuma Sheikh Khalifa bin Hamad Al Thani ya zama Amir na farko a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

    5. Bunƙasar Tattalin Arziki Bayan ’Yancin Kai

    Bayan samun ’yancin kai, Qatar ta ci gaba da dogaro da mai. A shekarun 1980s zuwa 1990s, gwamnatin ƙasar ta karkata ga isakar gas na halitta (LNG) daga babban filin North Field, wanda shi ne ɗaya daga cikin manyan ajiyar gas a duniya.

    Wannan mataki ya bai wa Qatar damar zama ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya arziki, tare da zuba jari a fannoni kamar:

    • Ilimi (Qatar Foundation, Education City).
    • Wasanni (FIFA World Cup 2022).
    • Jiragen sama (Qatar Airways).

    Kammalawa

    Tarihin Qatar ya nuna yadda ƙasar daga ƙaramin tsibiri da ke dogaro da kamun kifi da lu’u-lu’u ta koma cikin manyan ƙasashe masu arziki da tasiri a duniya. Hakan ya samu ne ta hanyar gwagwarmaya daga ƙarƙashin mulkin Ottoman zuwa Birtaniya, sannan ta yi amfani da albarkatun mai da gas wajen bunƙasa tattalin arzikin ta.

    Manazarta (References)

    [^1]: Rosemarie Said Zahlan, The Creation of Qatar (London: Routledge, 1979), shafi na 12–25.

    [^2]: Habibur Rahman, The Emergence of Qatar: The Turbulent Years, 1627–1971 (Kegan Paul International, 2005), shafi na 40–52.

    [^3]: Allen J. Fromherz, Qatar: A Modern History (Georgetown University Press, 2012), shafi na 64–70.

    [^4]: J.E. Peterson, Historical Dictionary of Saudi Arabia and the Gulf States (Scarecrow Press, 2003), shafi na 122–130.

    [^5]: Jill Crystal, Oil and Politics in the Gulf: Rulers and Merchants in Kuwait and Qatar (Cambridge University Press, 1995), shafi na 89–92.

    [^6]: Zahlan, The Creation of Qatar, shafi na 130–145.

    [^7]: Rahman, The Emergence of Qatar, shafi na 200–212.

    [^8]: Fromherz, Qatar: A Modern History, shafi na 150–160.

    [^9]: International Monetary Fund (IMF), Qatar: Economic Outlook Report (Doha, 2020).

    Karanta Gudunmawar King Abdulazeez Da Birtaniya Wajen Kafa Ƙasar Saudi Arabia

    Edita@rumasau-kallamu

  • Lissafi Akwai Zaƙi

    Lissafi Akwai Zaƙi

    Assalamu alaikum yara.

    Shin ko kun san cewa lissafi, wato Mathematics,  wani abu ne mai daɗin gaske?  Kuma idan ka iya za ka gane cewa yana da sauƙi. Kawai dai ɗan lokaci za ka ba da ka yi ya bita, sai ka ɗanƊani zumar lissafi.

    Daɗin daɗawa lissafi ilimi ne na yau da kullum. Misali- kullum sai an raba muku abu a gida. Wannan sai da lissafi. Idan kin je yawin sallah kin dawo za ki zo ki ƙirga kuɗin da kika samu. Wannan sai da lissafi. Baban ku zai ce tela ya gwada ku domin ɗinkin kayan salla. Wannan ma sai da lissafi. Idan Abban ki zai gina muku sabon gida sai an yi gwaje-gwaje da yawa. Duka wannan sai da lissafi. Ashe ko yara kun ga ilimin Math yana da matuƙar anfani. Ba abun mu guje shi ba ne. Kawai za mu ba da ɗan lokaci ne sannan kuma mu daina tsoro.

    Sai mun haɗu a gaba

    Domin karanta Yunƙurin Hausantar Da Kimiyya Da fasaha danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Wanda Ya Ji Tsoron Zaluncin Wani Mai Iko

    Addu’ar Wanda Ya Ji Tsoron Zaluncin Wani Mai Iko

    اللهُمَّ رَبَّ السَّمَاوَاتِ السَّبْعِ ، وَرَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، كُنْ لِي جَاراً مِنْ (فُلَانِ بنِ فُلان) وَأَحْزَابِهِ مِنْ خَلَائِقِكَ ، أَنْ يَفْرُطَ عَلَيَّ أَحَدٌ مِنْهُمْ أَوْ يَطْغَى عَرَّ جَارُكوَجَلَّ ثَنَاؤُكَ ، وَلَا إِلَهَ إِلاأنت

    Allahumma rabbas samawatis sab’i wa rabbal arshil azeem, kun lee jaran min (fulan bin fulan) wa’ahzabihi min khala’iƙika, an yafruda alayya ahadun minhum au yadga, azza jaruka, wajalla sana’uka, wala’ila ha illa anta

    Ya Allah! Ubangijin sammai bakwai, kuma Ubangijin Al’arshi mai girma, Ka kasance Mai tsari gare ni daga (wane ɗan wane), da dukkan rundunarsa daga cikin halittunka kar wani daga cikinsu ya yi gaggawar azaba a gare ni, ko ya ƙetare haddi. Kariyarka ta buwaya, kuma Yabonka ya girma, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.

    اللَّهُ أَكْبَرُ، الله أعَزُّ مِنْ خَلْقِهِ جَمِيعاً ، اللهُ أَعَزُّ
    مِمَّا أَخَافُ وَأَحْذَرُ ، أَعُوذُ بِاللهِ الذي لا إلَهَ إلاّ هُوَ ، الْمُمْسِكِ السَّمَاوَاتِ السَّبْعِ أَنْ يَقَعْنَ عَلَى الأَرْضِ إِلا بِإِذْنِهِ ، مِنْ شَرِّ عَبْدِكَ (فَلان ، )وَجُنُودِهوَأَتْبَاعِهِ وَأَشْيَاعِهِ مِنَ الْجِنِّ وَالإِنسِ. اللهُمَّ كُنْلِي جَاراً مِنْ شَرِّهِمْ ، جَلَّ ثَنَاؤُكَ وَعَزَّ حَاَرُكَوَتَبَارَكَ اسْمُكَ ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ (ثلاث مرات)

    Allahu akbar Allahu a’azzu min khalƙihi jami’an,Allahu a’azzu mimma akhafu wa ahzar, a’uzu billahil lazee la’ilaha illahu, almumsikis samawatis sab’i an yaƙa’ana alal ardi illa bi’iznih min sharri abdika (fulan)wajunudihi wa’atba’ihi wa’ashya’ihi minal jinni wal’ins. Allahumma kun lee jaran min sharrihim, jalla sana’uka wa’azza jaruka, watabarakas muka, wala’ilaha gairuka.(salasa marraat)

    Allah Shi ne Mafi girma. Allah Shi ne Mafi buwaya daga dukkanin halittarsa. Allah Shi ne Mafi buwaya daga abin da nake jin tsoronsa kuma nake shayinsa. Ina neman tsarin Allah, Wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Mai rike sammai daga su ruguzo a kan kasa sai da Izininsa, daga sharrin bawanka wane (ya ambaci sunansa), da rundunarsa, da mabiyansa, da kungiyoyinsa na aljanu da mutane.

    Ya Allah! Ka zamo Mai tsari gare ni daga sharrinsu. Yabonka ya girma, kuma Kariyarka ta buwaya, kuma alherin Sunanka ya yawaita, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba. (Sau uku)

    Domin karanta Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Take danna nan 

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Maganin Damuwa Da Baƙin Ciki

    Addu’ar Maganin Damuwa Da Baƙin Ciki

    اللّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ ابْنُ عَبْدِكَ ابْنُ أَمَتِكَ، نَاصِيَتِيبيَدِكَ ، مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ، عَدْلٌ فِيَّ قَضَاءُكَ أسْأَلُكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ سَمَّيْتَ بِهِ نَفْسَكَ أَوأَنْزَلْتَهُ فِي كِتَابِكَ ، أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَداً مِنْ خَلْقِكَ أَوْ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الْغَيْبِ عِنْدَكَ أَنْ تَجْعَلَ
    الْقُرْآنَ رَبيعَ قَلْبِي ، وَنُورَ صَدْرِي ، وَحَلاءَحُزْنِي وَذَهَابَ هَمِّيَْ

    Allahumma inni abduka inbnu abdika ibnu amatika,nasiyatee biyadika,madin fiyya hukmuka, adlun fiyya ƙada’uka, as’aluka bi kulli ismin huwa laka sammaita bihi nafsaka au anzaltahu fee khitabika, au allamtahu ahadan min khal’ƙika awistaasarta bihi fee ilmil gaibi indaka an taj’alal ƙur’ana rabee’a ƙalbee,wa nura sadree wajala’a huznee wazahaba hammee.

    Ya Allah! Ni bawanka ne, kuma ɗan bawanka, kuma ɗan baiwarka. Makwarkwaɗata a Hannunka take, hukuncinka zartacce ne a kai na, kuma ƙaddararka gare ni mai adalci ce. Ina roƙon Ka da kowane Suna naka, Wanda Ka ambaci Kanka da Shi, ko Ka saukar da Shi a cikin Littafinka, ko Ka sanar da Shi ga wani daga cikin halittarka, ko Ka keɓance Kanka da saninsa a cikin ilimin da ke da ke wurin Ka, da Ka sanya Alkur’ani ya zama kaka ga zuciyata, da haske ga ƙirjina, da kwaranyewa ga baƙin cikina, da kuma mai tafiyar da damuwata.

    اللّهُم إنِّي أَعُوْذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحُزْن، وَالْعَجْز وَالْكَسَلِ وَالْبَحْلِ وَالْجُبْنِ ، وَضَلْعِ الدَّيْنِ وَغَلَبَةِالرِّجَال

    Allahumma inni a’uzu bika minal hammi walhuzin, wal’ajzi walkasal walbukli waljubni, wadal’il deeni wagalabatir rijaal.

    Ya Allah! Ina neman tsarinka daga damuwa, da baƙin ciki, da gajiyawa, da lalaci, da rowa, da ragwantaka, da nauyin bashi, da rinjayen mazaje.

    Karanta Addu’ar Addu’ar Shiga Wata Karkara Ko Wani Gari

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Take

    Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Take

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) yace: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: “Ku taru zan karanta muku ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani, sai waɗanda suka haɗu suka haɗu, Sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fito sai ya karanta “Ƙulhuwallahu Ahad”.

    Sannan ya shiga gida, sai muka ce da junanmu mu zaton wahayi ne ya zo masa daga sama, shi ya sa ya shiga gida, sai ya fito ya ce haƙiƙa na ce da ku zan karanta muku ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani, ku faɗaka haƙika ita (ƙulhuwallahu tana daidai da ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani”. (Muslim 812)

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Suratul Falaƙi Da Nasi Ta Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Matakan da Iyaye Za Su Bi Don Kare Tarbiyyar ‘Ya’yansu A Intanet

    Matakan da Iyaye Za Su Bi Don Kare Tarbiyyar ‘Ya’yansu A Intanet

    Shin ka taɓa tsayawa ka lura ko ka tambayi kanka: “Me yasa yarona ba ya fita daga waya ko kwamfuta? Ko Kuma me yake yi da ita wanda ya kamata na sani?”

    A yau, duniya ta canza sosai. Wayoyin hannu, kwamfutoci da Intanet sun zama tamkar abinci da ruwa a rayuwarmu. Muna amfani da su wajen neman ilimi, kasuwanci, nishaɗi, da kuma sadarwa. Amma akwai wani ɓangare da yawancin iyaye ba sa kula da shi sosai :tasirin Intanet a rayuwar yara da tarbiyyarsu.

    Yaro na iya koyon alheri daga Intanet, amma kuma zai iya faɗawa cikin sharri idan ba a ja hankalinsa ko an sa ido ba. Akwai bidiyo marasa kyau, shafukan da ba su dace ba, sada zumunta da ba a san waye a can ba, da kuma labaran ƙarya da ke iya lalata tunaninsu.

    Abin da ya fi sa damuwa shi ne: yara suna da saurin koyo da kwaikwayo fiye da yadda iyaye ke zato. Wannan yasa wajibi iyaye su ɗauki matakai na kare tarbiyyar ‘ya’yansu online. Ga wasu matakai guda 5 masu sauƙi amma muhimmanci da kowanne uba ko uwa zai iya bi:

    1. Kasance Abokin Hira ga Yaronka – Ka Jawo hankalinsa da tausayi da shaƙuwa: Idan ba ka buɗe ƙofa ta tattaunawa da yaranka ba, to za su nemo bayanai daga waje. Kuma ka sani, Intanet tana da miliyoyin “malamai” waɗanda da dama daga cikinsu marasa gaskiya ne.

    Ka saba hira da yaranka game da abin da suke kallo, wasannin da suke yi, ko abokanen da suke chatting da su. Kada ka fara da tsawa ko zargi, sai su fara ɓoye maka gaskiya. Ka tambaye su cikin sauƙin hali:

    “Wani abu ne ya fi burgeka a wannan wasan?”

    “Wane aboki ne ka fi jin daɗin hira da shi?”

    Da haka za ka gina aminci, shaƙuwa da gaskiya da yaronka. Yaro idan ya yarda da kai, zai faɗa maka duk wani abu da ya gani a Intanet wanda ya dame shi.

    2. Sanya Dokoki da Iyakoki – Ka Nuna Kai ne Jagora. Yara suna buƙatar kulawa da Shata musu iyaka. Idan ka bar su da ‘yanci marar tsari, za su iya faɗawa cikin hatsari.

    • Kafa lokaci: Ka ƙayyade lokacin da yaro zai yi amfani da waya/Intanet. Misali: awa 1-2 a rana bayan makaranta.
    • Haramta wurare: Kar a yarda da waya ko kwamfuta a ɗakin bacci. Sai dai a ɗakin iyaye ko parlour inda ake gani.
    • Ƙa’ida: Idan an karya doka, sai a ɗauki matakin ladabtarwa mai ma’ana (kamar rage lokacin waya ko ɗauke ta na wasu kwanaki).

    Wannan yana koya musu yanda za su yi amfani da fasaha ta hanyar da ya dace.

    3. Yi Amfani da Parental Controls – Fasaha ta Kariya: Yawancin wayoyi, kwamfutoci da apps suna da Parental Control Settings. Wannan yana ba ka damar:

    Taƙaita shafukan da yaro zai iya ziyarta.

    Sa ido kan abinda yake yi online.

    Kariya daga shafukan batsa, tashin hankali da labaran ƙarya.

    Idan kai ba ka da ilimi sosai a kan wannan, ka tambayi wanda ya ke da sani a kai. Ko ka kalli bidiyon koyarwa a YouTube. Ka tuna, kariya ba ta nufin hana ilimi, sai dai nufin tsare tarbiyya.

    4. Ka Ilimantar da yaronka kan yanda zai amfani da intanet ta hanyar da ya dace.

    Idan muka koya wa yara karatu da rubutu, me yasa ba za mu koya musu yadda ake amfani da Intanet lafiya ba musanman a wannan zamani da muke ciki?

    Ka koyar da su cewa:

    • Ba a amincewa da duk wani abu da ake gani a Intanet. Akwai labaran ƙarya da yawa.
    • Kada su taɓa bayar da sirrinsu (password, adireshi, lambar waya) ga wanda ba su sani ba.
    • Kada su taɓa amincewa su haɗu da mutum daga online ba tare da sanin iyaye ba.
    • Su riƙa tambayar ka kafin su sauke app ko shiga wani sabon shafi.

    Wannan shi ake kira Digital Literacy da Safety – kuma yana daga cikin manyan ilimin da yara har ma da manya ke buƙata a wannan zamani.

    5. Ka Taimaka Wajen Nemo Abubuwan Alheri da za su amfane su – Ka Nuna Musu Hanyoyin Ilimi. Maimakon kawai a hana yara shiga Intanet, ka nuna musu madadin haka mai alheri:

    • Ka sa su dinga duba darussa a YouTube na ilimi (misali: lissafi, kimiyya, addini).
    • Ka koya musu amfani da apps masu amfani na koyar ilimin addini da na zamani.
    • Ka nuna musu shafukan labarai masu inganci na Hausa/English.
    • Ka tallafa musu wajen amfani da Intanet don yin binciken makaranta.

    Da haka za ka canza Intanet daga hatsari ko gurbacewar yaro zuwa makaranta.

    A ƙarshe, Iyaye sai Kun Tashi Tsaye. Intanet ba za ta tsaya ba, kuma yara ba za su daina sha’awarta ba. Amma iyaye na da iko sosai wajen shiryawa da kare tarbiyyar ‘ya’yansu.

    Ka tuna da Hadisin Manzon Allah (SAW):

    “Dukanku makiyaya ne, kuma kowane makiyayi za a tambaye shi kan abin da ya kiyayye.”

    Iyaye, ku kasance makiyaya na gaskiya – ku kula da amana.

    Kada mu bari Intanet ta yi mana hijira daga tarbiyyar Musulunci da al’adun Hausa. Mu amfani da ita a matsayin makamin cigaba, ba makamin lalacewa ba. Tambaya ta iyaye ce:

    Me kuka lura da shi game da yaranku da Intanet? Kuna ganin matsalar da ta fi yawa ko kuwa tana da alkhair mai yawa, ko kuma lokaci kawai ake ɓatawa?

    Ku rubuta a comments domin mu tattauna tare.

    Danna nan don karanta Tarbiyyar Yara

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Maguzawa Suke A Taƙaice

    Yadda Maguzawa Suke A Taƙaice

    SHIMFIƊA
    Hoton rayuwar wata al’umma takan fito cikin ayyukan adabi wanda adabin Hausa bai keɓanta ba. Hakan na faruwa ne idan marubuci ya taɓa jin labari, ko gani, ko karanta wani aiki da ya shafi wannan al’umma. Wani lokaci kuma zamantakewa ke kawo nason rayuwar wasu al’ummomi na kusa ko na nesa cikin aikin adabi.

    Idan kuwa ba haka ba, hoton rayuwar da aka gani wadda marubuci ke bayani; yana yiwuwa jinin marubuci ne da ke da asali tun daga iyaye da kakanni. Kenan asalin marubuci yana iya tasiri cikin rubutu har a ga hoton rayuwar magabata ta kusa ko nesa na mai rubutu, ya sani ko bai sani ba.

    MAGUZAWA

    Maguzawa Hausawa ne na asali da ke zaune a ƙasar Hausa tun da daɗewa. Tarihin Hausa da Hausawa ba zai kammalu ba sai an ambaci Maguzawa domin ba su da wani harshe sai Hausa.

    HALAYYA DA ƊABI’UN MAGUZAWA

    Wayo: Wayo yana ɗaya daga cikin ɗabi’ar Maguzawa (Abdullahi, 2008:4). Ana iya gane wayon Bamaguje idan aka yi mu’amala da shi, ko aka ji labarin wani abu da ya faru tsakaninsa da wani. A labarin Ɗan hakin da ka raina na cikin littafin Magana Jari Ce na uku, an nuna cewa Maguzawa mutane ne masu wayo. Ga dai abin da Anunu Mahauci da abokansa suke cewa:

    Suka hanga, guda ya ce , Bahaushe ina? Kuna ganin Bamaguje, ku dubi irin kayan gogan mana, iya magana yanzu nan ko ɗan Kano. Daga nan sai guda wanda ake kira Anunu ya ce : “Haba wane wayo ke ga Arne, daga dai an ƙyale su”. Guda ya ce: A! don wayo dai suna da shi. A nan Anunu da abokansa sun tabbatar da cewa duk wani Bamaguje yana da wayo. To amma dai haɗuwarsu a wannan wuri an yi wa Bamaguje hikima an cuce shi.

    Shi kuwa marubucin littafin Malam Inkuntum, ya nuna wayon Maguzawa ne a wurin da ya ambaci wani Arne da ke neman bawan Allah wanda zai ba ɗiyarsa a matsayin miji. Arnen ya gwada wayonsa ga wasu musulmi da cewa:

    Arne:Kai! Bawan Allah ne kai in kashe ka maimakon nawa da ya kashe jiya.
    Ladan : Lallai ni kam bawan Allah ne. In ka kashe ni ka kashe bawan Allah.
    Arne: Kashe ka fa zan yi yanzu, ko ƙyaftawa babu.
    Ladan: Ai ta samu gare ka. Allah ya ba mu cikawa da imani, mu tashi da imani, amin.
    Arne: (ya mai da gatarinsa a kafaɗa, ya kama hannun Ladan ) Zo mu je gidana , kuma kwantad da zuciyarka, ba kashe ka zan yi ba.

    Wannan misali ya nuna wayon da Arne ya yi amfani da shi domin ya tantance wanda zai ba ɗiyarsa aure. A ɓangaren su Anunu da Bamaguje kuwa, cutar da Anunu ya yi wa Bamaguje ya rama ta hanyar ɓad da kama kamar haka:

    To Bamagujen nan ya yi kamar ya ƙyale, sai da ya bari an yi kamar kwana ashirin har an bar wannan Magana, sai ran nan ya sami kayayyaki farare irin na Hausawa ya sa, ya nemi rawani ya bayar aka naɗa masa. Bamaguje ya nufi wajen Anunu ya tarad da shi da kan akuya yana sayarwa. Da zuwansa sai ya dafa kan Anunu, ya dubi kan akuya ya ce: “wannnan kan nawa ne?” Anunu ya ciro ido ya dube shi ya ce: “ Mene ne kuma na dafa mini kai? Ku dai Malamai kun raina mu..To ga shi nan faɗi abin da za ka biya.

    Nan ma wayo Bamaguje ya yi wa Anunu domin ya dafa kansa a matsayin kan akuyar da ake ciniki. A ƙarshen wannan ciniki dai sai da aka dangana da gaban alƙali. Ko da alƙali ya ji duk yadda aka yi tun lokacin da Anunu ya sayi San Bamaguje har ya zuwa cinikin kan akuya, ya san cewa, Bamaguje ya rama abin da aka yi masa ne. Ga shi kuma Bamaguje ke da gaskiya, don haka a ƙarshe dai Anunu ya yi hasara fiye da wadda Bamaguje ya yi lokacin da aka sayi Sansa.

    MUHALLIN MAGUZAWA

    A duk inda Maguzawa suke, sun fi son su zauna cikin daji, wato nesa da gari ba tare da mutane sun tsangwame su ba. Wannan ya sa suka ba noma muhimmanci a rayuwarsu fiye da duk wata sana’a. Cikin littafin ƙarshen Alewa Ƙasa marubucin ya yi bayanin muhallin Maguzawan Tsaunin Gwano da cewar:

    Wannan gari na Tsaunin Gwano yana da gidaje kamar guda ɗari biyu. A gefen garin akwai wani dogon tsauni wanda ta wajen ne garin ya sami suna. A da can ‘yan shekaru kaɗan da suka wuce dukkansu suna zaune a kan tsaunin nan ne. Wannan kuwa ya faru ne saboda tsoron masu harin bayi suna sayarwa. Nan ma nuni ne da muhallin Maguzawa tun lokacin da suke a saman duwatsu, har ya zuwa saukowarsu daga duwatsu, kuma a cikin daji.

    SANA’O’IN MAGUZAWA

    -Noma
    -Ƙira
    -Farauta

    NOMA

    Sana’ar da ta fi kowace muhimmanci wajen Maguzawa ita ce noma. Ita suka gada kaka da kakanni, da ita suke alfahari fiye da komi a duniya, (Abdullahi 2008). Ya ƙara da nuna baya ga noma Maguzawa suna da wasu sana’o’i irin su: ƙira, da farauta, da kiwo. Hoton sana’o’in waɗannan mutane sun fito cikin littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa inda marubucin yake bayanin yekuwar farautar shekara da za a yi kamar haka :

    “Hyai, hyai! Ina mazajen Tsaunin Gwano, Sarkin Ƙira ya gaishe ku. Bayan gaisuwa ya ce a faɗa maku lokaci ya yi wanda duk mai ji da kanshi ya shirya….” Wani Saurayi wanda ake kira Mailoma yana zaune a kan wani buzu da aka yi da fatar biri ya miƙo hannu suka tafa. Sai ya yi wuf ya miƙe gaban hantsi yana gyaran lagen gwadonsa.

    Ya ce bara kuwa an yi farauta da sa’a. Ka tuna lokacin da muka darkaki ƙatuwar Barewar nan? Shi wannan ɗan tsoho sunansa Ci-wake. Duk garin Tsaunin Gwano da kewaye an san shi da yin jima. Wannan sana’a da yake yi ta sa a kullum ba ya rasa abin yin kayan miya.

    Waɗannan misalai sun kawo hoton sana’o’in Maguzawa da suka ƙunshi farauta, da jima. To amma ba waɗannan sana’o’in ba ne muhimman sana’arsu ba kamar yadda ya zo cikin littafin , noma shi ne babbar sana’arsu.

    Shi kuwa labarin Ɗan Hakin da ka Raina na cikin Magana Jari Ce ya nuna cewa noma da kiwo suna daga cikin sana’o’in Maguzawa. Farkon labarin ya fara ne da bayanin sana’ar Maguzawa kamar haka: Wata rana wani Bamaguje ya lafta wa takarkarinsa hatsi, ya kora zai kai kasuwa. Kasuwar da za shi kuwa ana ɗam mudu ƙwarai, don kullum in ya kai kayan takarkarin nan, daga ya sayar sule talatin sai ya sayar talatin da biyar.

    Haka ma a cikin littafin Malam Inkuntum, lokacin da Arne ya je neman bawan Allah, ya nuna cewa shi manomi ne inda ya ce:
    Arne:Kai tsaya tambayarka zan yi. Akwai mutane cikin akurkin nan naku?
    Malam Almu: Ai tukuna. Yanzu dai muke harama. Anjima kaɗan za a taru. Sallar za ka yi yau?
    Arne: Tir! Me ya kai ni wannan abin duƙe-duƙe ba wurin noma ba.
    Wannan Arne ya nuna babu wani abu da zai sa ya dinga wasu duƙe-duƙe in dai ba wurin noma ba. A ganinsa wurin noma ake yin duƙe-duƙe a nasa tunanin.

    SUNAYEN MAGUZAWA

    Suna shi ne kalmar da ake amfani da ita wajen kira ko ambato ko wani abu, (Ƙamusun Hausa 2006:401). Akwai abubuwa da dama da kan ba da haske wajen sa wa yaro ko yarinyar da aka haifa suna.

    Cikin irin waɗannan abubuwa akwai: yanayi, da halin haihuwa, da yanayin haihuwa, da siffar mutum , (Yahaya 1979:5-8). A wasu lokuta kuma, akan sa sunan wata dabbar daji ko ta ruwa a matsayin suna ga Maguzawa. Wasu daga cikin sunayen gargajiya da aka yi amfani da su cikin waɗannan littattafai guda uku su ne :

    Arne: Wanda ke yin tsafi, kuma ana kiran Maguzawa da wannan suna.
    Bamaguje: Suna ne na namiji tilo mai bin addinin gargajiya na Hausa.
    Dubu: Wadda aka haifa lokacin da ake yin bikin dubu da tambarci.
    Hantsi: Yaron da aka haifa lokacin da rana ta fito kafin ta kai tsakiya
    Juda: Suna ne na wata dabbar daji mai kama da Mage. Ana samun turare daga wasu sassa na wannan dabba.

    Maguzawa: Jam’i ne na kalmar Bamaguje
    Malka: Ita ce Yarinyar da aka haifa lokacin da ruwan damina ya kai tsakiya.
    Sarkin Arna: Shugaban Maguzawa kuma mai jagorancin bautar gargajiya.
    Sarkin Dodanni: Abin bautar gargajiya ne.
    Sarkin Noma: Mai yin jagoranci wajen harkokin noma.
    Sarkin Tsafi: Mai yin jagoranci wajen tsafi.
    Tayani: Sunan abin zama ne wanda aka saƙa da kaba tare da fatu, mata suke kaɗi kansa.
    Tamu: Suna ne da ake sa wa yaron da aka haifa shekarar da gyaɗa ba ta yi kyau ba.

    MAGUZANCI

    Maguzanci a Wasu Rubutattun Littattafan Adabin Hausa:
    Imani da tunanin Maguzawa na gargajiya shi ke jagoranci wajen tafiyar da harkokin rauwarsu. Wannan shi ne abin da ya bambanta Maguzawa da sauran ‘yan’uwansu Hausawa. Wannan fasali ya dubi wasu ɓangarori cikin imani da tunanin Maguzawa a gargajiyance da suka haɗa da bautar gargajiya, da cin mushe da sharholiya, da zagi da batsa da dai sauransu.

    Bautar Gargajiya:

    Bauta da abin bauta a wajen Maguzawa suna da muhimmancin gaske, don haka suke kiyayewa da mutunta duk wani abu da ya shafe su. A tsarin bautar Maguzawa, akwai abin da ake yi wa bauta, da wurin bauta, da hidima ga abin bauta, da kiyaye dokokin abin bauta, da kuma sakamakon da ake samu ida an saɓa ma abin bauta.

    Abin Bauta:

    Addinin Maguzawa addini ne na gargajiya ne da suka gada wajen iyaye da kakanni. Hanyoyin bautar Maguzawa su ne tsafi, da bori, da mu’amala da dodo. Abubuwan da suke bauta ma kuwa su ne Aljanu, da Dodanni, da wata dabba da sukan keɓe, ko wani itace. Aljanu su ne abubuwan da suka fito a matsayin abin bauta cikin wannan aiki.

    Misali, a rigimar Bamaguje da Anunu Bamagujen na cewa:
    Da ni dai na fi son kan da kome , don in kai wa gunkinmu ya sha jini.
    Bayanin wannan Bamaguje ya nuna cewar gunki yake bauta ma, amma ba gunkin ba ne aljani yake nufi domin gunki ba ya shan jini. Shi kuwa littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa Aljani ne aka ambata a matsayin abin da suke yi wa bauta.

    Kodayake an ce yakan fito cikin siffar maciji ko wani abin daban, amma dai Aljani ne. An bayyana shi da cewa:
    Wannan surin yana ƙarƙashin wata babbar tsamiya ce …… Sarkin Arna da jama’arsa Talakawa sun yarda cewa wai a cikin wannan surin akwai wani tsohon Aljani. Shi wannan Aljani an san shi a cikin siffar maciji, ko da yake an ce kuma ba abin da ba ya rikiɗa.
    Shi ma wannan ya nuna babu tsayayyar sifar da abin bautar yake da ita, sai dai a iya cewa ya fi bayyana cikin sifar maciji.

    Ana iya samun jinsin mata cikin aljanun da ake yi wa bauta kamar yadda Arnen cikin littafin Malam Inkuntum ya ce:
    Ladan: Na ji na yarda, amma ina so a ɗaura aure.
    Arne: Ku yi can ruwa ga wuya, in ji mata. Ai ni tun da Uwar Dawa (aljana) ta yi mini izini, iyakar nawa ke nan. (arne ya koma gida).

    Wurin Bauta:

    Maguzawa ba kamar sauran mutane ba, sukan keɓe wani wuri na musamman domin yin bauta. Duk wurin da suka keɓe suna yin bauta nan ne mazaunin da abin bautar tasu yake. Suna kula da wurin fiye da makwancinsu ta fuskar tsaftacewa, da ba wurin kariyar da ta dace musamman ga wanda bai san darajar wurin ba. Irin wannan wuri na iya kasancewa ɗaki a cikin gida, ko bishiya a ƙofar gida ko bayan gari.

    Misali cikin littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa an ambaci wurin bauta da cewa:
    Ita fadar Sarkin Dodanni wani irin wuri ne inda yake da wani irin babban shuri wanda girmansa ya kai tsawon mutum uku dogaye. Wannan shurin yana ƙarƙashin wata babbar tsamiya ce, kuma a kowace rana Sarkin Arna yakan sanya yaran shi su share wurin nan fes. Lallai wannan wuri ya amsa sunansa wurin bautar gargajiya na Maguzawa kasancewarsa bayan gari, kuma ga shuri jikin bishiyar tsamiya. Wanda ake sharewa a duk safiya.

    Hidima ga Abin Bauta:

    A tsarin bautar gargajiya ana yin hidima ga abin da ake yi ma bauta. Hidimar da ake yi ta haɗa da tsaftace wurin, da yin yanka ga abin bauta, da sagale ƙasusuwan dabbar da aka farauto, da yin kyautar mutum ko dabba ga abin bauta. Cikin labarin Bamaguje da Anunu na Magana Jari Ce , an nuna inda Bamaguje ya so a bari ya yanki Anunu domin Gunkinsu ya sha jini. Bamagujen na cewa: Da ni dai na fi son kan da kome, don in kai wa gunkinmu ya sha jini.

    A littafi Ƙarshen Alewa Ƙasa kuwa, an yi bayanin hidimar da ake yi wa abin bauta kamar haka: A kowace shekara Sarkin Arna yakan zo ya yi sujada, kuma ya kawo wa Sarkin Dodanni ‘yar gaisuwarsu. Irin gaisuwar da Sarkin Arna ke kawo wa tana da nauyi ƙwarai. Wato kyautar da ake yi ita ce rai guda na mutum. Ita ma wannan hidima masu gudanar da bautar sun gaje ta ne tun iyaye da kakanni ba sai cikin wani labari ba.

    A wajen wasu Maguzawan kuwa, ba sa bayar da ran mutum sai na dabba. Bayanin Maguzawan garin Jinjin Wawa na cikin Ƙarshen Alewa Ƙasa ya tabbatar da haka:
    Jinjin Wawa wani gari ne wanda shi ma girmansa kamar na Tsaunin Gwano yake. Suna da Sarkinsu na tsafi, to amma shi ba a ba shi ran mutum sai na dabba.

    Sakamakon Saɓa Ma Abin Bauta:

    A duk lokacin da ake gudanar da bauta a Maguzance, ya zama wajibi a kiyaye tare da mutunta wannan abin bauta. Idan ba haka ba za a ga sakamako wanda ba daɗi. A lokacin da Mailoma ya yi karambanin zuwa fadar Sarkin dodanni ya aikata abin da ba a yi kamar haka:

    Da yake wannan yaro ba ya cikin hankalinsa, ko tufafinsa bai tuɓe ba. Da ya ji tarin ya ƙi tsakaitawa sai ya tura ɗan yatsa a maƙogwaro ya yiwo aman giya a kan shurin nan. Yace ma shuri, “sha mana” Ya sake kecewa da dariya. Wannan rashin kunya da Mailoma ya aikata ga Sarkin Dodanni na daga cikin abin da ba a yi a wurin tsafinsu. Yin haka kuwa kan haifar da mummunan sakamako ga wanda ya aikata.

    A dalilin wannan rashin kunya da Mailoma ya yi, wasu abubuwa sun faru da shi kamar haka: Ai wannan babu shakka cizon maciji ne, don kuwa ga alamar ɗan jini da kuma shaidar haƙora. Maciji? Aha ga amsa a fili. Nan take ya fusata ya yi ruri cikin dajin nan yana kira, MACIJI. MACIJI! SARKI. SARKI! Kai ne ka cinye Tayani.

    Zagi Da Batsa:

    Zagi shi ne faɗa wa mutum baƙar magana ko bacin iyayensa, (Ƙamusun Hausa 2006: 487). Zagi wani ɓangare ne cikin lafuzzan ɗaurin auren Maguzawa wanda a wasu lokuta yake zuwa surke da batsa. Maguzawa suna sanya zagi cikin lafuzzan ɗaurin aure domin wanda yake da niyyar ƙalubalantar ɗaurin aure idan ya tuna girman zagin, da kallon da jama’a za su yi masa ya fasa, (Abdullahi 2008: 5-7).

    Ko ba wurin ɗaurin aure ba Maguzawa sukan yi ashar cikin magana ta yau da kullum, ko da kuwa zagin surke yake da batsa. A irin wannan yanayi, ba sa jin nauyi ko kunyar wani don sun yi irin waɗannan kalamai. Misali an sami zagi cikin litttafin Ƙarshen Alewa Ƙasa a yayin da Mailoma yake yin kirari kamar haka:

    “Ni ne na bara ni ne na bana
    Mijin Tayani dogon yaro
    Samun irinku sai an tona
    Yaro ko kana musu in ci ubansa”.

    Haka kuma Mailoma ya sakeƙunduma wani ashar ɗin lokacin da matarsa ta sheda masa tana da juna biyu inda ya ce:
    “ Sai ni Arne tsaran manya na Chiwake da Tayani.
    Yaro ko kana shakka ne yanzu in ci ƙundun durin uwarka .

    Batsa ita ce maganar banza musamman wadda ta danganci ambaton al’aurar mace ko namiji. Ga Bamaguje, batsa ta zama jiki, domin tana cikin lafuzzan ɗaurin aurensu. A maganganun yau da kullum, al’ummar Maguzawa ba sa jin kunyar yin batsa. Haka ma a littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa batsa ta fito a wannan wurin kamar haka:
    Dutsen niƙa: Kakir-kakir
    Malka: “Ba ruwan ka da yaron kowa”
    Malka ta sake maimaitawa.
    “Ba ruwan ka da yaron kowa
    To, zagayo ka ci gutsu,
    A hankali ba da garaje ba”.

    Batsar da ke cikin wannan zance na Malka tana ƙunshe da kalmomi waɗanda idan ba Bamaguje ba, babu wanda ke iya faɗi ba tare da jin kunya ba. Dalili kuwa, an ambaci al’aurar mace ba tare da jin kunya ba.

    ABINCIN MAGUZAWA

    Cin Mushe:
    Hausawa na cewa: “kyawun Bamaguje ya ci mushe”. Mushe shi ne naman wata dabba ko tsuntsu da ya mutu ba tare da an yanka ba. A wurin Maguzawa dabba ko tsuntsu da ya yi mushe nama ne mai kyau. Wasu Maguzawa da aka kira da sunan Filani cikin littafin
    Malam Inkuntum, an nuna cewa sun ci mushen Biri a cikin daji kafin su iso gari.

    Marubucin na cewa:
    Ana ta rawa da waƙa sai ga waɗansu Filani su uku sun fito daga cikin daji. Ashe sa’ad da suke can daji yunwa ta kama su har sun tarad da gawar bika sun gasa namansa sun ci. Sun yi wa juna alƙawarin ba wanda zai faɗi wannan magana har abada. Ko kafin su iso nan ƙishirwa ta kama su ƙwarai da gaske. Sai kuma suka ji durin kiɗa ake yi, suka tona asirinsu.

    Bafillace na Farko: Ho ɗan kare da ba da ƙishirwa
    Bafillace na Biyu: Hala kana so ka faɗi.
    Bafillace na Uku: He, ku faɗi, mun ci biri, mun ci biri, mun ci biri.

    Shan giya

    Sharholiya ita ce yin abubuwa na jin daɗin rayuwa da nufin more rayuwa da shaƙatawa. Abubuwan sharholiya ga Bamaguje su ne shan giya, da wasanni, da auren mata da yawa, da yin bukukuwa, da sha’awar doki, (Abdullahi 2008:5) Daga cikin waɗannan ɗabi’un, giya ita ce ta mamaye littafin Ƙarshen Alewa Ƙasa. A farkon littafin an fara zancen giya lokacin da ake sanarwa domin gayyatar farauta da cewa:

    Hantsi ya ajiye ƙoƙon da ya gama shan burkutu da shi, ya yi wata doguwar miƙa ya yi murmushi. Hantsi ya ƙara ciko ƙoƙonsa da giya ya ce: A wannan rana duk tsawon rai na ba zan iya mantawa da ita ba. Lallai da ban sa baki ba da ai da kun yi ɗanyen aiki, ya miƙo masa giya cikin ƙoƙo, Mailoma ya karɓa.

    Ko da yake yin wannan sanarwa, waɗannan samari suna cikin sharholiyarsu ne da giya. Wannan ya nuna cewa rayuwa ba ta gudana wurin Maguzawa sai da giya, kuma wa da ƙani suna iya haɗuwa su sha ba tare da sun ji komi ba. A lokacin da Mailoma ya je yi ma Juda gaisuwar ɗansa, an nuna cewa ko a nan sai da ya sha giya ya yi tatul har aka ba shi wadda ya yi guziri da ita. Juda ya fara bayani da cewa:

    Ku kawo masa giya nan, hankalin yaron nan ya tashi.” Ku yi sauri mana ku zubo, ka bar kukan nan.” Bayan an zubo giya a ƙoƙo sai aka miƙa wa Mailoma don ya sha. Ya karba.
    Bayan da Mailoma ya ƙare zaman gaisuwa, sai ya yi sallama da jama’a ya nufi ƙauyensu. Ko da yake dai shi ya yi sallama da mutane, amma a gaskiya bai san lokacin da ya yi ba.

    Giyar da ya ɗirka da kuma naman da ya ci duk sun yi masa babakere a ciki. Ga shi saboda buguwar da ya yi har da ƙyar yake iya takawa. Kuma tun lokacin da ya zauna gindin su Manje mai kukuma yake ɗaukar ƙoƙo bisa ƙoƙo na burkutu, wanda ma ba ya ko ɗan saurarawa domin ya huta. Ya tinkaro hanyar Tsaunin Gwano da wani goran giya mai girma a hannunsa.

    Wannan kyauta ce wadda Juda ya yi masa saboda ba a samu wani wanda ya kama ƙafansa wajen shan giya ba. Kusan kowane lungu da saƙo na rayuwar Maguzawa, giya ba ta rasa gurbi. Idan kuwa babu wata hidima, to haka nan ma sukan sha domin annashuwa.

    NAƊEWA

    Haƙiƙa adabi ba ƙaramin tanadi ya yi wa rayuwar Maguzawa ba, ya kuma haskaka mana rayuwar Maguzawa. Kenan hoton Maguzawa da Maguzanci cikin wasu littattafan adabi, rayuwa ce ta wata al’umma da wasu marubuta suka ƙyallaro cikin fasaharsu a rubuce.

    MANAZARTA

    Abdullahi, I.S.S. 2008. Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa. Kundin Digiri Na Uku. Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato..
    Abdullahi, I.S.S 2008. “Bamaguje da Ɗan Akuya: Rashin Ƙauna Ko Ƙiyayya?” Departmental Seminar Series, Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.
    Abdullahi, I.S.S 2012. “Falsafar Ɗaurin Auren Maguzawa”. Muƙalar da Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani a Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

    Karanta Gudunmawar Ali Gumzak Wajen Samarwa Da Kuma Haɓaka Finafinan Hausa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Gudunmawar Ali Gumzak Wajen Samarwa Da Kuma Haɓaka Finafinan Hausa

    Gudunmawar Ali Gumzak Wajen Samarwa Da Kuma Haɓaka Finafinan Hausa

    NAZARIN WASU DAGA CIKIN FINAFINANSA

    DAGA
    FATIMA ADAM ISAH
    adamisahfatima@gmail.com
    07015974659
    DA
    MUHAMMAD SAHAL ALIYU
    Sahalaliyu@gmail.com
    07065994177
    ƊALIBA A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA DA KIMIYYAR HARSHE,
    JAMI’AR JIHAR KADUNA, KADUNA

    Maƙalar Da Aka Gabatar A Taron ƙara Wa Juna Sani Na ƙasa Da ƙasa Karo Na Biyar Mai Taken ‘Hausa Playwrights And Dramatists As Agents Of National Integration And Development’ In Commemoration Of Late Playwright, Alhaji Yusuf Ladan, Ɗan Iyan Zazzau, 2th-4th Dec 2021. Wanda Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Harshe Jami’ar Jihar Kaduna Ta Shirya.

    DECEMBER, 2021.

    Tsakure
    Tun samuwar fina-finan Hausa a shekarun baya, harkar ta sami bunƙasa da haɓaka sosai wanda hakan ba ya rasa nasaba da yadda matasa da ‘yan kasuwa suka shigo cikin harkar shirya finafinai. Waɗannan fina-finai na Hausa idan aka masu fyaɗar kaɗanya, za a ga yawancin saƙonnin da ke ƙunshe a cikinsu ba ya wuce soyayya da matsalolin zamantakewar aure.

    Don haka ne ma wannan muƙalar za ta mayar da hankali a kan ɗaya daga cikin jigogi a harkar shirya fina-finan Hausa da ba da umurni wato Ali Gumzak tare da nazarin gudummuwarsa wurin samar da kuma haɓaka fina-finan Hausa. Daga ƙarshe, za a yi nazarin gundarin soƙonni da ke ƙunshe a wasu fina-finansa guda uku wato Burin Fatima da Izzatu da kuma Ƙawaye.

    Gabatarwa

    Ko shakka babu, finafinan Hausa ɓangare ne na adabi kuma fasaha ce ta al’umma da ke nuni da yanayi da tsarin rayuwar al’umma. Ta hanyar fina-finan Hausa za a iya ganin hoton rayuwar wata al’ummar da ta gabata, haka kuma za a iya fahimtar tsarin rayuwar waɗannan mutane da ɗabi’unsu da tattalin arziki da zamantakewarsu.

    Za a iya ganin hoton abin da ke faruwa a cikin al’umma, har ma wani lokaci a iya kirdaden abin da zai iya faruwa a cikin al’umma. Finafinan Hausa hanya ce ta bayyana tunanin mai shirya fim ɗin, ko marubuci, ko kuma irin falsafarsa game da rayuwa.

    Taƙaittaccen Tarihin Samuwar Fina-finan Hausa

    Fim abu ne mai gajeran tarihi idan aka kwatanta shi da sauran ɓangarori na adabin zamani. Misali waƙa da rubutun zube waɗanda tuni suka ci gaba ta fuskar nazari da aikace-aikacen masana da manazarta masu rubuta kundayen bincike don neman digiri na farko zuwa na uku.

    A wajen Hausawa wasan kwaikwayo shi ne tushen samuwar fina-finan bidiyo domin shi aka fara aiwatarwa a dandali kafin a samu na’urar ɗaukar hoto ta majigi wadda daga baya kuma aka sami gidajen talabijin da na’urar bidiyo da ake amfani da ita a yanzun.
    Dangane da wasannin kwaikwayon majigi, sun fara samuwa ne a wajen 1950 lokacin da ma’aikatar yada labarai ta Arewa (Ministry of Information Northern Nigeria) take ƙoƙarin wayar da kan ‘yan Arewa dangane da harkokin noma da wayar da kan su al’amuran da suka danganci rayuwar yau da kullum.

    To sai ma’aikatar ta zaɓi ta yi amfani da wasan kwaikwayon majigi domin shi ne hanya mafi sauƙi da za a jawo hankalin ‘yan Arewa a kan su noma abubuwan da gwamnati take buƙatar da su a kan yadda da wannan noma ta hanyar amfani da hanyoyin zamani. To gwamnatin wannan lokacin ta yi amfani da wasan kwaikwayon majigi domin gudanar ta hanyar amfani da mota wadda take ɗauke da na’urorin nuna majigi wato “Projector”.

    Ana amfani da wannan mota ne ta bin birane da ƙauyuka domin nuna wasannin domin ilimantar da su a wannan ɓangare na noma da kuma ɗebe masu ƙewa. Dangane da fim wanda aka fara aiwatarwa a harshen Hausa kuwa shi ne Baban Larai Mai Auduga a cewar Abdulkadir (1998:24) wanda aka aiwatar a shekarar 1948.

    Daga nan sai Ɗan Arewa a London, sai kuma fim ɗin Shaihu Umar a shekarar 1976 da sauran ɗimbin fina-finan da aka samar a wannan lokacin, sai dai akwai fina-finan masu yawa da wasu mutane ko jihohi suka shirya, to amma ba su zo ga jama’a ba saboda wasu dalilai.

    Akwai kuma fina-finan da tashoshin gidajen talabijin na ƙasa da suke jihohin Arewa suka gudanar don nuna wa jama’a. Misali Golobo daga Sakkwato da Karkuzu na Bodara daga Kano. Dukkan waɗannan shirye-shirye na NTA da suke a waɗannan jahohi. Har ila yau, kuma akwai Bakan-Gizo da Hadarin Kasa sa Hankaka na CTV 67 Kano (Gidan Dabino da Wani), a cikin Adamu da wasu, (2004:342).

    Fim na farko da ma’aikatar yaɗa labarai ta Arewa ta fara nuna wa jama’a sun haɗa da fim ɗin Baban Larai da Dan Arewa a London da Shaihu Umar da Kulɓa na Ɓarna da sauransu. Nuna fim babu ko shakka hanya ce mafi inganci ta yada al’ada. Ta wannan hanya ce al’adun ƙasar Indiya da Sin da Amurka su ka zo Nijeriya har ma wasunsu suka samu karɓuwa, aka kwaikwaiye su.

    Binciken da aka gudanar a 1970, a Arewa akwai gidajen silima ɗari huɗu(400) wato a cikin birnin Kano kawai, akwai guda shida (6) kuma kowannen su za su iya ɗaukar mutane fiye da dubu biyu(2000) a lokaci ɗaya. Sa’anan kuma akwai gidajen silima da dama a sauran ƙasashen Arewa, amma duk cikin su babu na ‘yan ƙasa, ƙwarori ne (Lebanese) ke da su. Saboda haka mutanen Arewa, ba su da zaɓin fim ɗin da za a nuna masu.

    Dangane da wannan dalilin, shi ya sa mutane suka shaƙu da kallon fina-finan Indiya, ga kaɗe-kaɗe da raye-raye. Ba abin mamaki ba ne a ƙasar Hausa ka ga wani magidanci na rera waƙar Indiya lokacin da yake nishaɗi ko kuma lokacin da yake gudanar da wani aiki. Su ma mata ba a bar su a baya ba, lokacin Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna a 1974, lokacin da fito da wani fili na kaɗe-kaɗen Indiya da ake sawa, ba mamaki ka ji ana kiran mace Bahaushiya da sunan Hema ko Rani da dai sauran sunayen taurarin da suka yi fice a fina-finan Indiya.

    Kaunar da Hausawa ke wa labaran soyayya, shi yasa CTV 67 ke nuna wasu wasanni guda biyu wato Bakan Gizo da Hadarin Sama waɗanda suka sami nasara. An gina labaran ne kan soyayya irin ta Indiya (Salihu,2002).

    Bunƙasar Fina-Finan Hausa

    Sun fara samuwa ne tun kafin ‘yancin Nijeriya musamman bayan kammala yaƙin duniya na biyu. A wannan lokaci tattalin arziƙin Turai ya yi rauni ƙwarai tun ma ba na Ingila ba. Saboda haka ne Turawan mulkin mallaka suka taru don tattauna hanyoyi da za su fitar da ƙasashensu daga wannan ƙangi, inda suka shirya cewa a samu kaya da suka sarrafa a kasuwa.

    Nan take aka yanke shawarar cewa ƙasshen da ake wa mulkin mallaka ne za a iya matsawa su noma abubuwa da za a kawo nan ƙasar Ingila irin su gyaɗa da auduga maimakon kayan abinci, sa’annan kuma a yi wa jama’a farfaganda domin su yi amfani da kayayyakin da aka ƙera a ƙasashen wajen. Ta irin wannan hanyar ce sai su jama’a suka kashe kuɗaɗen da suka samu ta sayan kayayyaki daga waje.

    Me ya kamata a yi don a tura wa mutane wannan hanyar kashe kuɗi? Sai aka yanke shawarar yin fina-finai da Hausa domin ‘yan Arewa. Nan ne aka fi samun manoma sai aka shirya fim ɗin Baban Larai. Wanda aka nuna wani hamshaƙin manomi ne da ya bunƙasa wajen noman gyaɗa da auduga.

    Bayan samun ‘yancin kai an yi fina-finai don nuna muhimmancin haɗa kan ƙasa, da samun ‘yancin kai, da yadda ake gudanar da zaɓe. Haka kuma an yi fina-finai irin na Sir Ahmadu Bello da sauran mashahuran mutane da Jam’iyyar NEPU da NCNC mafi yawan waɗannan fina-finan Hukumar Talabijin ta Amurka ce ta yi su, inda aka yi fim mai suna Ɗan Arewa a Landon inda aka nuna Dr. Ibrahim Tahir a matsayin tauraro. An nuna yadda ɗan Arewa ya kamata ya gudanar da rayuwarsa a Landon.

    An fara yin fina-finan Hausa a 1960 lokacin da Adamu Halilu ya shirya fim ɗin Shehu Umar wanda aka gina kan littafin nan na Shehu Umar na Abubakar Tafawa Ɓalewa. Fim ɗin ya sami gagarumar nasara saboda abu biyu. Na ɗaya, ita ce a lokacin babu fim na Hausa tsantsa sai shi, na biyu kuma shi ne jigon labarin mai tsuma jiki ne wato soyayyar uwa zuwa ga ɗanta.

    A lokacin da aka nuna fim ɗin a silima ta ‘Plaza’ a Kano a 1976, duk wanda yake ganin ya shahara wajen zuwa silima ya je kallo. Bayan waɗannan fina-finai an yi waɗansu fina-finan da suke magana kan al’adun gargajiya na Hausawa waɗanda suka haɗa da “Auren Hausawa” da “Kano Heritage” da “Hawan Sallah” dukkansu na Alhaji Yahaya Imam.

    Dangane da bunƙasar fina-finan Hausa kuwa (Salihu, 2011) ya ce za a iya cewa sun yi tashin gwauron zabi ta yadda suka kai ga wani matsayi da za a iya kwatantawa da matsayin sana’ar kwatantawa da matsayin sana’ar acaɓa a ƙasar Hausa.

    Daga shekarar 1990 lokacin da aka fara gudanar da fim ɗin bidiyo na sayarwa zuwa yanzu an sami kamfanoni fiye da 121 da suka yi rijista da ƙungiyar masu shirya fina-finai ta Jihar Kano, ban da waɗanda kuma suke gudanar da harkokinsu a ɓoye, sannan daga wannan lokaci zuwa yanzu an samar da fina-finan Hausa sama da guda dubu (1000).

    Muhimmancin Fina-Finan Hausa

    Fina-finan Hausa abubuwa ne masu matuƙar muhimmancin gaske ga al’ummar Hausawa, musamman domin ilmantarwa da faɗakarwa da ke tattare da irin waɗannan fina-finan. Maƙasudin shirya fim shi ne domin wayar da kai ko kuma maganin wata matsala da take tattare ga al’umma, wato ta yi wa al’umma dabaibayi. Ta harkar fim ake nuna wa jama’a wata matsala mai wuyar warkewa kuma a warwareta domin nuna wa jama’a ta yadda za su kuɓuta duk lokacin da suka ci karo da irin wannan matsala.

    Kuma ana shirya fim a kan kowace matsala ta rayuwa domin warware ta ko maganinta.
    Fim hanya ce ta faɗakar da al’umma, wato ana amfani da fim don ilimantar da mutane a kan wani abu da ya shige musu duhu ko kuma wani abu da ake so su yi ko su ɗauka.

    Misali, idan gwamnati tana so ta faɗakar da jama’a bisa ga muhimmancin ilimi za ta sa a shirya fim wanda wani ya shiga makaranta har ya gama ya samu aiki ya zama wani a al’umma ta yadda mutane za su kwaikwayi wannan mutum. Akwai fina-finan da aka shirya domin ilimantarwa waɗanda suka haɗa da Jahilci Ya Fi Hauka da Wuyar Magani Zato wanda yake ilimantarwa a kan yawan zage-zage da ke faruwa a ƙauyuka musamman a kan maganar maita da sauransu.

    TAKAITACCEN TARIHIN ALI GUMZAK

    An haifi Ali Gumzak a shekarar alif ɗari tara da saba’in da tara (1979), a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano. Asalin sunansa Aliyu Ibrahim Khalil. Ya yi karatun firamare a makarantar Makama Primary School, sannan ya yi karatun sakandire a wata makaranta da ake kira “Gwale Secondary School, sannan daga bisani ya tafi School of Management Studies, inda ya karanci Financial.

    A hirar da aka yi da shi, ya bayyana cewa abun da ya jawo shi shiga harkar fim shi ne sha’awa da kuma sana’a. Ya fara harkar fina-finai a shekarar dubu biyu da sha ɗaya inda ya shirya fim ɗinsa na farko mai suna Salma Hayat. Fim ne da ya ja hankalin mutane sosai saboda saƙon da yake cikin sa.

    Salma Hayat fim ne da aka yi shi domin jan kunne ko gargaɗi ga ‘yan mata masu wulaƙanta samari. Ali Gumzak ya ce ba zai iya tuna adadin fina-finan sa ba sai dai a ƙalla za su kai hamsin (50) ko fiye da hakan a halin yanzun’. Misalan wasu daga cikin wannan fina-finan sun haɗa da:

    1.Salma Hayat
    2.Baban Sadiq
    3.Manyan Gobe
    4.Sultan
    5.Zango
    6.Dawo Dawo
    7.Burin Fatima
    8.Jaruma
    9.Ka yi na yi
    10.Aliya
    11.Wata Ruga

    12.Ruma
    13.Meera
    14.Wasiya
    15.Haidar
    16.Maƙota
    17.Ƙawaye
    18.Sai da ke zan rayu
    19.Manyan Mata
    20.Ga Duhu Ga Haske
    21.Rumfar Shehu
    22.Karangiya

    DALILIN SAMUWAR SUNAN GUMZAK

    Ya samu wannan suna na Gumzak ne sanadiyar wani aiki da ya yi a ƙarkashin kamfanin wani mutum mai suna Hamza, Hamza ya haɗa sunan garin Mahaifinsa wato (Gumel) da kuma sunan garin Mahaifiyarsa (Zakirai) shi ne ya samar da Gumzak. Sanadiyar ficen da ya yi a wannan kamfanin ne ya sa ake kiran shi da wannan sunan.

    Ali Gumzak ya kara da cewa ba shi da wata gaɓa da ya fi karkata a kai, yana taɓa kowane sashe walau na barkwanci ne ko na soyayya da dai sauran irin nau’in fina-finai. Duk wanda ya kalli fim ɗin Rumfar Shehu ya san fim ne na barkwanci, fim din Dawo-Dawo fim ne na soyayya, fim ɗin Salma Hayat fim ne na jan hankali. Ya shirya fim ɗin da ya shafi addinin muslinci wato Ga Duhu ga Haske.

    ƘALUBALEN DA YA FUSKANTA A RAYUWARSA

    Kamar yadda muka sani duk wata ɗaukaka ta rayuwa sai an sami ƙalubale. Daga cikin ƙalubalen da ya fuskanta su ne; Ba ya manta lokacin Gwamna Shekarau a Kano, shi da abokin sa Aminu Saira sai da suka bar garin Kano suka dawo garin Kaduna, a lokacin ko kuɗin da za su kama ɗaki ba su da shi. Sai daga baya suka samu wani ɗaki da ake biya a Arewa House.

    Ya ƙara da cewa wannan babban ƙalubale ne mutum ya tafi ya bar mahaifansa. Bayan haka ya ce kallon da mutane ke musu da cewa suna ba da gudunmawa wajen ƙara taɓarɓarewar tarbiyan yara, ya ce wannan ma wani babban ƙalubale ne’. Sannan yace satar fasaha ma ƙalubane ne, domin sai sun gama wahala ba su mai da kuɗinsu ba sai zauna gari su kwafe don su saida.

    NASARORIN DA YA SAMU A HARKAR FIM

    Yace nasarorin da ya samu sun fi kalubalen yawa, sanin da mutane suka mai a duniya yana ganin babban nasara ce a rayuwar shi. Da kuma tarin masoya da ya samu ya ce matuƙa wannan abun yana burge shi. Daga cikin nasarorin ya samu gidan zama na shin a kan shi sannan ya sai abun hawa, har ila yau ya yi aure duk ta sanadiyar wannan harka ta fim. Inda yace yanzun kam Alhamdulillah yaran sa biyu sannan yana da mata ɗaya kuma yana zama a garin kano .

    YADDA ALI GUMZAK YAKE KALLON HARKAR FIM

    Ya ce a ganinsa harkar fim hanya ce da ke gyara tarbiya, sai dai kowa akwai irin kallon da ya ke ma harkar. Yadda mutum ya ɗauke ta, haka zai amfana da ita, sai dai su suna yi ne don gyara da jan hankali da kuma gargaɗi ga masu irin halin walau mai kyau ko akasin hakan. Ko kuma ya za a yi a nuna ma al’umma dai dai da kuma akasin hakan. Ya ƙara da cewa jigon fim shi ne mutum ya gani ya yi koyi da mai kyau ko ya watsar da na banza.

    NAZARIN FIM ƊIN BURIN FATIMA

    Yan Wasa
    1.Adam.A.Zango
    2.Aisha Aliyu Tsamiya
    3.Maryam Booth
    4.Ummah Shehu
    5.Jamila Gwaska
    6.Jamilu Kochila
    7.Haj. Aisha Mahuta
    8.Tasiri Kaduna
    9.Asma’u Nass

    Shiryawa; Abubakar Bashir Maishadda
    Mataimakin mai shiryawa; Aisha Aliyu Tsamiya
    Umarni; Ali Gumzak
    Mataimakin mai shiryawa; Murtala Balala
    Shirin kamfanin Maishadda Investment Nig.Llimited
    Shekarar: 2017

    Da farko dai an nuna Fatima da ƙawayenata su biyu a cikin makaranta, suna Magana a kan auren da Fatima ta yi, suna ba ta shawarar cewa ya kamata ta yi irin tsarin nan na ma’aurata domin idan ta haihu hakan zai shafi karatun ta. Bayan Fatima ta ba wa mijin ta wannan shawarar sai ya yi fushi ya nuna mata baya so. Sannan ya faɗa mata cewa haihuwa ba ya hana karatu, ya kuma kawo mata misali da wata da ta zama Farfesa, kuma ta yi aure ne bayan ta kamala karatun sakandare.

    An nuna Fatima ta samu juna biyu bayan wani ɗan lokaci, Umar ya yi matuƙar murna da wannan labarin sai dai bayan ta je makaranta ne ƙawayenta su ka ga tana amai sai suka fara ba ta shawarar cire cikin, har suna ba ta misali da cewa cikin mai laulayi ne ga shi karon farko har ta rasa jarabawa na gwaji na makaranta.

    A haka Fatima ta biye wa shawarar ƙawayen ta aka zubar da wannan cikin, ta cewa mijin ta ta yi ɓari. Bayan kammala makarantar Fatima da ɗan wani lokaci ne sai ta fara son haihuwa, amma sai Umar mijin ta ya ce mata “haihuwa na Allah ne, in lokacin ya yi zai ba su”. Duk da haka Umar bai daina neman mata magani ba a duk inda ya samu labarin wani likita ko mai maganin gargjiya.

    Ana haka ne kwatsam Umar ya samu labarin wani ƙwararren likita sai ya ɗauki Fatima, ya kai ta wajen shi. Bayan gwaje- gwaje sai ya gano wannan zubar da cikin da tayi ne a baya ya haifar mata da wanann matsalan, bayan komawar su gida ne sai Umar ya yi fushi da Fatima har ta kai ga ya ƙarba shawarar da mahaifiyarsa ta daɗe tana ba shi a kan ya ƙara aure.

    Bayan Umar ya ƙara aure ne da ɗan wani lokaci sai wannan matar ta samu ciki, murna a wajan Umar da mahaifiyar sa ba kama hannun yaro, lokacin ne koma Fatima ta ci gaba da ganin bambamci a cikin gidan, wanda amaryan ta haihu a hakan ba abun da ba ta gani. Umar bai da lokacin Fatima sai daga ƙarshe da ta nuna za ta bar gidan sai ya ce mata ya yafe mata kuma zai cigaba da neman man mata magani har Allah ya sa a dace.

    JIGON FIM ƊIN BURIN FATIMA

    Kamar yadda muka sani jigo na nufin ginshiƙin abin da fim ya ƙunsa. Wato dalilin yin fim ɗin. Akwai masana da dama da suka yi magana a kan jigo. Sun haɗa da, Sarbi,(2007;71) in da ya ce jigo a fagen adabi na nufin manufar marubuci, wanda dukan bayanai suka dogara da ita.

    Jigon cikin wannan fim ɗin shi ne “Gargaɗi ko jan hankali ga masu bin shawarar ƙawaye”. Idan muka yi duba yadda mijin Fatima wato Umar ya nuna mata soyayya sannan ya nuna mata yana son haihuwa, amma ƙawayen ta suka zuga ta da cewa idan ta bari ta haihu za ta kasa karatunta na jami’a, tattaunawarsu da ƙawarta a cikin cikin makaranta ɗaya ga cikin ƙawayen ta ta ke ce mata:

    “Ni fa na san ba a iya haɗa aure da karatu, domin da zarar kin samu ciki za ki fara samun carryover, daga nan kuma sai spillover, daga nan kuma sai tafiya, ba ki ga Karima ba sai da aka kore ta.” Har ila yau, za mu ga tun daga nan ta fara haska mata irin matsaloli da za ta fuskanta idan har ta yadda ta ɗauki ciki, da kuma abin da zai biyo baya na samun cikas a a harkar karatu, tare da buga mata misali kan makomar ɗaya daga cikin ƙawayensu mai suna (Karima) ta shiga, suna dai ganin rashin cikin shi ne alheri a shawarar su.

    An kara nuna su tare, inda suke zuga Fatima domin ta zubar da cikin da ta samu, duk da cewa ta nuna musu tana jin tsoro amma a hakan suka dage suka cusa mata wannan ra’ayin a zuciyar ta har ta amince da wannan shawarar: “Fatima kin ga tun daga yanzun daga samun cikin, kin fara samun matsala ba ki da test ɗin da malam ya yi jiya, sannan ya ce ba zai yi ma kowa makeup ba, kin ga abun da muke guje miki ke nan tun farko, don haka ki zo mu je asibiti a markaɗe cikin.”

    Sai Fatima ta ce:To me zan ce wa Umar? Ba ku ga yadda yake son cikin nan ba.”
    Sai ƙawarta ta ce mata: “To ki faɗa mai za ki yi kin zubar da cikin, zuwa kawai za ki yi mu je wajen wani doctor na cikin sauƙi zai miki komai, shi dai kawai ya san kin fito makaranta idan an gama ki koma gida ki kira shi a waya ki sa kuka yana zuwa ya tambaye ki ki ce cikinki, kin yi ɓari, shi ke nan”

    Bayan Fatima ta amince ne sai suka je aka cire cikin kuma ta yi duk yadda suka tsara mata. Idan muka duba wannan maganan da ƙawar Fatima ta yi za mu ga cewa ta ɗora ta a kan turbar ƙin yi wa mijinta biyayya wanda hakan ne ya haifar mata da duk wata matsala da ta shiga ciki na rashin haihuwa. Fim ɗin Burin Fatima ya nuna mana ƙin aminta da ƙawayen banza da kuma ɗaukar shawararsu wacce idan mutum ya bi tabbas zai faɗa halaka.

    NAZARIN FIM ƊIN IZZATU

    Jaruman cikin shirin sun haɗa da:
    Ali Nuhu
    Abdul.M.Shareef
    Hadiza Muhammad
    Fatima Muhammad(Fandi)
    Abdussalam Imam
    Ladidi Fagge

    Shiryawa; Yakubu Inuwa qyari
    Umarni; Ali Gumzak Sak
    Kamafanin; Gumzak investment Nigeria Limited
    Shekarar; 2019

    An nuna yadda wata budurwa mai suna Izzatu da wani ɗan uwanta wanda yake tamkar aboki a gare ta duk inda za ta suna tare haka ma aikin gida ko saƙo duk tare suke yi. Har iyayen su suke tunanin haɗa su aure domin ana ganin soyayya suke yi, kwatsam Izzatu ta kawo mijin aure gida aka sa lokacin aure ana ta shirye-shiryen buki, kwanaki na ƙara ja har lokacin bukin nan ya zo.

    Suna cikin shagalin buki ne a dandali da daddare sai ga wani tsoho ya zo yana musu magana a kan su daina dare ya yi, sai Izzatu ta yi masa rashin kunya ta ce bai isa ya hana su yin rawar gaban hantsi ba, har tana cewa ji tsohon nan. Bayan ta koma gida ta kwanta bacci ne sai wasu irin ƙuraje suka fito mata a jiki, aka dinga neman magani amma ba a dace ba, kwatsam sai aka samu labarin wani mai magani.

    Bayan sun je wajen shi sai ya ce wannan mutumin aljani ne, sannan za a samu magani amma sai wani na jikin ta wato mahaifin ta ko ɗan uwan ta ko dai mijin ta su ne kaɗai za su iya zuwa wajan maganin. Babanta makaho ne ba zai iya zuwa ba, don haka sai aka ce mijin da ta aura shi ya ce. Kwatsam sai wannan mijin ya kawo mata takardan saki.

    Don haka wannan ɗan uwan nata shi ya tafi wajan samun maganin, dama kuma da sharaɗin wanda ya je sai ya dawo shi ma da wata kalar cutan. Cikin nasara ya samu mata magani ta samu lafiya sai dai ya samu irin ƙurajen a jikinshi da kuma ƙusinbi.
    Iyayen Izzatu sun yi tunanin haɗa Izzatu da wannan abokin nata aure amma ta yi butulci ta ƙi yarda.

    Mahaifiyarta ta yi Alawadai da halin ta har ta kai ga gudu ta bar gida. Garin guduwan ne sai mota ta bige ta har aka yanke mata ƙafa. Bayan dai wannan abun da faru da ita sai suka so haɗa ta aure da ɗansu, sai suka gano asalinta su ma suka yi tir da ita suka mai da ta gidan su, da ƙyar suka yafe mata dai a ƙarshe.

    JIGON FIM ƊIN IZZATU

    Kamar yadda aka ba da ma’anar jigo a baya, shi ne ginshiki na gina fim ɗin. Wannan fim na Izzatu jigon shi, shi ne Butulci. Butulci na nufin (yankakkiyar rashin godiyar Allah). Rashin nuna godiya ga wani mutum. Inda butulci ya fito a wannan fim din shi ne inda Izzatu ta ƙi ta aure wannan ɗan uwan nan ta har ta gudu ta bar gidan su sanadiyar hakan.

    Sannan butulci a karo na biyu shi ne inda mijin ya sake ta a lokacin da ta ke buƙatar shi, lokacin da ya kamata a ce ya tafi wajan neman mata magani, amma sai ya mata sakayya da takardan saki duk da irin soyayyan da aka nuna sun yi. Butulcin da Izzatu ta ma wannan ɗan uwan na ta har ta nuna tana ƙyamar shi sannan kamar ma ba ta san shi ba.

    Wannan shi ne abun da ya faru a cikin shirin izzatu, an yi ƙoƙarin jan hankalin ‘yan mata masu ma tsofaffi rashin kunya da rashin ladabi ga na gaba da su, sannan an ja kunne ga kyautata wa wanda ya kyautata maka a rayuwa.

    NAZARIN FIM ƊIN ƘAWAYE

    Jaruman cikin fim ɗin
    Ali Nuhu
    Sani Danja
    Hafsat Ɓarauniya
    Aisha Humaira
    Hajara Usman
    Rahama Hassan
    Da sauran su

    An nuna ƙawaye guda biyu Ruma da kuma Fatima a makaranta saboda tsabar ƙawancen su a ɗaki ɗaya suke kwana a makarantar babu abin da ɗaya za ta yi ɗaya ba ta sani ba. Sai dai halinsu ya sha bamban kamar yadda ma su iya Magana kan ce ”Sai hali ya zo ɗaya ake abota” Su kuma wajan su ba haka ba ne. Don ita Fatima tana da natsuwa akasin ƙawarta Ruma.

    Hakannan matsalar ɗaya ta ɗaya ce, haka kuma kowa da yake a makarantar ya san su tare don haka komai na su ɗaya su ke yi. Suna cikin hakan ne ita Ruma ta samu matsala da saurayin ta sanadiyyar halinta na bin maza. Bayan kodayaushe ƙawar tana nuna mata gaskiya da cewa iyayen su fa karatu suka turo su ba wasa ba, amma ta ƙi ji. Saurayin da ya gane sai ya dai na zuwa wajan ta ya kuma dai na kiran ta.

    Sanadiyar hakan Ruma ta ne ma ƙawarta ta raka ta Abuja wajen shi, amma sai ta umarci ƙawarta da tace mai ta zo biki ne, hakan kuma suka yi sai ya kama mata ɗaki ya kuma ba ta kuɗi bayan ta faɗa ma Ruma ne sai ta ce ai soyayya su ke yi ba ta yarda ba, cikin hakan ne ta kira mahaifiyarta a waya tace mata ga fa ƙawarta ta tafi Abuja bayan kuma ta hana ta tafiya, maman ta yi fushi ta kira ta a waya ta tambaye ta inda ta ke sai ta ce tana gidan yayarta.

    A haka dai har ta samu ta kira yayar ta mata bayani shi koma saurayin Ruman ya biya mata kuɗin jirgi don ta yi saurin dawowa. An nuna lokacin da za ta shiga otel ɗin da ya kama mata, mijin da za ta aura ya ganta daga nan ya je ya yi mata mummunan zato sannan ya fasa auren ta, ya aika gidan iyayen ta aka kwaso masa kayan auren shi.
    Haka ita ma Ruma saboda halinta wannan saurayin nata ya fasa auren ta, ya dawo ya aure wannan ƙawar tata wato Fatima mai natsuwa da kuma hankali.

    JIGON FIM ƊIN ƘAWAYE

    Jigon wannan fim ɗin ba ya wuce nunawa ‘yan mata muhimmancin kamun kai. Idan aka ce kamun kai ana nufin natsuwa da yin abun da ya kamata da kuma kama mutuncin kai.
    A wannan fin ɗin mun ga yadda ƙawar Ruma wato Fatima ta so ta sa ƙawarta a hanyar daidai amma ta ƙi, don akwai inda ta ke ce mata;

    “Wai ke Ruma ba za ki canza halinki ba? Kin ga irin abun da nake faɗa miki ko, ba kya jin magana wannan tsalle-tsallen da kike yi ya yi yawa, yau ke ce kwaso wannan gobe ki ɗakko wancan, me ye amfanin shi? Ya kamata ki zauna ki ma kanki karatun ta-natsu ki riƙe mutuncinki, ke fa mace ce aure za ki yi wata rana……….”
    An samu wuri da dama inda aka nuna tana zama domin yi mata faɗa a kan halayen ta amma ta ƙi.

    KAMMALAWA

    Kamar yadda muka ji ma’anar fina-finai daga bakin masana da kuma jigon fim da kuma tarihin ɗaya daga cikin masu bayar da umarni a harkar fim ɗin, sannan da yadda muka yi sharhi a wasu daga cikin fina-finan, wato Burin Fatima, da Izzatu, da Kawaye. Haka koma mun ga muhimmancin fina-finai da kuma yadda mai ba da umarnin yake kallon harkar fim ɗin.

    MANAZARTA

    Sadik, L.A (2021) “Karatun Jami’a A Fina Finan Hausa” :Nazari Daga Wasu Fina-Finan Hausa. Kundin Digiri Na Ɗaya Jami’ar Jahar Kaduna.
    G.P Bargery, (2016) “A Hausa-English Dictionary And Englsh-Hausa Vocabulary” Jami’ar Ahmadu Bello University Press Limited.
    Chamo I.Y (2016), Saƙo A Fina-Finan Hausa: Nazari Kan Jigo Da Rabe-Rabensa, Kundin Binciken Digirin Na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero Kano.
    Gidan Dabino, A.A da Wani (2004) “Matsaloli Da Nasarorin Masu Shirya Fina-Finan Hausa Musamman Na Kano” A Cikin Adamu da Wasu (Editoci). Gidan Dabino Publishers, Kano.
    Hira da Ali Gumzak Da Muka Yi A Ranar Laraba 27-10-2021, A Garin Kaduna.

    Don Karanta Adana Harshe (LANGUAGE PRESERVATION) danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

     

     

     

  • Tarihin Farfesa Abdallah Uba Adamu

    Tarihin Farfesa Abdallah Uba Adamu

    Wannan Shi ne Farfesa Da Ya Kafa Tarihi A Duk Faɗin Najeriya.

    Farfesa Abdallah Uba Adamu, ɗan asalin unguwar Daneji a Kano, da ya kafa Tarihin zama Farfesa na farko sau biyu a fannoni daban-daban a Najeriya a Jami’ar Bayero, Kano. Ya zama Farfesa na farko a Science Education a 1997, sannan a Media and Cultural Communication a 2012. Shi kaɗai ne a Arewacin Najeriya da ya sami wannan nasara, yayin da mutum uku kacal ne a Najeriya gaba ɗaya.

    Baya ga koyarwa da bincike, ya shahara wajen nazarin Hausa, Tarihi, Al’adu, fina-finai, da tasirin kafofin sada zumunta, har ma ya ƙirƙiri haruffan Hausa masu lanƙwasa (ɓ, Ɓ, ɗ, Ɗ, ƙ, Ƙ) a kwamfuta a shekarun 1990. Ya shugabanci National Open University of Nigeria (2016–2021) tare da kawo sauye-sauye a tsarin karatun nesa, ya gabatar da shahararren jawabin Sunset at Dawn, Darkness at Noon (2004), kuma ya koyar a jami’o’in ƙasashen waje ciki har da Poland, Amurka da California Berkeley.

    Duk da irin wannan manyan nasarori, Farfesa Adamu ya kasance mutum mai barkwanci, sauƙin kai, da shahara a kafofin sada zumunta.

    Karanta Sababbin Karin Maganar Hausa

    Edita@rumasau-kallamu