Tag: yadda ake

  • Tsokaci A Kan Littafin Salmanu Da Salma

    Tsokaci A Kan Littafin Salmanu Da Salma

    Littafin “Salmanu da Salma” littafi ne na soyayya da aka gina bisa tubalin kimiyya da ilimi. Marubucin ya nuna cewa soyayya ba motsin zuciya ba ne kawai, tana buƙatar fahimta, haƙuri da haɗin kai.

    Babban jigon littafin shi ne soyayya, wacce ta haɗu da ilimi, inda jaruman ke fuskantar ƙalubale tsakanin burin rayuwarsu da  kuma soyayya. Labarin ya nuna yadda ilimi ke taimakawa wajen yanke shawara mai kyau a rayuwa.

    Salmanu jarumi ne mai son kimiyya da burin samun nasara, yayin da Salma ke ta kasance mace mai hankali, ilimi da juriyar zuciya. Rikice-rikicen da suka shiga sun sa labarin ya zama mai jan hankali.

    Kuma an yi amfani da kalmomi masu sauƙin fahimta, waɗanda suka dace da kowane mai karatu. Saƙon littafin shi ne cewa soyayya ta gaskiya tana bunƙasa ne, idan an haɗa ta da ilimi da mutunta burin juna.

    Karanta Tarihin Farfesa Abdallah Uba Adamu

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    “Ubangiji (Allah) ya halicci mutane, Samuel Colt ya dai-daita su”

    – Sammuel Colt (1836)

    12/08/2024

    SHIMFIƊA

    Samuel Colt ya faɗi wancan maganar ce bayan ya ƙirƙiri ƙaramar bindigar hannu (Revolver), don ya nuna mahimmancin abin da ya ƙirƙira. Sannan dan ya nuna rashin fifikon wani a kan wani idan kowa ya mallaki bindiga.

    Allah SWT ya ce: “Kada ku kashe kawunan ku, Allah mai rahama ne a gareku” (Q4:29). Allah Ta`ala ya ce: “Wanda ya kashe Mumini da gangan, sakamakonsa jahannama zai tabbata a cikinta…” (Q4:93). A Hadisi Manzon Allah SAW ya ce:” Baya tare da mu wanda ya ɗau makami a kan mu”

    Waɗannan ayoyi da hadisi da wasu masu tarin yawa suna hani ne game da kisan kai. A ayar farko Allah sai da ya nuna shi kansa mai rahama ne ga bayinsa, wato rashin tausayi ne da imani a zuciya ya ke sanya wani ya kashe mutum ɗan uwansa.

    A aya ta biyu kuma Allah ya nuna sakamakon wanda ya yi kisan kai ba da wani dalili na shari`ah ba. Manzon Allah ya faɗi cewa ba ya tare da Shi (Manzon Allah SAW) sannan ba ya tare musulmi gaba ɗaya wanda ya ɗau makami don zubar da jinin musulmi.

    MAKAMI A HANNUN FARAR HULA

    Hasashe ya tabbatar da cewa a duniya akwai ƙananan makamai kimanin milliyan ɗari Takwas da Saba`in da Biyar (875M) yawancin su a hannun fararen hula da gama-garin mutane.

    Kimanin miliyan ɗari (100) daga cikin waɗannan makaman suna Afirka, har da ƙasar mu Najeriya. Sannan kashi Arba`in (40%) na daga cikin mace mace a duniya sanadiyyar amfani da waɗannan makaman ne.

    Yaɗuwar ƙananan makamai musamman bindiga, wata matsala ce da duniya take fama da shi a yanzu. Bincike ya tabbatar da cewa abubuwan da suke ke janyo yaɗuwar ƙananan makamai sun haɗa da yaƙe yaƙe -rashin zaman lapiya a ƙasashe daban daban, da ayukan ta`addanci.

    Na biyu taɓarɓarewar dokokin ƙasashe da rashin ƙarfin gwamnatoci. Na uku ƙaruwar kamfanonin ƙirƙiran makamai a duniya. Waɗannan dalilai suna janyo ƙaruwar laifuffukan da suka haɗa da kashe-kashe, fashi da makami, kashe kai, ƙaruwar ayyukan ta`addanci da sauransu.

    Wannan matsalar ta shafi duniya gaba ɗaya, kullum ayyukan ɓarna da ke afkuwa cikin ƙasashe daban daban suna tabbatar da haka. Manyan ƙasashe irin su Amurka, kullum suna fama da irin waɗannan matsaloloin na amfani da ƙananan makamai wanda sanadiyyar su kullum ake rasa rayuka masu yawa.

    Duk da Amurka tana da dokar mallakar makami. Amma wannan matsalar ta addabi Amurka. Babban misali a nan shi ne yadda wani matashi mai suna Thomas Mathew Crooks ya kai wa ɗan takaran shugabancin ƙasar Amurka Donald Trump hari da bindiga, hakan ya yi sanadiyyar tsinke masa saman fatan kunnensa na ɓangaren dama.

    Wannan harin ya faru ne ranar 13 ga watan Yuli, 2024 a birnin Pennsylvania yayin da Donald Trump ya ke tsaka da yaƙin neman zaɓensa a zaɓen da ya gabata. Najeriya ɗaya ce daga cikin ƙasashen duniya da kuma Afirka da ke matuƙar fama da wannan matsala ta yaɗuwar ƙananan makamai a hannun gama-garin mutane da fararen hula, musamman a waɗannan shekarun.

    Ƙaruwar yaɗuwar makamai a hanun gama-garin mutane a Najeriya za a iya danganta shi daga lokacin da aka fara fasa bututun mai da kuma masu sace fararen fata suna garkuwa da su, musamman a kudancin ƙasar nan a baya.

    Zuwa rigingimun addini a Arewa ta tsakiya a farkon shekarun 90s, rigingimun Tibi da Jukun, sannan rigimar Boko haram/ISWAP da `yan ta`adda masu garkuwa da mutane a Arewa maso gabas na ƙasar nan, waɗannan rigingimu sun ta da zaune tsaye da kawo rashin kwanciyar hankali, sun janyo rasa rayuka masu yawa tun daga shekarun 2008 har zuwa yau.

    Gwamnatoci, ba za a ce ba sa taɓuka komai ba, amma a gaskiya, ayyukan `yan bindiga daɗi da masu tarzoma sun yi tsanani fiye da ƙima. Mutane har gani suke kamar sun fi ƙarfin hukumomi saboda wasu dalilai.

    Samuel Colt da ya ce Allah ya halicci mutane, shi kuma ya daidaita su. So yake ya fito da wani abu mai mahimmanci a fili. Duk wanda yake aikata aikin ta`adanci dan kawai yana riƙe da makami, toh ba fa ya fi wanda ya ke yi wa ta`addancin ƙarfi ba ne, kawai dan yana riƙe ne da makami.

    Duk lokacin da wanda ake yi wa ta`addanci shi ma ya riƙe makami, to sai dai kowa yi ta kansa, a lokacin kowa daidai yake da kowa, ba wanda zai yi wa wani ta`addanci, sai dai a yi kare-jini-biri-jini. Don haka kowa sai ya sa kowa cikin zullumi da tsoro.

    Masu riƙe da makamai sun sani, idan kowa zai sami makami toh su kansu ba za su ji daɗin rayuwar su ba kamar yadda suke yinta a yanzu, saboda yadda suke farautar sauran mutane, haka suma za a rinƙa farautar su.

    A irin wannan yanayi, sai rayuwa ta zama tamkar rayuwar dabbobi a daji wanda Allah ya ba shi sa’a shi ke nan, ba wanda ya ke da tabbacin rayuwarsa. Kowa kullum cikin zullumi da rashin kwanciyar hankali. Rayuwa ta zama ba komai ba, mara daɗi, gajeriya mai cike da tsoro.

    RUFEWA

    Allah SWT ya sanya rahama a cikin zuciyoyin halittarsa musamman ɗan adam, shi yasa za a ga Uwa yadda take tarairayar `ya`yanta. Wannan rahamar ce ta ke sanya mutum ba ya iya kashe ɗan uwansa haka kawai idan wannan rahamar tana cikin zuciyarsa. Shi ne abinda Allah ya ke nuni da ayar a aka ambata a farko.

    Shi kansa Allah da ya halicce mu, bai zama mai ɗaukan ranmu haka kawai ba, sai ajalin da rubuta mana ya yi. Duk wanda ya kashe wani, ya sani ba zai tabbata a duniya ba shi ma wata rana sai ya mutu, ya bar duniyar.

    A hadisin Manzon Allah SAW a fili ya faɗi cewa duk wanda ya ɗau makami ya yi kisan kai, to ba ya tare da Mu (wato ba ya tare da Manzon Allah SAW da kuma sauran muminai). Shin idan mutum ya mutu amma ba ya tare da Manzon Allah SAW, ina ne makomar sa?

    A aya ta biyu Allah ya ja kunnen mu da nuna mana sakamakon wanda ya aikata aika aikan kisan kai, makomar sa wutar jahannama kuma zai tabbata a cikin ta har abada. Shin wannan abin da Allah ya faɗa shin akwai wanda ya ke ganin ba haka ba ne? Ko kawai tatsuniya ce da labarin ƙanzon kurege?

    Duk musulmin da ya yi imanin akwai ƙiyama, akwai hisabi sannan akwai sakamako, to ya tabbata abinda Allah ya faɗi gaskiya ne to ba zai yarda ya kusanci wannan mummunan aikin ba, ba zai yarda ya ɗau ran wani mutum ba.

    Dukkan musulmi da yake rayuwa a wannan duniyar, na farko dai ya san zai mutu, toh buƙatar sa in ya mutu ya sami rayuwa mai daɗi da take cike da ni`ima wadda tafi ta nan duniyar. Rayuwar lahira ta aljannah ba a samun ta da saba wa Allah, musamman da mummunan aika aika na kashe ran ɗan Adam.

    Allah muna roƙonka ka shiryar da mu, Ka ganar da mu hanya mai kyau, Ka tabbatar da mu a kan ta, sannan Ka ba mu rayuwa mai kyau a nan duniya da rayuwa mafi kyau a lahira. Amin.

    Karanta Ayyukan Ta’addancin Matasa A Kano: Aure, Yawan Haihuwa Da Tarbiyya A Wata Mahanga

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Atini Yake (Dysentery)

    Yadda Atini Yake (Dysentery)

    Idan mutum na fama da atini yakan rasa samun sukuni, sannan a kodayaushe ya kan ji kamar kashi ya matse shi sosai tare da jin kamar zai yi shi a wando, amma kuma yana zuwa banɗaki sai ya ji ya kasa yin kashin ko ya yi ɗan kaɗan!!

    Idan ya kasance kana fama da wannan matsalar ko ka taɓa yin ta a baya, daure ka karanta wannan gajeren rubutun domin sanin  abin da ke kawo maka wannan matsala.

    ABUBUWAN DA KE KAWO ATINI:

    1. Kumburin magudanar Kashi (rectal inflammation): Rectal inflammation kan sa mutum atini sosai, bayan atini waɗansu daga cikin Alamominsa sun ƙunshi kashin jini da majina.

    2. Basir (Haemorrhoids): Basir Yana daga cikin abinda kan sa mutum atini sosai, musamman kafin ya yi tsiro, wani sa’in Kuma yakan sa mutum kashi mai tauri (constipation), kashin jini da sauransu.

    3. Infectious dysentery ko ɓacewar ciki: A lokacin da cikin mutum ya ɓaci bayan cin wani abu, mutum zai ta atini sosai sannan ya kasa sukuni a waje ɗaya.

    1. Kansar magudanar kashi (Rectal tumour): Duk mutumin da ke fama da rectal cancer kan zo da kashin  jini, kashi mai tauri(constipation) bayan atini.
    2. Pelvic Inflammatory diseases (sanyin Mata): Alamomin PID sun haɗa da ciwon mara, ƙaiƙayin gaba tare da fitar da wani irin ruwa mai wari daga gaban mace (vaginal discharge,) haɗe da zazzaɓi wani sa’in. Wani lokacin yakan haɗu da sanyin mafitsara, hakan zai sa ki yawan fitsari da rana ko yawan tashi da daddare (sau uku zuwa huɗu) domin yin fitsari, zafi yayin fitsari (dysuria), ganin jini a fitsari (haematuria) da sauransu.
    3. Kansar babban hanji (Tumour of descending colon): Alamominta sun ƙunshi atini, gudawa ko kashi mai tauri bayan rama da waɗansu alamomi na cutar kansa.
    4. Ulcerative colitis: Ulcerative colitis na daya daga cikin cututtukan da kansa kumburin Hanji. A lokacin da hanji ya kumbura mutum zai ta fama da atini da gudawa mai ɗauke da majina da jini wani sa’in.

    ME YA KAMATA MUTUM YA YI?

    Duk mutumin da ke fama da wannan ya kamata dai ya je asibiti domin masana abun su yi cikakken bincike a kan abin da ke janyo masa wannan matsalar. Binciken da masana za su iya yi maka a asibiti: likita zai iya saka yin waɗannan binkicen:

    1. Proctoscopy or sigmoidoscopy 

    2. Ko rectal biopsy a lokacin da likita ke zargin kansar magudanar kashi

    3. Coloniscopy with biopsy and Barium enema a lokacin da likita ke zargin alamomin colon cancer

    4.High vaginal swab (HVS), Abdominal Ultrasound Scan (USS) a lokacin da likita ke zargin sanyin Mara wato PID.

    MAGANIN DA LIKITA ZAI MAKA A ASIBITI:

    Maganin da likita zai maka ya danganta da abin da bincikensa ya gano:

    • Idan yakasance Infectious dysentery ne, likita zai ba ka Analgesia domin rage raɗaɗi, zai iya saka maka ruwa (iv fluids) tare  Antibiotics Wanda ya danganta me abun da test ɗin stool mcs ya nuna.
    • Idan Rectal inflammation ne likita zai iya ɗora ka a kan magunguna kamar steroid suppositories ko 5-ASA enemas, sannan zai iya ƙara makaa ruwa (fluids IV ) idan ka kasance ka yi amai sosai, likita zai ba ka antibiotics saboda infection.
    • Idan mutun na fama da PID ne toh likita zai iya ba ka waɗannan magungunan kamar analgesia domin rage raɗaɗin zafin. Ruwa (fluids IV) a lokacin da ya ga jikinka na buƙata empirical antibiotics.
    • Haemorrhoids (Basir) likita zai ba ka magunguna sannan zai ce ka dinga yin Sits bath (wato Zama cikin ruwan gishiri) ko kuma idan ya yi tsauri sosai ya yi maka aikin da ake kira Haemorrhoidectomy.
    • Idan ya kasance Rectal tumors ne ko colonic tumors toh likita zai iya buƙatar yi maka aiki ko ɗora a kan magungunan kansa. (cytotoxic drugs) ko ya yi maka  radiation therapy.

    Daga Cikin bayanan da na yi za a ga na ɗan yi bayani a kan magani na yi hakkan ne kasancewar akwai ɗalibai ‘yan uwana. Allah Ubangiji ya ba mu Lapia da zaman lapia Amin ya rabb

    Danna nan don karanta Yadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa

    Yadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa

    Mahaifar Mace wato “Uterus” a sanda ta ɗauki ciki babu wani guri a jikin halittar ɗan adam da jini ke kai-komo ba tare da ƙaƙƙautawa ba irin wannan gun…. Saboda ƙoƙarin jiki don ganin ya samarwa da abinda ke cikin iska, jini, abinci da kyakkyawan yanayi. Guri ne da ake kira “No go Area” in dai da sunan wargi ne, saboda ko ya hatsari ya faru ana iya shiga uku.

    A duk minti ɗaya na agogo wato sekons 60 sai jini adadin Milimeter 800 zuwa dubu (1liter) ya shiga mahaifa ya fita. Wato dai kwatankwacin ledar pure Water 3 zuwa 4 na jini a duk minti. Shi ko jini baki ɗaya a jikin mutum an yi ƙiyasin ba ya wuce lita 5. Ka ga kenan a minti biyar kacal duk adadin jinin da ke jikin mutum ke shiga ya fita daga cikin Mahaifa. 

    Toh wannan ne yasa ko ya mace ta haihu jini ya ɓalle minti 4 zuwa 5 kacal ta mutu ta gama. Abun ba ya buƙatar ɗaukar lokaci, domin kafin a ankara an yi ta an ƙare. Shi yasa zubar jini bayan haihuwa da ake kira post partum hemorrhage ke kashe mata a karkara da birane ba ji ba gani, domin ko kuna raye a inda manyan asibitoci suke jinkiri kaɗan na abin hawa, ko shawarwarin ya za ai, ko cinkoso a hanya na iya kawo mutuwa ɓagatatan. 

    Toh yanzu Mace masu ciki sun saka kansu cikin wata musiba ta shan wani ruwa da suke wa laƙabi da “RUWAN NAƘUDA” ko a sakaya a riƙa faɗin “RUWAN ADDU’A”. Da ake karɓarwa mata a ba su su sha da sunan naƙuda ta zo musu a gurguje su haihu nan da nan abinda muke kira “PRECIPITATE LABOR.” 

    To alal haƙiƙa ku sani wannan ba wani ruwa ba ne illa ruwan musiba, ruwan guba, ruwan ta-da zaune tsaye, wallahi, wallahi, wallahi duk macen da ke marmarin tafiya lahira a dalilin haihuwa, ko take da burin ta sha da ƙyar tare da ja wa mijinta da iyayen ta asarar manyan kuɗaɗe ba tare da shiri ba, ko take da burin daga haihuwa ɗaya kar ta kuma har abada…

    Toh ta je a ba ta wannan ruwan ta riƙa sha, tunda Allah ya ba ku hankali don ku yi tunani amma sam kun mai da ƙwaƙwalenku tamkar tsumma. Kowanne tarkace yanzu kawowa ake mata su kuma su ɗiba babu lissafi. Shi wancan ruwan wasu muggan sinadarai ake sa mishi masu aiki irin na “Okzitosin” da nan da nan ke sa mahaifa ta fara harbawa tana jijjiga domin juye abinda ke cikinta, tana fisga tana talewa ƙarshe musibar da ake shiga FASHEWAR MAHAIFA yake haddasa wa inda nan da nan Mace kan fita hayyacinta, ta nufi lahira.

    Amma masu ba da irin wannan ruwan wasu ma iyayen yaran ne ke kawo musu. Sun kashe ‘ya’yansu ba tare da sun san su ne suka kashe su ba, sai dai a ce ta haihu amma jini ya ɓalle Allah ya yi mata rasuwa. Karya ne ku kuka kashe ta, kuma akwai shari’a gaban Allah. Kun ba ta abinda ba ku da ilimi kansa, kun ƙi kuma saurarar masana ku ji jan hankalin da suke game da irin wannan muggan al’adun.

    A ƙalla na sami mata uku da suka mutu a wannan tsakanin dalilin shan wannan ruwan naƙudar. Sannan na sami mutum 2 tsakanin nan ‘ƴar shekara 17 da ƴar 21 wanda suka sami fashewar mahaifa, duk da ba su mutu ba sun sha da ƙyar to amma dai hakan na nufin ba su ba kuma ɗaukar ciki ballantana su haihu a duniya, in mahaifa ta fashe ba batu ne a ɗinke ta ba, ta riga ta yi condemn.

    Kuma abin takaici duk jariran nasu sun mutu tun a ciki, shikenan in ba mazajen ƙwarai ba ne shin wa zai zauna da macen da ba zata iya haihuwa ba a irin wannan rikitaccen zamanin namu? Sabuwar amaryar shekara ɗaya a ce ka gane ba ita ba kuma haihuwa dole sai kai shirin kuma sabon aure in kana son haihuwa. 

    Toh wannan ba shi ba ne ma ƙarshen damuwar, ba su ba kuma iya riƙe fitsari, yanzu rayuwarsu za ta dauwama ne da robar fitsari a jika, hanyar kashi ta ɓulle ta dubura ta haɗe da farji. Tsabar wauta da rashin hankali, yarinyar da ko haihuwar fari ba ta yi ba amma da zarar ta sami juna biyu shikenan anta mata aiken abubuwa iri-iri ana ta sha, wannan maganin zaƙi, wannan maganin ciwon mara da dai sauran su.

    Ya kamata idon ya buɗe ku gane me duniya take ciki, kar ki laminci ganganci da rayuwarki. Lallai mu hankalta. Babban abin damuwar har ‘yan boko ko matan da kake ganin suna da ilimi su ma sukan auka cikin irin wannan ɗebe-ɗeben, a haka na sami mace me Masters amma ta je wai an ba ta maganin fibroid a Islamic CHEMIST. An ce idan ta sha zai narke, ƙarshe ga shi fibroid bai narke ba dukkan mararta ta zazzage.

    Dole aka cire mahaifar aka zubar, sannan ba ita ba kuma haihuwa, sannan mafitsararta “Bladder” ta fashe ba za ta gyaru ba, fitsari yanzu ta cikin farjinta yake fita, haka zalik kashi ma wani na fita ta duburarta wani kuma na biyo ta cikin farjinta duk. Yanzu me ya fi wannan tashin hankali, kin je kin kashe kuɗi kin illata kanki a banza da wofi.

    Hakance dai ke faruwa a fannin breast cancer, mace na fama da ciwon nono amma taita biye-biyen masu magunguna a loko suna karɓe mata kuɗi, ba za ta je asibiti ba sai abu ya gama lalacewa nono ya fara wari, in cancer ta gama yaɗuwa inda sai de mutuwa kurum. Don haka Lallai Yan Uwa Mata ku yi hattara, lafiya ta wuce wasa wallahi in kunne ya ji……

    Karanta Yadda Hawan Jini Yake (HYPERTENSION)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Kammalawa Daga Cikin Littafin Ka San Kanka

    Kammalawa Daga Cikin Littafin Ka San Kanka

    Warwara

    Duk da na bayyana muhimmancin mutum ya gano kansa, zan iya cewa ba dole sai ka yi hakan ba. Gano kai wani aiki ne babba mai matuƙar wahala, da in ba ka yi sa’a ba zullumin da za ka shiga a ƙoƙarin gano kanka zai iya lahanta maka ma rayuwa, ya hana ka jin daɗinta.

    Kamar yadda na fara ba da labari a farko, na daɗe ina son gane ni wane ne, kafin na gano kai na har ciwon damuwa sai da na yi, na ma fara karɓar magani a asibiti na ga abun ba mai ƙarewa ba ne na watsar, amma ban karaya ba, na ci gaba da tambayar kai na da kuma ƙoƙarin nemo amsoshin tambayoyin.

    Ba zan ce iya ƙoƙarin gano kai na ne ya sa ni a damuwa ba, abubuwa ne da yawa suka haɗu, amma dole ko dai rashin sanin ni wane ne ya taimaka, ko kuma son gano ni wane ne ya ƙara ingiza abun. In kana ganin ba lallai ka iya jure wahalar da take cikin aikin gano kanka ba, ba kuma za ka iya rayuwa cikin haɗarin rashin sanin kanka ba, to ina ganin abu ɗaya za ka yi.

    Ka bi wanda yafi ka sanin kanka sau da ƙafa. Duk abin da kake son sani ya turo an sanar da kai, duk abin da kake son aikatawa ya turo an koya maka. Na san za ka fahimci inda na dosa, ina nufin ka zama mutumin kirki mai biyayya wa Allah da manzonsa (tsira da aminci su tabbata gare shi) domin in dai ka tsaya kan hanyar da suka ɗauraka a kai, dole za ka amfanu kuma za ka amfanar, za a ƙaru da zuwanka duniya, kuma duk abubuwan da na lissafa a baya za su dinga zuwa maka a ɗabi’ance (naturally) ba tare da wani hoɓɓasa ba, kamar dai abin da ake cewa “autopilot”.

    Idan ka yi wannan ka hutasar da kanka yawan tunani. Duk da cewa ita ma fa wannan hanyar ba sauƙi ne da ita ba, domin kana buƙatar ilimi da kuma aiki da ilimin, ilimi na gaske ba na wasa ba, aiki na gaske ba na wasa ba. Sai ka san ibada da mu’amala da haƙƙoƙin mutane a kanka da haƙƙoƙinka a kansu, da dabarun zaman lafiya da mutane, da yadda rayuwarka a cikinsu za ta amfane su kamar yadda ta magabata ta ke amfanarmu.

    A iya ilimina (wanda ɗan kaɗan ne) ban san wani mutum da ya yi wata bajinta ba a duniya da bai zo wata gaɓa da ya san kansa ba. Kowa in za ka saurare shi, ko za ka karanta littafi ko rubutunsa ko tarihinsa za ka fahimci cewa daga cikin sa’ar da ya yi a rayuwa akwai gane shi wane ne da ya yi da wuri.

    Don haka ko wanda ya zaɓi yin rayuwarsa kan tsari mai kyau zai zo gaɓar da zai san kansa, ko kuma ya dinga rayuwa kamar ta wanda ya riga da ya san kansa ko mai daren daɗewa. Akwai wani hadisi da sahabbai suke tambayar Annabin Allah mai tsira da aminci kan cewa tunda Allah ya riga da ya ƙaddara ƴan wuta da ƴan aljanna, ai ba buƙatar kowa ya yi komai, sai ya jira ƙaddararsa, sai ya ba su amsa da cewa “ku yi aiki, kowa za a sauƙaƙe masa abin da aka halicce shi don shi”.

    Wannan yana nuna mana cewa ba a taɓa kafa hujja da ƙaddara, ko a zauna ana jiran rayuwa ta faru, manufar halittar shi ne ka rayu, ba ka zauna jiran rayuwar tana wucewa ba (waɗanda suka mutu a wurin kare addini Allah yace kar mu ɗauka a mace suke, a raye suke, wataƙila saboda sun mutu a kan manufa da bin tafarki, Allah ne mafi sani).

    Don haka in ba za ka iya sanin kanka ba, to ka bi Allah ka huta, in za ka iya sanin kanka kuma ka samu riba biyu kenan, ka san kanka, kuma kana bin Allah a yadda kake don haka komai zai dinga zuwa maka a sauƙaƙe. Manufar rubuta wannan ɗan ƙaramin littafin shi ne karkato da hankalinmu kan yin rayuwa da manufa da tsari, ba kara zube ba.

    In muna kara zube yanzu muka fara ganin cin kowanne irin kashi, ba za mu taɓa kwarjini ba, balle mu cimma wani abu, mu da ƙorafe-ƙorafe da ganin laifin juna mun ɗaura kenan har illa masha Allahu. In ka samu wannan littafin kada ka karanta shi ka ajiye shi, ka yi ƙoƙarin yin aiki da wasu abubuwan da ka ga za su iya dacewa da taka rayuwar.

    Sani ba aiki ba ya canja komai, bambancinsa da rashin sani kaɗan ne. Allah na ke
    roƙo ya ba mu dacewa duniya da lahira ya kuma azurta mu da kyakkyawan ƙarshe.
    Kada a manta da yaɗa wannan saƙon dan amfanar ƴan’uwa gaba ɗaya, musamman matasa ƴan’uwana da ke ta faɗi tashin ganin sun gano kan rayuwa.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

    Danna nan don karanta Yadda Manufar Rayuwarka Take

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Manufar Rayuwarka Take

    Yadda Manufar Rayuwarka Take

    Manufar Rayuwarka
    Wannan kusan zan iya cewa shi ne ma ya kamata ya zo a farko, amma na jinkirta shi ne saboda amsar da ka samu daga sanin kai wane ne ita za ta haska maka manufar rayuwarka. Kowa akwai abin da Allah ya halicce shi ya yi a wannan duniyar, wanda ya gano na sa da wuri kuma ya duƙufa a kai shi ne yake cimma nasarori da wuri.

    Idan ka bibiye littafin nan tun daga farko, za ka gano wata gaskiya guda, babu irinka a duniya. Kafin a samu wani da ƙwayar halittarku ta zo ɗaya, shekarunku, iliminku, gogewarku, abokanku, iyayenku, makaranta da unguwarku duk ɗaya abu ne mai matuƙar wahala.

    Kenan kai a matsayinka na wanda babu irinsa akwai abin da za ka yi da rayuwarka da ba lallai wani ya yi irinsa sak ba. Ba kowa ne yake iya gano manufar rayuwarsa ba ko da ya san kansa, amma aƙalla dai zai zama ya samu wata hanya da yake bi, tunda ya san shi wanene, zai gane ina ya kamata ya dosa.

    A lokacin da yake kan hanyar ne kuma Ubangiji zai ta haskaka masa yana nuna masa abubuwa. Wani lokacin za ka yi ta yin wani abu ba ka ɗauke shi a bakin komai ba, sai
    rayuwa ta yi nisa sai ka ga ashe wannan abin kamar an shirya ka ne don ka zama wani da shi a gaba. Wani lokacin kuma kwatsam wani abin zai faɗo rayuwarka, in ka ba shi lokacinka da tunaninka sai ka ga hanyar tana ta ƙara faɗaɗa.

    Yana da kyau mai ƙoƙarin gano manufarsa ya amsa waɗannan tambayoyin. Ni wanene? Daga ina nake? Ina zan je ni? Yanzu a ina nake? Me nake yi yanzu don isa wurin? Lallai waɗannan tambayoyi matukar an dage da yinsu ba za a samu zaman lafiya ba sai an isa wurin. Kuma hakan ake buƙata.

    Ita rayuwa duk lokacin da ta ga wani gurbi ba a cike shi da komai ba, sai ta cike wa mutum da wani abu da ba zai amfane shi ba. Kamar yadda basirar da aka ƙi yin komai da ita take nemawa mai ita abin yi, haka rayuwa take raba mana ayyuka ba tare da mun shirya musu ba. Kafin mu ankare kuma sun zame mana jiki sai mu ma ɗauka dama su ne ya kamata mu yi ta yi.

    Abin dai da yafi muhimmanci shi ne mu ayyana wa kanmu wata hanya da muka ɗauka muke son bi, wannan zai sa komai na mu ya dinga tafiya a tsari, in ma hanyar ba mai ɓullewa ba ce ba mu da asara, za mu samu darussa da dama, kuma ta haka za mu lalubo mai ɓullewar. Kowa nan duniya da ka gani da gwaji ya kai in da ya kai, wanda yake tsoron faɗuwa ba ya taɓa zama gwani.

    Duk lokacin da aka yi zancen manufa dai ya zama kana tuna cewa Allah ne ya halicce ka, kuma yace ka bauta masa, kuma yace in ka bauta masa zai maka sakamako da aljanna, kenan ya zama dole ya zama koma mene ne za ka yi kana kawo waɗannan abubuwan a farko.

    Duk layin da ka ɗauka ka ga ba zai kai ga wannan ba daga ƙarshe, wannan ba layin kamawa ba ne, ka yi ƙoƙari ka watsar da shi ka nemi wani. Allah yana da kyauta, duk abin da za ka yi in ka yi da niyyar ya ba ka lada babu abin da zai hana ya baka lada sai in har ka saɓa masa ko ka saɓawa koyarwar manzonsa.

    A taƙaice dai jin daɗin lahira ne yake zama kan gaba cikin tunanin mai manufa da kuma aiki yadda addini yace a yi, ko da kuwa a yanzun baƙar wahala yake sha, tunda ya san sakamakonsa yana can. Abubuwan da za su taimaki mutum a kan manufa sun haɗa da kyautatawa Allah zato.

    Duk inda kake tsammaninsa a nan yake kamar yadda ya faɗa a hadisul Ƙudsi. Bayan wannan sai mutum ya so kansa, ka da ka raina kanka duk yadda kake, domin kana da wani abu da za ka iya bayarwa ba tare da ka ma sani ba. Daga nan sai tsaida hankali kan ƙananun abubuwa na kusa, kada ka shagaltu da tunanin manyan abubuwan da za ka yi, har hakan ya hana ka yin ƙanana.

    Na sha shagaltuwa da tunanin manyan abubuwan da yakamata ace na yi ko ina yi, a haka lokacina zai tafi, ban yi ƙanana na kusa da ni ba, kuma babban ma ba yi zan yi ba. Yanzu da na fara ƙananan sai haske yake ta zuwa mini, nake samun matakala da za tai ni zuwa ga sauran.

    Ba dole sai ka shahara da wani abu ba za ka ba da gudunmawa, amfanin manufa shi ne kawai ya zama an ƙaru da kai ko yaya ne. In dai ana ƙaruwa da mutum kuma hakan ya sa a gaba to ya riga da ya samu manufa, ko da ba a san shi a dandalin sada zumunta ba (in hakan ba ya cikin burinsa kenan).

    A matsayinmu na bayi, waɗanda ba mu san ƙaddararmu ba, aiki shi ne na mu, zartarwa kuma na mamallakin ranar sakamako ne. Ganin damarsa ne ya cika mana burukanmu tun a nan, ganin damarsa ne kuma ya mana tanadi a can, ba a masa dole, ba a kuma kwanciya da sa ran shi zai yi, za mu yi, za mu jira zartarwarsa ba tare da ƙosawa ba, in bai ba mu ba sai mu sake gwada wani layin, wataƙila a can rabon yake.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

    Danna nan don karanta Yadda Za Ka Tambayi Kanka Da Kanka

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Za Ka Tambayi Kanka Da Kanka

    Yadda Za Ka Tambayi Kanka Da Kanka

    ❖ Wacce Baiwa Kake Da Ita?

    Sanin wannan rabe-rabe na mutane zai haska maka kai wanene, daga nan sai ka tambayi kanka, menene ƙarfi na? Wacce baiwa ce Allah ya mini da mutane duk sun sallama in dai a wuri kaza ne in dai ba ni ba sai dai a yi maleji?

    Menene a ɗabi’ance yake zuwa mini da sauƙi? Rubutu ne? Karatu ne? Gudu ne? Hadda ne? Iya magana ne? Haƙuri ne? Juriya ne? Naci ne? Son jagoranci ne? Lissafi ne? Da dai duk wata baiwa da ka san kana da ita.

    Wani yana da basirar ƙirƙirar sabon abu, wani kuma basirarsa tana cikin kwaikwayo ne, in dai za a yi a gabansa sai ya kwaikwaya, wani kuma saurin koyo ne da shi, in dai an koyar da shi to sai ya gane, wani yawan bincike ne da shi, duk abin da ake so a binciko zai iya.

    Babu wani da Allah ya yi shi ba wata baiwa, in ma mutum bai gane baiwarsa ba to ita baiwar za ta kai shi zuwa wani wuri da take kai irin masu baiwar. Misali mutum zai iya tsintar kansa a halin yin waƙe-waƙe, ko wasan barkwanci, ko rubutu duk wannan yar manuniya ce da ke nuna cewa mutum yana da basirar ƙirƙira.

    Abin da ya rage kawai ya tsaya ya nutsu yaga mai zai yi da wannan baiwar da yake da ita. Zai iya zuwa ya koyi aikin hannu kowanne iri ne, zai iya shiga harkar binciken fasaha don ya samar da wanin sabon abu.

    Wanda yake da baiwar hadda ko yawan karatu ya ɗauko hanyar ilimi da malumta, ya rage ya nutsu ya san wanne ɓangare ne na ilimi in ya yi zai fi zuwa masa da sauƙi, kuma mutane za su fi amfana da iliminsa. Ba malumta ba kaɗai, duk wanni fanni da zai buƙaci ƙarfin iya kiyaye bayanai komai yawansu.

    Wanda yake da baiwar iya magana ko jan ragama ya san Jagoranci zai zo masa da sauƙi, don haka duk inda ya samu wata dama da zai zama jagora ya yi ƙoƙarin jan ragamar, saboda wannan zai sa ya ƙara samun gogewa a harkar mulki da hulɗa da jama’a. Idan na yi maganar jagoranci ba na nufin mutum ya fito takara ko ya zama mayen mulki (ba a son mutum ya dinga neman mulki), abin nufi a wurin da ya samu kansa da ya tabbatar in bai tsaya tsayin daka kan jagorancin ba tafiyar za ta gurgunce.

    Abin dai shi ne, ba wata baiwa da ba ta da amfani, abu mafi wahala shi ne a gano ta, bayan an gano ta kuma a san inda za a yi amfani da ita. A wannan mataki iyaye da makusantan mutum suna da rawar da za su taka, waɗanda aka gano inda suka fi karkata tun suna ƙanana kuma aka taimake su a kan hakan sun fi saurin cimma nasara sama da waɗanda aka bar su suna ta tsilla-tsilla.

    ❖ Me Kake Jin Daɗin Yi/Me kake so?

    Bayan ka gane ƙarfinka da rauninka na halitta abu na gaba da za ka nutsu ka tambayi kanka shi ne menene kake jin daɗin yinsa. Duk abin da kake jin daɗin yi yana haska maka kai wane ne, domin son wani ƙin wani ne, yadda kake son abin haka wani kuma yake ƙinsa, kenan da kai da shi iri ɗaya ne da shi ma ya so.

    Shi wannan ɓangare sai ka durfafe shi kamar mai nazarin kimiyya, ma’ana yadda wanda ya shiga ɗakin gwaje-gwaje yake nutsawa cikin bincike, ya yi ta gwada abubuwa kafin ya gano daidai haka kai ma za ka yi. Idan ƙwallon ƙafa kaɗai kake bugawa ba za ka san daɗin ƙwallon kwando ba, har sai ka buga dukka biyun da ƙwarewa iri ɗaya kafin ka gane wacce ta fi maka daɗi.

    Wanda yake saurarar karatun sheikh Sudeis kaɗai ba zai iya cewa ga karatun da yafi daɗi ba har sai ya saurari na sheikh Shuraim. Don haka kar ka gajiya da lura da kanka a duk wani aiki da ka yi don ka gane wanne ne in ka yi shi ko lokacin da kake yi kake jin wani shauƙi na musamman.

    Haka nan za ka san me kake so ne ta hanyar gwada abubuwa da yawa. Ba za ka san kalar abincin da ka fi so ba sai ka ɗanɗana abinci da yawa. Wanda iya tuwo yake ci ba shi da hurumin cewa ya fi son tuwo duk cikin abinci har sai ya ɗanɗana farfesun naman kai ya ji. Don haka wannan fannin yanabuƙatar nutsuwa sosai kafin mutum ya gane mai yake so.

    Wannan kuma fa ba ya nufin ka shagaltu da gwada abubuwa kaɗai, kana ci gaba da
    rayuwarka ne za ka dinga ganewa. Idan kallon fim ko kallon ƙwallo ko danna waya ko yawan bacci ko zaman majalisa ne abin da ka fi jin daɗin yi fa? Gaskiya saboda Allah mutum a irin wannan halin babu inda zai je, dole ya tashi tsaye ya natsa da tambaya da
    lura da aikata wasu abubuwan har ya gano wasu abu da yake jin daɗi.

    Ya kamata a wannan gaɓar mutum ya tambayi kansa kan abubuwan da yake jin daɗi tun yana yaro, in ya manta ya tambayi makusantansa, saboda lokacin da muke yara ba mu gurɓata da komai na duniya ba, muna nan a tsarkake yadda Allah ya halitto mu, don haka amsoshinmu da dama kan sanin kanmu suke komawa kan yarintarmu.

    ❖ In Ba Kuɗi A Duniya Me Za Ka Yi?

    Idan da a ce yau za a wayi gari ba kuɗi a duniya, ko kuma ka samu duk kuɗin da kake buƙata har ka mutu, me za ka yi? Wannan tambayar amsa ta yana da matuƙar muhimmanci saboda yawancin mutane kuɗi ne yake mantar da su kansu. Wani yana sha’awar ya zama uba nagari, wani miji nagari, wani ɗa nagari to amma saboda neman kuɗi sai ya rasa lokaci da ikon cika waɗannan burukan.

    Wani koyarwa yake so amma saboda cin kashin da ake yi wa malamai sai ya gwammance ya buɗe shago. Wani ƙere-ƙere yake sha’awa, to amma likitoci suna samun albashi mai yawa, don haka ya gwammanci ya yi ta zama a asibiti ko da hakan ba ya sa
    shi jin yana wata uwa da rayuwarsa.

    Wani ilimi yake buƙata, to amma mawaƙa sun fi kowa samun kuɗi dan haka ya bar makaranta ya shiga sana’ar waƙa. Duk waɗannan abubuwan da na lissafa kuɗi ne ya karkatar da hankalin mutum daga haƙiƙaninsa, da kuɗi ba matsala ba ne da wataƙila wannan fannin zai ɗauka.

    ❖ Menene Cin Nasara A Wurinka?

    Muna rayuwa a wata duniya da ake ɗauka cewa tara dukiya shi ne cin nasara saboda kallon talabijin da fina-finai. Amma cin nasara daga mutum ne. Kowanne mutum a can ƙasan zuciyarsa ya san menene in ya samu ko ya aikata ya ci nasara. Yana da kyau a lokacin da kake ƙoƙarin gano kanka ka amsa wannan tambayar, menene nake ɗauka a matsayin cin nasara?

    Kada ka yaudaru da abin da mutane suke ɗauka a matsayin cin nasara, ka tsaya dai iya kan tambayar kanka mene ne in na yi na ci nasara. Shi samar da ma’anar nasara a rayuwa yana da matuƙar amfani, saboda cin nasara ba abu guda ɗaya ba ne, sai an samu gamsuwa a fannoni da dama na rayuwa kafin a samu gamsuwar an ci nasara.

    Tun daga kan ɓangaren addini, iyali, abokai, aiki/sana’a, lafiyar jiki, mutanen da ake hulɗa da su duk sai mutum ya iyakance mene ne cin nasara a ciki. Wacce irin mata zan aura na ci nasara? Me zan dinga yi na addini kullum da zai sa ni cikin masu nasara? Waɗanne irin abokai ya kamata na dinga hulɗa da su? Wanne mataki zan kai a sana’a ta na zama na ci nasara?

    Lafiya cikakkiya na ke buƙata ko kuwa ko da ina laulayi ma ina ɗaukar kaina a matsayin na ci nasara? Wannan fa duk kai a karan kanka ne za ka amsa su, domin cin nasara a
    kowanne ɓangare na rayuwa yana da alaƙa da kai wanne irin mutum ne, me kake so, me ka zaɓi ka tafi a kai, me kake yawan tunani a kai.

    ❖ Yanzu A Ina Kake?

    Tambaya ta gaba da za ka amsa ita ce yanzu a wanne mataki kake a rayuwa? Wanne irin ilimi ka tara? Wani mataki ka kai a sana’arka? Menene kake da ƙwarewa a kai? Mutumin da bai san a ina yake ba ba zai iya sanin shi wane ne ba. Ita wannan tambayar ta matakin da kake yanzu za ta taimaka maka wajen kamanta wurin da kake da ma’anar da ka ba wa cin nasara.

    Sannan za ta zama maka wata matakala da za ka taka ko wani sitiyari da za ka juya akalar rayuwarka da shi. Misali, idan daga cikin ma’anar da ka ba wa cin nasara akwai ƙwarewa a sana’arka, sai ka dubi inda kake yanzu ka ga ba ma ka ɗauko hanyar
    ƙwarewar ba, ko kuma ba ma a sana’ar da ya kamata kake ba. Wannan zai sa ka fara tunanin matakan da za ka ɗauka don ka ƙware, ko kuma hanyar da za ka bi don canja sana’a ko ƙarawa da wata sana’ar.

    ❖ Me Yake Ɓata Maka Rai?

    Ɓacin rai motsin rai ne mai ƙarfin gaske, a lokuta da dama mu kan ga abubuwa da yawa da ranmu yake ɓace a kansu. Wasu za mu iya sauya su amma ba mu taɓa gwadawa ba, wasu kuma sun fi ƙarfinmu, wasu kuma za mu iya amma mun fi jin daɗin mu jingina wa wasu lefin, mu ba wa kanmu hanzari.

    Sau da dama abubuwan da suke ɓata mana rai suna haska mana mu waɗanne irin mutane ne, mene ne burinmu, kuma da za mu samu dama mai za mu iya aikatawa? Don haka yake da muhimmanci mutum ya dinga lura da mene ne a cikin al’umma yake yawan ɓata masa rai.

    Idan lalacewar ilimi yana damunka kuma kana yawan surutu a kan hakan to wataƙila Allah ya maka wata baiwa ne a ɓangaren ilimin, da za ka tsaya ka yi nazarin mafita kuma ka aikata hakan da sai kaga an samu waraka, kai kuma jin daɗinka zai zama gaban kwatantawa domin ka warware wata matsala da take ci maka tuwo a ƙwarya.

    Idan lalacewar tarbiyya ce ta dame ka, kuma ranka yana ɓaci a kan hakan to wataƙila za ka iya zama jagora na kawo sauyi a wannan ɓangaren. Idan rashin wutar lantarki ne yake damunka wataƙila kana da wani abu da za ka iya yi a kai ba ka sani ba. Haka dai za ka yi ta duba abubuwan da suke damunka kana musu kallon “a maimakon a ce ina jiran wani ya zo ya ceto mu, in da ni zan yi ceton ta wanne ɓangare ne zan fi ba da gudunmawa?”

    Akwai mutanen da su dai burinsu a gaza ne su bayyana an gaza, ba lalle abin yana damunsu ba, babbar alamar gane su shi ne kullum surutu suke amma ba sa komai a kan matsalar. To in ka samu kanka a wannan halin abu ɗaya (1) za ka yi, shi ne ka tambayi kanka ko kana da iko kan wannan abin? In ba ka da iko to ka ɗauke hankalinka daga wurin, in kuma kana da iko ka sa himmar kawo gyara.

    A taƙaice dai muna buƙatar mu dinga tunani a kan abubwuan da suke ɓata mana rai don mu ga ta ina za mu iya kawo gyara. Elon Musk haɗarin da duniya ta shiga na gurɓacewar yanayi yana damunsa don haka ya zage dantse yana ta aiki tuƙuru dan ganin an samar da wata duniyar da mutane za su iya rayuwa, sannan ita ma wannan ɗin a ga ya za’a kakkaɓeta daga wannan yanayin.

    Steve Jobs hankalinsa yana tashi in ya tuna girman Computer ya kai girman ɗaki, don haka ya yi ta aiki dan ganin computer ta zama za a iya yawo da ita a hannu ko aljihu. Na kasance ba na jin daɗi irin yadda muke rayuwa, ilimi muna hango shi a can nesa, da nima na tsaya ina jiran gwamnati da shuwagabanni su yi wani abu a kai, amma daga baya na gane cewa ni ma fa akwai ta inda zan ba da gudunmawa, don haka na duƙufa da bincike da kuma yaɗa sakamakon binciken nawa cikin harshen da kowa zai gane don ya zama ilimin ya zo kusa da mu.

    Waɗannan su ne tambayoyin da za ka yi wa kanka kuma ka amsa su da kanka dan gano kai wane ne, babu amsar da ba daidai ba, duk abin da ka gano a nan to daidai ne matuƙar ka tambayi kanka da gaske. Abubuwan da ka kasa gano amsarsu sai ka ci gaba da bincike ta hanyar karatu ko sauraren masu karatu. Wasu kuma amsoshin daga makusantanka da abokananka ne za ka samu amsarsu, kada ka yi ƙasa a gwiwa wajen
    tambayarsu.

    Wasu daga cikin tambayoyin nan sun zo a littafin “Discover yourself na Scott Schewefel”, sai dai misalan da tsarin sun sha bamban, amma za a iya komawa can don ƙarin bayani.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

    Karanta Ya Ake Sanin Kai?

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ya Ake Sanin Kai?

    Ya Ake Sanin Kai?

    Kamar yadda na sha faɗa a rubuce-rubuce na, mutum haɗin gambiza ne na ƙwayar halittarsa, tarbiyyar da ya samu daga gida, iliminsa, abokanansa, wurin da ya tashi da gogewarsa a rayuwa.

    Su waɗannan abubuwan su suke sa wa mutum ƙauna ko ƙin wani abu, su suke taimakawa mutum wajen yanke shawara, su suke taimakon mutum kan zaɓinsa da ayyukansa, su suke haskawa mutum abubuwan da zai iya yi cikin sauƙi da waɗanda sai ya wahala.

    Wanda yake son ya san kansa yana da kyau ya fara daga ƙwayar halittarsa, domin ita take zuwa da duk wasu halayensa da ya gada a wurin iyayensa da kakanninsa. Don haka ni ma zan fara da shi, ina mai cirowa daga litattafan masana a wannan fanin.

    ❖ Ka San Yanayinka Na Halitta

    Shi yanayin mutum shi ne halayen da aka haife shi da su, waɗanda ya gada daga iyaye da kakanninsa. Kafin ya shiga duniya ya koyi wasu dabarun. Tim Lahaye (marubucin littafin why you act the way you do) ya kasafta mutane zuwa gida huɗu (4).

    Bibbiyu, biyun farko su ne mutane masu surutu da hayaniya (extroverts) sauran biyun kuma su ne shiru-shiru waɗanda ba su cika shiga mutane ba (introverts). Zan kawo dukkanin kashi huɗun haɗi da rauni da ƙarfin kowanne, ina mai cirowa daga wannan littafin.

    SANGUINE

    A ɓangaren masu surutu akwai waɗanda ake kira “Sanguine”, waɗannan su ne irin mutane masu yoyon magana ɗin nan, ba sa iya riƙe bakinsu, duk inda suka shiga dole sai an san suna wurin, akwai su da haba-haba da mutane, ga su kuma ba wuyar sabo, ga saurin ƙulla abota. Ba su san jimami ba, kuma komai suna iya mayar da shi raha, sun yarda da tatsuniyar dawwama cikin farin ciki a rayuwa.

    Ƙarfinsu: suna da saurin sabo, sun iya ba da labari, ba sa gajiya da surutu, suna rayuwa a yanzu (tuna baya ba ya damunsu balle fargabar gaba), suna da nuna tausayawa da alhini kan abu marar daɗi na wani, suna nuna shauƙi kan komai, ga su da raha da kuma shiga cikin ayyukan sa kai dumu-dumu, saurin ƙulla abota, da fara magana in kun haɗu.

    Rauninsu: ba sa iya tursasa kansu su yi abin da ya dace, in ka ba su aiki da wuya ka ga sakamako yadda ya kamata, yanayinsu yana saurin canjawa daga walwala zuwa tausayawa, in ka shiga wani hali sai sun fi ka nuna jimami don haka ma ana iya zargin ko na ƙarya ne in ba a fahimce su da kyau ba, ba su da tsari, sun fi sauran nau’in mutanen girman kai, kuma cikin sauƙi suke samun kansu cikin yaudara, ƙarya da cutar mutane don su ɓoye rauninsu, sannan suna da ƙarawa komai gishiri (kambaba abubuwa).

    CHOLERIC

    Nau’i na biyu cikin masu surutu su ne “Choleric”, shi choleric bai kai Sanguine surutu ba, shi ma yana da saurin sabo da jama’a, shi ma’aikaci ne, yana da zummar cimmawa ko azama, yana zama jagora, yanke abin da zai yi ba ya masa wahala, haka ma yanke wa waninsa, yana wadatuwa da kansa, yana da buruka kuma yana tsara yadda zai cimma su.

    Ƙarfinsa: ƙarfin gwiwa, wadatuwa da kai, hangen nesa, duk abin da ya sa a gaba ana ganin ci gaba (progress), yanke shawara ba ya ba shi wahala, jagora ne, akwai shi da naci, ba ya jira, in ma ba ku yi ba zai yi da kansa.

    Rauninsa: ba ya nuna ƙawa zuci/motsin rai (emotion) dan haka bai cika nuna tausayi ba, yana ganin komai zai iya yi da kansa ko ba taimako, yana danne na ƙasa da shi da musu kama-karya, ya iya ƙeta, bai cika yafiya ba, yana da saurin fusata dan haka ma yake yawan faɗa da mutane, kuma ya iya cin fuska da baƙar magana, tunzura mutum ma yakan iya sa shi nishaɗi.

    MELONCHOLY

    Nau’i na gaba wanda shi ne na farko cikin mutane shiru-shiru shi ne meloncholy, waɗannan su ne irin mutane ma su basira ɗin nan, wanda kowa yake mamakin baiwarsu, akwai su da lissafi, sadaukar da kai, da son ganin komai ya cika ɗari bisa ɗari 100%. Ba su da saurin ƙulla abota amma in suka ƙulla abota da kai ba za su ci amanarka ba, yanayinsu yana saurin canzawa dan haka sun fi duk sauran saurin shiga damuwa.

    Duk da ba su da surutu amma in suka samu wuri za ka rantse ba su ba ne (ko da kuwa a gaban kyamara ne ko wurin wani taro). Akwai su da tattali da rowa, in an ɓata musu
    rai suna da fushi amma ba kamar choleric ba, su a zuci za su cigaba da tafarfasa dan haka suna iya ɗaukar fansa ma.

    Ƙarfinsu: ‘ƴan baiwa ne, akwai su da basira, suna da lissafi, suna son ƙyaleƙyale, suna iya tursasa kansu su yi abin da ya dace, suna da zurfin tunani da tsari, ba su cika son hayaniya ba, kaɗaici yana ba su damar zurfafa tunani, ba su cika yin raha ba saboda komai gaske ne a wurinsu(da muhimmanci suke ɗaukarsa), suna da baiwar ƙirƙira da bincike, duk aikin da suka sa a gaba sai sun ga ƙarshensa, sun fi sadaukar da kansu kan abin da mutane za su amfana ko da su suna cutuwa.

    Rauninsu: saboda zurfin tunaninsu cikas suke fara hangowa game da komai da za su yi, caccanzawar yanayinsu ya sa suna saurin shiga da kuma daɗewa a damuwa, saboda suna son yin komai ɗari bisa ɗari (100%) ya sa ba a cika burge su ba, su da kansu ma suna barin ayyukan da suka ga ba za su cika yadda suke so ba, ba sa shiga mutane, suna kallon rayuwa a yadda ya kamata a rayu ba a yadda take a zahiri ba, basirarsu ta sa suna da saurin zargi da munanan tunani kan abubuwa, suna da saurin kushe abu
    tare da caccakar abin da bai kai mizani ba a ma’auninsu.

    PLEGMATIC

    Kaso na ƙarshe su ne plegmatic, su waɗannan shiru-shirunsu har ya fi na meloncholy domin ba wani shauƙi da za su samu kan su a ciki da zai sa su zama ma su surutu. Da wuya ka ga sun yi fushi ko an ɓata musu rai, suna da mugun sauƙin kai don haka sun fi sauran daɗin zama, suna da kakaci amma ba su cika dariya ba ko da sun yi kakacin, ba sa wuce iya abin da aka sa su, ba su cika son ɗaukar nauyin komai ba, sun fi jiran rayuwa ta zo ta same su.

    Ƙarfinsu: nutsuwa da rashin hayaniya, suna da sauƙin kai da daɗin sha’ani, za ka iya dogara da su, sun iya sasanta mutane, suna da tsari, akwai su da kakaci, suna kallon rayuwa a zahiri, ba sa yin abu ba tare da tunani da kuma kyakkyawan tsari ba, ba sa fara aiki da kansu amma in dai an sa su sai sun kammala shi, suna da son tsafta, ba su cika shiga sha’anin mulki ba, amma duk lokacin da aka zaƙulo su aka ba su mulki, suna yin mulki da ƙwarewa ta ban mamaki.

    Rauninsu: ba sa iya zaburar da kansu, suna da ganda, suna da son kansu, akwai su da rowa da tsoro, suna da yawan damuwa da zullumi kan abubuwa (gujewa ɗaukar nauyi yana farautarsu), ba sa iya saurin yanke mai za su yi balle su yanke wa wani, kullum cikin ƙoƙarin kare kansu suke daga cutuwa ko asara dan haka da wuya su ɗauki kasada, suna da turjiya da tawaye, za ka iya musu bayanin mai kake son su maka, su yi kamar sun yarda amma da sun juya baya su yi a yadda suke so.

    Tim Lahaye bai tsaya a iya kasa mutane gida huɗu ba, ya ƙara bayani da cewa kowanne mutum haɗin gambiza ne na kashi biyu cikin huɗun, kowa ya haɗa ɓangare biyu amma ɓangare ɗaya yana iya fin rinjaye, akan samu ma su haɗa uku amma su suka fi ƙaranci, dan haka yace mutane za su iya kasuwa gida goma sha biyu (12).

    A taƙaice dai kai tsaye mutum ba zai iya gane wanne yafi rinjaye a tattare da shi ba, amma daga bayanan da suka gabata zai fuskanci inda ya fi karkata in ya zauna ya nazarci rayuwarsa. Abu na gaba da zan ƙara shi ne, su waɗannan ɗabi’u na halitta koyaushe suna tare da mutum har ƙarshen rayuwarsa domin gadonsu ya yi, amma
    iliminsa, tarbiyyarsa, imaninsa da aƙidunsa su suke mayar da shi mutum.

    Dan haka yana daga cikin amfanin gane ƙarfi da rauni na halitta mutum zai san ina zai karkata a rayuwa, sannan zai san waɗanne halayya ne zai zama a ankare da su dan kar su dinga ɓata masa hulɗa da jama’a. Misali, sanguine dole ya yi aiki a kan rashin iya sauraren mutane, ya koyi kama bakinsa ya ji suma me za su ce, choleric dole ya koyi dena yin ƙarfaƙarfa da danne na ƙasa da shi, saboda wannan zai sa su daina ganinsa da
    ƙima.

    Meloncholy dole ya koyawa kansa kyakkyawan tunani kan abubuwa, in ba haka ba basirar ta sa ba za ta masa amfani ba, phlegmatic sai ya koyi zaburar da kansa ko zama wurin da za a dinga yawan zaburar da shi in ba haka ba zai tsinana komai ba a rayuwarsa. Wannan raba mutane da Tim Lahaye ya yi ba lallai ya zama cif-da cif ɗari
    bisa ɗari (100%) ba amma a cikin duk rabe-raben da ake yi ana ganin cewa wannan na san ya fi tattara kowa da kowa.

    Manzon Allah tsira da aminci su tabbata gare shi ya ce “ Allah ya halicci Annabi Adamu daga wata damƙa da ya yi daga ƙasa (a wurare mabambanta), don haka ‘ƴan’adam an halicce su a gwargwadon haɗe-haɗen ƙasar. Sai ya zamto a cikin mutane akwai ja, akwai fari, akwai baƙi akwai kuma tsaka-tsakin dukkaninsu, akwai mai kyan hali, akwai mai munin hali, akwai mai sauƙin lamari, akwai mai wahalar sha’ani” (Abu dawud da Tirmizi, kuma sun ce hadisi ne kyakkayawa).

    Akwai wani jan hankali, ko da ka ga halin wani da ka sani kada ka yi gangancin faɗa masa ko da kuwa abokinka ne, domin in ya ga raunin irin wannan mutumin ba zai yafe maka, kuma da wahala ka iya gamsar da shi cewa ba iya bayanin ba kenan, dan haka gara ka bar shi ya gano da kansa in yana da buƙata, sai a kula.

    ❖ Ta Ya Zan Gano Kaina Daga Wannan Rabe-raben?

    Kusan komai da muke yi ya dogara ne da irin tunanin da muke yi, shi kuma tunani ba komai ba ne face tambaya da amsa, tambaya ce kake yi wa kanka a zuci kuma kake amsa ta da kanka a matsayin tunani, don haka yana da kyau ka dinga yi wa kanka tambayoyi ma su kyau.

    Da farko abin da za ka fara tambayar kanka shi ne, ina cikin ma su surutu ko ba na ciki? Idan ka san kana da yawan zuba a ko ina to kana cikin ma su surutu kenan dan haka za ka zama kana tsakanin Sanguine da Chloric. Daga nan sai ka sake tambayar kanka wanne irin surutu ne da ni? Ina hana sauran mutane magana saboda surutuna ko kuwa ina ɗan sararawa su ma su yi? Ina da tausayi in ana ba da labari ko wani ya shiga wani hali ko kuwa ba ruwa na? ina da son girma da nuna iko ko kuwa?

    Idan amsarka ta zama e a tambayoyi biyun farko, ta zama a a, a tambaya ta uku akwai yiwuwar ka zama sanguine, saɓanin haka kuma choleric. Idan dukka e ne ko dukka a a kuma wataƙila kai gamayyar biyun ne. Idan kuwa ɓangaren shiru-shiru kake za ka iya farawa da tambayar kanka ko kana son komai ya zama ɗari-bisa-ɗari? Ka iya lissafi? Kana da zurfin ciki da kawaici? Kana nuna halin ko in kula a kan komai?

    Tambayoyi biyun farko ɗabi’un Melancholy ne, biyun ƙarshe na Phlegmatic, idan e ne amsarka a kashin farko a a a kashi na biyu ka zama Melancholy kenan, saɓanin haka kuwa Phlegmatic. A lura, kamar yadda na faɗa a baya, za ka iya samu amsoshinka duk su zama e ko duk a a, wannan alama ce da ke nuna duk ka haɗa bangarori biyun.

    Ta yiwu kuma ka ga wasu halayenka sun faɗo a gidan ma su surutu, wasu kuma a gidan marasa surutu, in haka ta faru sai ka sake duba sauran abubuwan da suka gabata a bayanin rauni da ƙarfi dan ka ga inda kafi karkata. Bayan ka gano gidan da ka faɗa a wannan kashe-kashen sai kuma ka amsa waɗannan tambayoyin da za su zo a babi na gaba.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

    Karanta Amfanin Sanin Kai

    Edita@rumasau-kallamu

  • Amfanin Sanin Kai

    Amfanin Sanin Kai

    Kafin na yi nisa cikin wannan littafin, yana da kyau na fara kawo kaɗan daga cikin amfanin sanin kai ga kowanne mutum da yake da mafarkin rayuwa mai kyau.

    ❖ Sai Ka San Kanka Za Ka Ci Gaba

    Babu wanda ya zo duniya da sani, kowa a gidan duniya ya san duk abin da ya sani. Haka nan babu wani da yake samun ci gaba sai ya ci gaba da neman sani, duk wanda ya tsaya da neman sani daga nan rayuwarsa take ƙarewa.

    Za ka yi mamaki idan na ce da kai ‘ƴan gargajiyar da muke gani a yanzu masu ilimi ne a zamaninsu, sun ƙi yarda su karɓi ilimin sabon zamanin da suke ciki ne ya sa ake musu kallon ‘ƴan gargajiya. Haka duk wanda ya ƙi ci gaba da neman ilimi zai zama a zamanin gaba.

    Mene ne alaƙar ci gaba da sanin kai? Sai ka san kai wane ne da matakan da ka taka na ilimi kafin ka san inda za ka ɗaura. Wanda ya san bai iya turanci ba misali, ba zai yi karambanin karanta littafin turanci mai wahala ba, in kuwa zai karanta da wuya ya tsinci wani abu. Inda iliminka ya tsaya daga nan za ka ɗaura in ka san kanka, in ba ka san kanka ba kuwa za ka iya kamawa daga ko ina sai abu ya yi nisa ka ga ashe akwai wani giɓi a baya da ka baro.

    Sanin kai wane ne zai haska maka wuraren da kake da rauni, da wuraren da
    Allah ya maka baiwa, hakan zai taimake ka ka mayar da hankali wajen inganta baiwarka sama da ƙorafi a kan gazawarka. Wanda ya mayar da hankali kan inda baiwarsa take shi ne rayuwarsa take ci gaba ba wanda yake ta faɗi-tashi da rauninsa ba.

    Hakan kuwa ba lallai ya zo da mamaki ba saboda ƙa’idar ita ce: duk abin da aka mayar da hankali kansa shi ne yake ƙara girma da haɓaka.

    ❖ Za Ka Dena Haɗa Kanka Da Wasu

    Muna rayuwa a wani zamani da bayanai suka yawaita, abubuwan da muke karantawa, kallo da saurare ba ƙaramin tasiri suke mana ba a rayuwa, don haka muke shafe shekaru ma su tsawo a rayuwarmu muna kamanta kanmu da wasu, muna ganin cewa mu ma ya kamata mu yi rayuwa irin yadda suke yi, har ma mukan shiga damuwa a dalilin hakan.

    Wanda ya san kansa ba zai tsaya damuwa da kwatanta rayuwarsa da ta kowa ba, ya san me yake so, ya san ina zai je, ya san kuma hanyar da zai kama domin isa wurin, to yaushe zai tsaya tunanin wane ba haka yake rayuwa ba? Sanin kaina ya taimaka min sosai wurin rayuwa irin wacce ta dace da ni, zan ga mutane suna yin abubuwa, amma saboda abubuwan ba su shalle ni ba, ba na fatan na zama su, ina so ni dai kawai na fi yadda na ke a jiya.

    ❖ Za Ka So Kanka

    Son kai yana daga cikin abubuwa mafiya wahala a wannan zamanin, mutum ya ji yana ƙaunar kansa a yadda yake ba tare da jin haushin gazawarsa ba. Yana daga cikin dalilin da ya sa malaman tarbiyya suke ba wa iyaye shawarar su dinga nuna wa yaransu ƙauna, yaba musu in sun yi abin kirki, yaba musu a cikin mutane in sun yi bajinta, ba su ƙwarin gwiwa, rashin gwale su ko disga su, neman shawararsu da ba su dama su yi wasu
    abubuwan da kansu (Dr. Aisha Hamdan: Nurturing Eeman in children).

    Wanda ba ya son kansa ba zai taɓa tsinana komai ba, zai cika kansa da tunanin gazawarsa da rauninsa dan haka sai wannan ya zama masa matsala. Wanda ya san kansa ya san wuraren da Allah ya fifita shi a kan sauran mutane dan haka zai gode masa kuma zai cigaba da aiki tuƙuru a wannan fannin. Haka nan kuma zai san wuraren da yake da rauni, don haka zai dinga taka-tsantsan a wannan ɓangaren.

    ❖ Za Ka San Abokanka

    Zaɓar aboki wani ɓangare ne mai wahala a rayuwa musamman ga mutane shiru-shiru irina, ba mu da saurin ƙulla abota. Amma duk da haka duk lokacin da muka san kanmu muna samun sauƙi wurin zaɓen aboki. Aboki wani jigo ne na rayuwa, ana tasirantuwa da shi matuƙa, dan haka ake so mutum ya yi taka-tsantsan wurin zaɓar abokai.

    Misali, a sanin da na yi wa kaina tunani ya fi aikina yawa, zan daɗe ina tunanin abu har sai na gano ba zai yiwu ba sai na watsar tun kafin na fara, da na ƙulla abota da Mallam
    Bahaushe wanda shi kuma yana aikin yana tunanin a lokaci guda, sai ya zama na tasirantu da shi na koyi haɗa dukka biyun ni ma daga gare shi.

    Wataƙila da ba mu ƙulla abota ba da wannan littafin ma yana nan zaune cikin tunanina har yanzu. Sanin kanka da sanin manufarka zai sauƙaƙa maka wannan ɓangaren na
    rayuwarka, za ka yi abota da wacce ta ku ta zo ɗaya, za ka yi haɗaka da wanda za ku ƙarfafi raunin juna, za kuma ka ci gaba da mutunci da sauran mutane, domin ƙa’idar dama ita ce “ba a ce sai kowa ya zama abokinka ba, amma za ka iya yin mutunci da kowa”.

    ❖ Za Ka Koyi Yi Wa Mutane Uzuri

    Wanda ya san kansa yana saurin sanin cewa mutane kowa da yanayin halittarsa, yadda yake ba haka kowa yake ba, kuma yana lura ya gane ya mutane suke, hakan yana taimakonsa wajen yi musu uzuri.

    Kafin na samu haske kan ni wanene wannan yana daga cikin ɓangaren da ya fi wahalar da ni, sai in kasa gane me yasa mutane suke abu iri kaza, ko meyasa suke son su ga ina yin abu iri kaza, ko meyasa su ba sa lura da kaza da kaza.

    Wannan Ilimin yana daga cikin abubuwan da suka ɗaga darajar Ma’aiki mai tsira da aminci kan sauran shuwagabannin duniya. In kana bibiyar tarihinsa za ka ga yana bambance sahabbansa ko wurin sanya su aiki yana mai la’akari da yadda suke. In ana buƙatar zafi ba ya neman sayyadina Abubakar, sayyadina Umar yake nema, haka nan in ana buƙatar wata maslaha ko wani abu na sauƙin kai, ba ya neman sayyadina Umar sai dai ya nemi sayyadina Abubakar. A rubuce-rubucena na “Iya ruwa…” na kawo
    makamancin wannan misalin.

    ❖ Za Ka Ɗauki Alhakin Rayuwarka

    Sanin kai yana ragewa mutum yawan ƙorafi da ɗaurawa wasu lefin matsalarsa. Wanda ya san kansa zai gwammaci ya mayar da hankali kan abin da zai amfani rayuwarsa sama da ba wa kansa hanzari ba gaira ba dalili. Kai ne ya kamata ka zama a kujerar mai tuƙi a motar rayuwarka ba a kujerar mai zaman banza ba (Sean Covey: 7 habits of highly effective teens).

    ❖ Rayuwarka Za Ta Yi Sauƙi

    In ka san kanka komai zai zo maka da sauƙi. Misalin wanda ya san kansa kamar misalin me yin bulaguro ne, ya san inda za shi, ya san a ina zai samu mota, ya san wacce hanya za a bi. Idan ka san kanka komai za ka san irin na ka, tun daga kan abinci, tufafi, abun hawa, wasa, kai hatta kallo da zuwa wuraren nishaɗi, za ka je ko aikata abin da bai ci karo da kai waye ba ne, balle ka samu ƙunci.

    Za ka rage damuwa da kallon da mutane za su maka don kai ka san abin da ba su sani
    ba game da kanka (kamar yadda na yi tsokaci a baya, akwai lokacin da dole sai ka saje da su don maslaha).

    Kana buƙatar wani cikin waɗannan abubuwan a rayuwarka? In amsarka e ce to mu je zuwa, in kuwa ta zamto a a, ina mai ba ka haƙuri wannan littafin ba na ka ba ne.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

    Danna nan don karanta Ka Ɗauka Ka Sani

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ka Ɗauka Ka Sani

    Ka Ɗauka Ka Sani

    Gabatarwa

    Da sunan Allah mai Rahama mai Jin ƙai.
    Abin da za ka karanta mai yiwuwa ya iya canja maka rayuwa, yana da kyau ka samu wurin da babu kowa ka nutsu, ka kashe tv, ka kashe data, domin karanta wannan ɗan littafin a cikin cikakkiyar nutsuwa.

    Ba haka kawai na faɗa ba, ni ganau ne ba jiyau ba, na sha fama da abubuwa da dama a rayuwa, ga shi dai babu abin da na nema na rasa a gida, amma kullum ina ganin rayuwata tana shan bamban da ta sauran jama’a.

    Na daɗe ina yi wa kai na tambayoyi game da rayuwa, wasu daga cikin irin tambayoyin sun haɗa da:

    • Me yasa wasu mutanen surutu da shiga mutane ba ya musu wahala wasu kuwa yake musu?
    • Me yasa wasu sun gwammance su zama kullum suna su kaɗai wasu kuma ko da kuɗi ba za su iya ba?
    • Me yasa wasu duk abin da in dai a aji za a koyar ba abin da zai hana su ganewa wasu kuma sai an nuna musu shi ɓaro-ɓaro sun gani ko ma sun taɓa?
    • Me yasa wasu suke da saurin sabo da ƙulla abota wasu kuma sai an ja daga?
    • Me yasa wasu sun fahimci rayuwa da wuri wasu kuma har sun fara gangarawa amma ba su san inda suka dosa ba?
    • Me yasa wasu suke da naci, duk abin da suka sa a gaba sai sunga abin da ya turewa buzu naɗi, wasu kuma daga sun fara kamar ana mintsininsu suke bari?
    • Me yake sa mutum ya ji ga shi dai yana rayuwa kuma yana cimma abubuwa amma ba ya ganin ma’anar rayuwar ta sa, wani da bai kai shi ba kuma yana masa ganin ya kai wani mataki har yana sha’awarsa?

    Ba iya tambayoyin ba kenan, wannan kaɗan daga cikinsu ne, in kai iri na ne mai yawan zama yana ƙoƙarin gano wani abu ba mamaki ka taɓa yi wa kanka wasu daga cikin tambayoyin nan. Ko ka samu amsa ko ba ka samu ba, ni dai abin da nake fahimta shi ne, akwai lokacin da mutum yake matuƙar buƙatar ya san kansa, sanin kansa ne zai ba shi damar iya amsawa kansa mafi yawancin tambayoyinsa.

    Wasu tambayoyin ko da ka tambayi makusantanka, ko wasu da kake ganin sun fi ka, za ka ga ba za su ba ka amsa a yadda kai kake kallon abun ba, domin yawancin jama’a suna magana ne suna masu la’akari da yadda su suke.

    Wannan dalilin kaɗai zai iya hana abin da za su faɗa ya iya gamsar da kai. Amma idan kai ma ka san kanka fa? Za ka san a yadda za ka musu tambayar, kuma za ka fahimci a yadda suka kalli abun sannan ka alaƙanta amsarsu kai ma da yanayinka.

    Ni ba masanin kimiyya ko halayyar ɗan Adam ba ne, ni mai sha’awar rubuce-rubuce ne kawai, a wannan ɗan littafin na yi ƙoƙarin tattara abubuwan da na ci karo da su a halin binciken da na yi ta yi game da sanin kai na.

    Tambayoyi da dama na samu amsarsu, waɗanda ban samu ba kuma ina ci gaba da nemansu. Jin daɗin da nake yi a yanzu da na fahimci kaina ya wuce misali, haka kawai don mutane suna yin abu ba zai sa ni na yi ba, in ba ni da buƙatarsa (wannan ba ya kore siyasa ta rayuwa, in ka tsinci kanka a wurin da kowa yake da jela kai ma ka samu tsumma ka ɗaura, in ba haka ba za a dinga kallonka a matsayin barazana har a iya maka illa ta inda ba ka yi tsammani ba).

    Abubuwan da na ke sa ran za ku ƙaru da su a wannan ɗan littafin ga su kamar haka:

    • Meyasa ba ka san kanka ba
    • Muhimmancin sanin kai
    • Dabarun sanin kai
    • Amsa wasu tambayoyi da za su bayyana maka kanka
    • Muhimmancin samar da manufar rayuwa
    • In ba za ka iya sanin kanka ba to ka yi…

    Abin da na ke buƙata daga kai mai karatu shi ne wannan littafin na rubuta shi ne a matsayin wata ƴar ƙaramar tunatarwa ga kaina da sauran mutane da nufin ya yaɗu a tsakankaninmu mu ma su jin yaren Hausa. Don haka in ka samu kuma ka karanta kada ka bar shi a zaune haka nan, ka turawa abokananka ko da guda 3 ne domin su ma su amfana.

    Idan ka karanta wannan littafin ba ka ƙaru da komai ba, na bar “link” na whatsapp ɗina a kowanne shafi na littafin, za ka iya min magana don bayyana min kura-kuren da ke cikin littafin, da kuma bubuwan da suka sa littafin ya gaza wurin amfanar da kai.

    Idan ka ƙaru sosai kuma kana sha’awar cigaba da samun rubuce-rubuce na, ka ziyarci shafinmu na fesbuk da yake saman kowanne shafi domin mu ci gaba da ƙaruwa da juna.
    Allah nake roƙo ya amfanar da duk wanda wannan littafin zai isa gare shi, sannan ya ba mu ikon yin aiki da abubuwan da suke ciki ni da ku gaba ɗaya.

    Ka Ɗauka Ka Sani

    Sau da dama in na fito daga gida zan ga mutane a zazzaune suna hirar duniya ko a ƙarƙashin bishiya ko a kan wani dakali ko benci. Cikin irin hirarrakin nan da suke zai yi wuya ka ji babu labarin wani a ciki.

    Misali idan hirar ƙwallo suke za ka ga sun san komai game da gwaninsu, sun san haihuwarsa, garinsu, iyayensa, yaushe ya fara buga tamola, ƙungiyoyin wasannin da ya bugawa wasa, kofi nawa ya taɓa ɗauka, yanzu a wacce ƙungiya yake, nawa ne albashinsa da sauransu.

    Haka nan in hirar siyasa suke yi, komai na wannan ɗan siyasar sun sani, in hirar malamai ce ma haka, kowanne hali suke ciki suna sane. Haka nan idan ‘ƴan wasan kwaikwayo ne ko ma su sarauta. Abun ba ya tsaya a iya shahararrun mutane ba ne kaɗai, har waɗanda ake unguwa ɗaya da su, waɗanda suka kai, da waɗanda ba su kai ba za ka ga duk an san komai nasu.

    Wani abun ban mamaki shi ne da za ka kalli wannan mutumin shi a karan kansa, ta hanyar nazarin halayyarsa za ka fahimci ya san kowa ban da mutumin da ya fi cancanta ya sani, wato kansa.

    Ba haka kawai mutane suke nuna halin ko in kula da sanin kansu ba, saboda daɗewar da suka yi da kansu ne ya sa suka ɗauka sun san kansu, don haka suka mayar da hankalinsu kan sanin sauran mutanen duniya.

    Wannan kuwa ba abun mamaki ba ne, domin bincike kan bincike na masana ya tabbatar da cewa mutum halitta ce da dole sai ta yi imani da wani abu, in ba ta samu abun da za ta yi imani da shi ba sai ta ƙirƙiro abubuwa, ko ta dinga zato da tsammani kan wani abu, sannan ta mayar da zaton nan gaskiya a zuciyarta (Andrew Newberg: why we believe what we believe).

    Wataƙila wannan dalilin ya sa mutane da yawa suke ganin sun fahimci kansu, idan kana/kina cikin mutanen da suke ta ƙoƙarin ganin sun fahimci kansu amma sun rasa mafita saboda ƙarancin bayanai ko taimakon da zai haskaka musu su waye, to wannan littafin na ka/ki ne.

    Idan kana cikin mutanen da sun riga da sun ɗauka sun san kansu, amma hakan bai taimake ka wajen tsinana wani abu a rayuwa ba, yana da kyau ka ɗan duba wasu shafuka kaɗan cikin littafin nan. Idan ka fahimci kanka, kuma ka gamsu haka kake amma kuma ka kasa yin komai da rayuwarka duk da haka, akwai shawarwarin da zan kawo a gaba da za su taimaka maka. Sai a biyo ni domin shan karatu.

    Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

    Danna nan don karanta Sababbin Karin Maganar Hausa

    Edita@rumasau-kallamu