Tag: yadda ake

  • Tarihin Garin Rimin Gado

    Tarihin Garin Rimin Gado

    Akan yi wa garin Rimin Gado kirari da cewa “Rimin Gado garin ‘yan lalle”, silar hakan kuwa shi ne, Allah ya ba wa garin yalwa ta bishiyoyin lalle, wanda a zamanin baya ya kasance itace mai daraja wanda mutane ke rububin neman sa domin yin amfani da shi a matsayin sinadarin tsaftace jiki da magani da sauran su.

    Wannan gari, a zamanin baya, ya zamo kasuwa matattarar fatake inda mutane ke niƙo gari daga mabambantan sassa domin siyen lalle da sauran hajoji. A binciken da Mallam Muhuyi Magaji Rimin Gado ya yi, ya sanya kafuwar garin Rimin Gado da kimanin shekaru 300 da suka gabata.

    Kafin zamowar Rimin Gado gari, inda Rimin Gado yake a yanzu ya kasance (zango ne) wurin saukar matafiya ne masu kara-kaina tsakanin birnin Kano da biranen da ke yamma da ita misalin Sokoto.

    KAFUWAR RIMIN GADO

    An ce akwai wani mutum mai suna Magili, mabaraci ne, wanda ya taso daga Degel; wani ɗan ƙaramin gari da ke jamhuriyar Nijar a yau zuwa inda garin Rimin Gado yake, don haka ana iya cewa shi ne asalin kafuwar wannan gari.

    Bisa al’ada ta mabarata, sukan samu gefen turbar da mutane ke shigewa su fake suna addu’a ko zikirai ko waƙoƙin nasiha ga matafiya da makamantansu, da nufin neman sadaka daga masu shigewa. Magili ya gina gadon ƙasa a inda garin Rimin Gado ya ke a yanzu, a gefen turbar da matafiya ke wucewa zuwa birnin Kano, a kan wannan gado yake zama yana bara a ko-da yaushe.

    ASALIN SUNAN RIMIN GADO

    An ce Magili, wanda yake zama a kan gadon da ya gina na turɓaya yana bara da rana sai kuma ya kwanta bacci idan dare ya yi, ya samo ƙwanson Rimi da ya tattara a matsayin matashin kai wanda yake ɗora kansa yayin bacci.

    A kwana a tashi sai ‘ƴa’ƴan rimin da ke cikin ƙwanson ya rinƙa zuba daga gadon nasa zuwa ƙasa, har kuma aka yi sa’a tsiron bishiyar rimi ya fito a wajen wanda daga bisani ya girma ya zama bishiya gagaruma wadda ake zama don hutawa ko don gudanar da cinikayya a ƙarƙashin ta.

    Daga nan ne fa aka samo sunan ‘Rimin Gado’ wajen nuni da bishiyar Rimin da ya girma a ƙarƙashin ko a kusa da gado. Sannu a hankali wannan wuri ya haɓaka ainun tare da zamowa dandalin ya-da zangon fatake masu son shiga Kano waɗanda akasarin su suke tafiya a ƙafa, ko a jakuna da sauran ababen hawan lokacin daga birane irin Alƙalawa, Sokoto da sauran su.

    TURBAR KANO TA SASHEN RIMIN GADO

    Wannan turba ta soma ne daga ƙofar Kabuga wadda take a yammacin kano, ta keta ta shacin Janguza, ta wuce ta Yalwan Ɗan ziyal har zuwa wannan gari na Rimin Gado. Daga nan kuma sai ta cigaba da nausawa sashen yamma har ta keta Gwarzo zuwa wasu sassan ƙasar Katsina.

    Kuma kamar yadda tarihi ya nuna, ta wannan turbar ne aka rinƙa samun sadarwa a tsakanin biranin Kano da biranen da suka kafu a zamanin baya waɗanda a yanzu suke cikin jihar kanon kanta, da Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi har zuwa sassan ƙasashen Mali da  Nijar. Kuma haƙiƙa, ba iya Rimin Gado ba, akwai garuruwa da dama da kafuwar su ya samu ne daga albarkar wannan turba.

    Danna nan don karanta Tarihin Garin Gurin Gawa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Danya (Molluscum Contagiosum) Take

    Yadda Danya (Molluscum Contagiosum) Take

    Waɗannan ƙurajen da kan bayyana a fuskar manya da ƙananan yara wanda ake kira da “Molluscum Contagiosum” a kimiyyance, inda da Hausa akan kira su da DANYA, ƙuraje ne na larura da ƙwayar cutar Virus rukunin waɗanda ke sa cutar ƙyandar biri da cutar cin zanzana ke haddasawa, wato (monkey pox & small pox).

    Abinda ke bambance su da sauran ƙuraje shi ne lotsewar da tsakiyar ƙurjin ko tsirorin ke da shi. Sannan wani lokacin bayyanar wannan ƙurajen da yawa a jika musamman ga manya wanda suka san suna ‘ƴan tsalle-tsalle tsakanin abubuwa, toh fa hakan ka iya zamowa alamar farko da ke nuna mutum na ɗauke da cutar ƙanjamau.

    Kuma rashin zuwa a tantance shi ka iya sa su rikiɗe mutum ya yi karo da cutar cancer a fata wato “Kafosi sakoma” amma ga masu HIV/AIDS kurum. Shi yasa ko ba wannan ba, kar wanda yasan yana da HIV ya yi wasa da wani canji da zai gani a fatar sa. 

    • Ana iya ɗaukar su daga wani zuwa wani ta hanyar;
    • Musayar soson wanka da me su,
    • Ko taɓa ruwan ƙurjin a zo kuma a taɓa jiki ba tare da an wanke ba,
    • ko haɗa kayan sawa da me su,
    • ko kwanciya a gadon me shi,
    • ko tayar da kai da pillow ɗin da me su ke ta-da kai.

    Da dai duk wata hanya da ake iya samun cuɗanya da fatar me ɗauke da su. Na san wasu ƙurajen kan ba su sha’awa musamman idan sun fito a saman fatar ido musamman Mata, toh amma fa wannan ba abin so ba ne. Galibin wanda za ka gani da su alama ce ta ba su da ingantacciyar garkuwar jiki (Good immunity). 

    MAGANINSU SHI NE

    • A wasu wanda suke da garkuwar jiki me ƙarfi ko da sun kamu da su watanni 4 zuwa 6 a neme su a rasa ba tare da an yi maganin komai ba, a wasu kuma suna iya jimawa fiye da shekara ɗaya zuwa huɗu kafin su tafi.
    • A wasu kuma takan kai ga sai an ba su magungunan shafawa kafin su tafi.
    • A masu cuta me karya garkuwar jiki (HIV/AIDS) dole sai sun mayar da hankali a kan maganin su, ko kuwa in sabbin gano ciwon ne sai an ɗora su a kan magani akan iya warkar da ƙurajen danyar ko da kuwa an yi maganin danyar ba za ta tafi ba ba tare da maganin ƙanjamau ɗin ba.
    • A wanda al’amarin ya yi ƙamari sai an kai ga ciccire musu ita ta hanyar amfani da na’urar daskarar da su da sinadarin sanyi a reɗe su (cryotherapy), ko kuma na’urar ƙonewa tare da yankewa wato (electrocautery).
    • Galibi dai jinkirta magance su bai haddasa wata mummunar matsala, sai dai barinsu ba tare da ɗaukar mataki ba na iya sa su yi yawan da za su lulluɓe fuska ko su ɓata jiki baki ɗaya, kuma mutum ya zamto ya riƙa cutar da wasu musamman ƙananun yara da kan so hawan jikin mutane.
    • Hakanan kaucewa haɗa kayan sa wa, Gadon kwanciya, robar wanki ɗaya, runguma, musayar matashi da me su shi ma hanyar kare kai ne idan ana tare da me su.

    Karanta Illolin Sinadaran Samun Ƙwazo Da Kuzari

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Haƙƙin Maƙwabci

    Waƙa Mai Taken Haƙƙin Maƙwabci

    1. Allahu sarki ka ban sani,

    Da zai yi amfanuwa ga ni,

    Cikin dare har ma da wuni,         

    Tsare ni aikin take sani,

    Ina ta roƙon ka mai niya.

    2. Ƙaro salati ga Ahmadu,

    Sidi masoyinmu sarmadu,

    Fiye da ‘ya’ya da walidu,   

    Shumagaba namu Rashidu,

    Wannan da ya zo da shiriya.

     

    3. Ya ɗan uwa zance zan maka,

    Bisa ga haƙƙin maƙwabtaka,

    Da malamai sun faɗa maka,        

    To ga ni zan jaddada maka,

    Don mu kiyaye shi bai ɗaya.

     

    4. Akwai maƙwabci na gun zama,

    Gidanka ga nasa hakka ma,

    Duk wanda ke layin da zama,

    Baya gaba dama hauni ma,

    Su ne maƙwabtanka ka jiya.

     

    5. Akwai maƙwabci na kasuwa,

    Wurin sana’a ke haɗuwa,

    Ko kuwa ofis ke gamuwa, 

    Zama na mota domin zuwa,

    Wani gari yayin tafiya.

     

    6. Haƙƙin maƙwabci ko kafiri,

    Ne ba shi za ai ba jinkiri,

    In ko musulmi ne na gari,  

    Haƙƙi na addini tun wuri,

    Ga na maƙwabta za a biya.

     

    7. In ko musulmi ne ɗan uwa,

    Na jika to ukku haƙƙuwa,

    Na musulumci na ‘yan uwa,

    Na uku haƙƙin maƙwabtuwa,

    Za a cika babu tawaya.

     

    8. Haƙƙin maƙwabci fa babba ne,

    Ba da shi yankin imani ne,

    Kada mu tauye ko ƙanƙane,       

    Wannan umarnin Manzonmu ne,

    Zuwa gare mu baki ɗaya.

     

    9. Ka so masa duk abin ƙwarai,

    Kamar da ka so wa kanka kai,

    Abin tsiya kar ka so garai,

    Kamar da ka ƙi gare ka kai,

    Cikin dare ko ko safiya.

     

    10. In ya buƙatu ka taimaka,

    Don ɗan uwa yake gu naka,

    Kai za ya farko sanar maka,       

    Kafin kiran ‘yan uwan jika,

    Da ke a can nisan tafiya.

     

    11. In ya yi cuta dubo shi yi,

    Ka nuna damo da tausayi,

    Gare shi ko da sartse ya yi,

    In ma da ɗan hasafi ka yi,

    Shi ne tafarki na shiriya.

     

    12. Kar kai gini mai tsawon bisa,

    Jikin katangar gida nasa,

    Iskar ƙwarai ka tare masa,

    Sai ka biɗi izini nasa,

    Kada ka soma in ya ƙiya.

    13. Sharar da ka yi ka tattara,

    Kada ka watsa ta gangara,

    Gaban gidansa ba hattara,

    Ko da kuwa shi zai haƙura,

    Cutar maƙwabci haramiya.

    14. Ka soya nama na raguna,

    Ko kuwa kaji da zabuna,

    Amma maƙwabcinka ka hana,

    Rabonsa ƙanshi ga hantuna,

    Cuta kake yi ƙazamiya.

     

    15. Kada ka kwana a ƙosashe,

    Shi ko maƙwabcinka busashe,

    Ya kwana yunwa za ta kashe,

    Dukkan tukwanensa ƙeƙashe,

    Kai kuwa kaji a jar miya!   

     

    16. Annabi ya ce “Bai so ni ba,

    Da ni ku san bai imani ba,

    Wanda ya kwan ƙoshe bai ji ba,

    Yunwa maƙwabci kwano gaba,

    Ya yi zugum babu lomiya.”

     

    17. Aro na kayan buƙatuwa,

    In ya biɗa sai ka basuwa,

    Manjagara tsani don hawa,

    Wuƙa in ya roƙi daddawa,

    A sam masa gishirin miya.

     

    18. Dukkan abin yin farin ciki,

    Idan ya samar kamar biki,

    Ka zam taya shi har kaɓaki,

    Ka yi masa in baƙin ciki,

    Ne ku yi tare ba wariya.

     

    19. Haƙƙin maƙwabcinka ne idan,

    Ya mutu to kan gaba ka zan,

    Wajen suturce jana’izan,

    Har fa a binne shi saliman,

    Zaman makoki kar ka ƙiya.

     

    20. Idan da hali ka tallafa,

    Wa su iyalan ɗa’am dafa,

    Ka ba su ko tsabar su dafa,

    Tanyon marayun ka duƙufa,

    Ba za ka taɓe ba duniya.

     

    21. Cutar maƙwabci mu hanƙure,

    Kullum mu yafe in yai kure,

    Dukkan haƙi nasa mu tsare,

    Laifinmu Allah zai kankare,

    Ran lahira mu yi dariya.

     

    22. Kada mu zam cutar sa muke,

    Ko da ko shi cutar mu yake,

    Aljanna ba shi wanda yake,

    Cutar maƙwabci ko a fake,

    Faɗarsa Manzo abin biya.

     

    23. Allahu kab ba mu juriya,

    Bisa zamn tare lafiya,

    Ba ce-ku-ce ba hayaniya,

    Mu zam game kai ba fariya,

    Amin mu zam shafa fatiya.

     

    24. Mai tsara waƙar ga Nasiru,

    Ahmad ko ko sha’iru,

    Wannan da ke koyon shi’iru,

    Ba mahiri ne ko baharu,

    Bisa ga waƙe ba kun jiya.

     

    25. Ran Juma’a ne na kammala,

    Waƙar maƙwabci don mu kula,

    Ga jalla sarki nai hamdala,

    Ya khaliƙina salli ala,

    Ɗaha da ya zo da gaskiya.

     

    Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.

    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Baƙar Sana’a

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ƙaddamar Da Manhajar Karin Magana Challenge

    Ƙaddamar Da Manhajar Karin Magana Challenge

    Wasa Mai Ilimantarwa Cikin Harshen Hausa

    Mun ƙaddamar da manhajar Karin Magana Challenge, wani sabon wasan ilimi da aka ƙirƙira domin taimaka wa mutane su fahimci karin magana na Hausa ta hanyar wasa da nishaɗi.
    Wasan yana bai wa mai kunnawa damar:

    1.Koyo da fahimtar karin magana
    2.Zaɓar ma’anar da ta dace
    3.Gwada ƙwaƙwalwa da basira
    4.Koyon darussan rayuwa ta hanyar hikima

    Yadda Karin Magana Challenge Ke Taimakawa Ilimi

    1. Ƙara Fahimtar Harshen Hausa: Wasan yana taimaka wa ɗalibai da masu sha’awar Hausa su fahimci karin magana da ma’anoninsu.
    2. Koyar da Hikima da Tarbiyya: Karin magana na koyar da gaskiya, haƙuri, ladabi, da basira.
    3. Ilimi Ta Hanyar Wasa (Game-Based Learning): Wasan yana sa koyo ya zama abin jin daɗi, musamman ga matasa.
    4. Kare Al’adu da Gadon Hausa: Yana taimakawa wajen adanawa da yaɗa al’adun Hausawa ga al’ummar wannan ƙarni da ma ƙarni na gaba.

    Yadda Ake Sauke (Download) Karin Magana Challenge App

    Karin Magana Challenge ba sai ka je Play Store ba. Ana iya sauke shi kai tsaye daga yanar gizo kamar app.
    Matakai:
    Buɗe wannan shafi a wayarka:

    https://karinmaganaapp.web.app
    Da zarar shafin ya buɗe, za ka ga: “Add to Home Screen” ko “saka app a waya”
    Danna Add / Install
    App ɗin zai shiga wayarka kamar sauran apps
    Za ka iya buɗe wasan kai tsaye daga Home Screen.

    Yadda Ake Kunna Notifications (Sanarwa)

    Domin samun sabbin karin magana, ƙalubale, da tunatarwa, ana buƙatar kunna notifications.
    Matakai:
    Lokacin da aka tambaye ka: “Allow Notifications?”
    Danna Allow
    Idan ba ka gani ba:
    Je ka zuwa Settings
    Buɗe Notifications
    Nemo Karin Magana Challenge / WikiHausa
    Kunna Allow Notifications
    Me Ya Sa Notifications Suke Da Muhimmanci?

    • Tunatarwa don yin wasa
    • Sabbin ƙalubale
    • Ƙarfafa koyon Hausa a kai a kai
      👉 Gwada, sauke, kuma ka kunna sanarwa a nan:
      https://karinmaganaapp.web.app
      Karin Magana Challenge – Ilimi cikin nishaɗi, hikima cikin wasa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Illolin Sinadaran Samun Ƙwazo Da Kuzari

    Illolin Sinadaran Samun Ƙwazo Da Kuzari

    Energy drinks wani rukunin Lemo ne me ƙunshe da tarin sinadarai masu ƙarfin gaske da ke iya hargitsa lissafin ƙwaƙwalwa. Yana ƙunshe da sinadarai irin su ‘kapen’ me matuƙar ƙarfi tare da wasu tarin sinadaran dakan shafe kwanaki ba tare da jikin mu ya iya tacewa tare da fitar da su ba cikin datti.

    Wannan lemon na kusanta duk wani me shansa ga hatsarin samun toshewa ko fashewar magudanar jini a cikin ƙwaƙwalwa dakan sa mutum ya bayyana da shanyewar ɓarin jiki wato STROKE.

    Sannan shansa na kusanta mutum ga hatsarin bugun zuciya wato doɗewa ko fashewar magudanar jinin da ke bai wa zuciya JINI Mayokadiyal infakshin. Ba iya nan ba kwai ƙwaƙƙwarar alaƙa tsakanin shan wannan lemon da ciwon ƙoda gami da cutar jeji wato CANCER.

    Energy drinks kan zo a mabambantan sunaye kama daga Lucozade, Predator, Fearless, Red bull, Monster, Boost, Power horse. Da sauransu, amma duk illar su guda. Lemo ne da ke sanya addiction shi yasa sai mutum ya yi da gaske in ya fara ratsa jikinsa in ba haka ba nan zai dauwama.

    Lemo ne da kamfanoni ke samar da shi da zummar a sha domin a sami kuzari’ sai dai sam ba Lemo ne na sha kullum kullum ba, hasali Lemo ne da ya dace in ma ya zamar maka dole shi ne ka sha guda ɗaya duk bayan sati ɗaya ko biyu, saɓanin mutanen da a rana za ka ji su kan sha biyu ko uku, ko ɗaya kullum-kullum.

    Matashi ne ɗan shekara 34 ya zo da ƙorafin ciwon ƙirji me tsanani, wanda ya zamto ya sami myocardial infarction ne ‘wato bugun zuciya, abinda ke da matuƙar wahala ka samu a matashi ko da kuwa menene, sai dai sam bai da wata sananniyar larura a jika. Babban abinda da muka iya samu “as Risk factor” shi ne frequent consumption na energy drinks ne ya jawo hakan, wanda hakan ke nuna lfyar sa ta gama taɓuwa.

    Don haka matashi idan kana aiki ka ji gajiya… Toh tsaya ka huta kurum, jiki na da limit, ba za kai ta aiki ba hutu ba kuma bayan ka gaji kace za ka sha wani sinadari don samun kuzari alhalin tuni jikin a gajiye yake

    Energy drinks nervous stimulant ne me ƙarfi da wasu sinadaran ma na tabbata an ɓoye su ba a bayyana ba, shi yasa a wanda suke so sensitive in suka sha wannan abin da yamma ko bacci ba sa iya da dare.

    Bana kashewa kamfanoni sana’a amma dai ku gane wannan lemon ba wai Lemo ba ne kaɗai. Kowa lafiya za ta yi wa daɗi barin me ita ne. A lura Matasa.

    Danna nan don karanta Yadda Warin Jiki Yake (Body Odour)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tarihin Garin Gurin Gawa

    Tarihin Garin Gurin Gawa

    Kamar yadda marubutan littafin ‘Urban Society ‘ Gist da Halbert suka faɗa, kuma kamar yadda yake game da asalin ita kanta wayewar, tushen kowanne birni kusan ya samo asali ne daga hijirar mutanen ƙauyuka.

    Birane su ne cibiyar hadar-hadar kasuwanci, tsaro, al’adu, ilimi da bincike. Don haka ya sanya mutanen karkara na kusa da na nesa, da ma wasu mutanen da ke wasu biranen da dama kan ziyarci birane domin samun mafakar tsaro, ko kasuwanci, ko samun ilimi ko cimma wani dalili na al’ada da ma sauran muradai walau ziyarar ta kasance ta wucin gadi ko kuma ta-din-din-din.

    Akwai ilimin tarihi mai yawa da mukan rasa yayin kawar da kawunan mu ga tafarkan da suke sadar da mutane zuwa waɗancan birane. Wannan kuwa ya haɗar da tarihin wasu muhimman abubuwa da aka taɓa yi ko kuma muhimman wurare masu dangantaka da biranen kansu.

    Sau tari a ƙasar Hausa mutane kan niƙi gari domin ziyartar wani birni amma sai su shantake a wasu wurare na kusa ko na nesa da biranen bisa wasu dalilai. Haka kuma a wasu lokutan, sauyawar yanayai kan tursasa mutanen cikin birane komawa makusanta ko manesantan garuruwa ko birane da zama.

    Garin Gurin Gawa na ɗaya daga cikin ƙauyukan da suka kafu a turbar kano. Hasashe ya nuna cewar mabanbantan mutane da akasarin su ƴan tafarki ne suka kafa garin tsawon lokaci da ya shuɗe. Garin yana kudu da garin kano, akan turbar da za ta shigar da mutum birnin kano ta ƙofar Ɗan Agundi (wadda aka sara a wajajen shekarar 1499AD). Don haka duk mutanen da suke son shiga kano daga yankunan Rano, Jos, sassan ƙasar Bauchi da makamantan su sai sun bi ta wannan turba.

    ASALIN SUNAN GURIN GAWA

    Akwai mabanbantan zantuka game da asalin sunan Gurin Gawa.

    1. Na ɗaya: Gurin Gawa daga Gurin Gawarwaki. An ce an samo sunan ne daga kasancewar wurin filin daga. Watau a zamanin yaƙi, da zarar kano ta samu labarin an tunkaro ta da yaƙi ta wannan shiyya, sai ta turo dakarunta ta jibge su a wannan wuri. Don haka a nan za a fafata yaƙi, anan kuma za a samu tulin gawarwaki bayan ƙarewar yaƙi.

    2. Na biyu: Gurin Gawa daga ‘Gurin-Ge‘: Wannan ra’ayin yana cewa an samu sunan ne daga wani Bafillatani mai suna Gurin-ge, wanda kiwo ya biyo da shi ta wajen har kuma dabbobin sa suka gano masa wani kwarmin ruwa, don haka ya mayar da wajen mazaunin sa, daga bisani ƴanuwansa fulani suka riƙa riskar sa da zama.

    3. Na uku: Gurin gawa daga Gurin da aka samu  gawar Kuyangar Sarkin Rano: An ce akwai wani rafi tsakanin Medile da Gurin Gawa wanda ake kira ‘Ci-kuyangi’, saboda yadda ya yi silar mutuwar kuyangi da dama a ciki har da wata amintacciyar kuyangar Sarkin Rano wadda ta rasu a wurin a kan hanyarta ta shiga Kano, an ce daga nan aka samo sunan na Gurin Gawa.

    Zuwa yanzu, garin ya kasu kashi biyu, akwai Ruga inda fulani masu sarautar garin suke, da kuma ɓangaren Hausawa inda ake kira Dausayi. A nan ne mahaifiyar shahararren masani marigayi Sheikh Nasir Kabara ta ke.

    TASIRIN SHAHARAR KANO GA SAURAN MAKUSANTAN GARURUWA

    Kasancewar birnin Kano birnin kasuwanci ne ba birnin Siyasa ba, ya samu ɗaukaka tsawon lokaci saboda yadda fatake ke tururuwar zuwa gare shi bisa dalilan kasuwanci. Wannan ya taimakawa birnin wajen zamowa shahararre, shahararsa kuwa ta yi tasiri ga makusantan ƙauyuka wajen karɓar baƙi a ko-da-yaushe, da kuma hada-hadar kasuwanci.

    Kamar yadda aka sani, a baya babu tsarikan otal ko masaukai a ƙasar Hausa, sannan akan rufe ƙofofin shiga birane idan dare ya yi. Saboda haka, matafiya a zamanin baya sukan samu waje da suka aminta da amincin sa su ya-da zango idan dare ya yi kafin su ƙarasa cikin birni. Don haka kafuwar ƙauyuka a kusa da birane kan zamo masaukai ga baƙin da suke haramar shiga kano yayin da dare ya yi musu.

    A irin haka ne aka samu wani mutumi daga ƙasar Bade ta cikin jihar Yobe a yanzu haka ya ya-da zango a Gurin Gawa tare da soma sana’ar Kwarami (awo), inda ya samu shahara a wannan sana’ar, ya rinƙa sauƙaƙawa fatake masu zuwa kano da jakuna siyan hatsi da kuma masu fitowa daga Kano neman haja ba tare da sun yi dogon zango ba. (Har yanzu ana yi wa mazaunin wancan babarbare laƙabi da suna ‘Marken Bade’).

    A ƙarshe, ina da ra’ayin cewar muhimmancin buƙatar bibiyar tarihin manyan tafarkan da suke sadarwa zuwa biranen mu tamkar na sanin tarihin biranen ne.

    Karanta Yadda Aka Yi Bautar Kurmin Jakara A Kano

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Baƙar Sana’a

    Waƙa Mai Taken Baƙar Sana’a

    1. Muna godiya ga Rabbi sarki ubangiji,
    Da ya ba mu hankali yake ba mu lafiya.

    2. Salati da sallama su duma ga Musɗafa,
    Da ya ƙarfafe mu kan mu nemo halaliya.

    3. Batuna a yau baƙar sana’a ce zan faɗa,
    Da ke damun dukkanin musulmi na duniya.

    4. Sana’ar da ke zub da mutuncin mutum duka,
    Ya zam ba shi ƙima a idanu ko da ɗaya.

    5. Sana’ar da ke zubar da ƙimar Arewacin,
    Ƙasarmu Nijeriya anai mana dariya.

     

    6. Sana’ar da Manzonmu ya ce mu guje mata,

    Don kame mutuncinmu dare har da safiya.

    7. Sana’ar BARA gami da ROƘO nake nufi,

    Da yara suke yi har da manya a rariya.

    8. Akwai yara ƙolaye na ƙauye da ke zuwa,

    Birane suna bara a kowacce nahiya.

    9. Akwai masu naƙƙasa ga hannu ko ko ƙafa,

    Sun ɗauke ta lasisin bara sun ƙi moriya.

    10. Abin ban takaici wai bara har gidan giya,

    Jagora da dare ke zuwa da makauniya.

     

    11. Akwai masu yawo ma da katin asibiti,

    Suna ƙaryar ciwo za su sai wai dawa’iya.

    12. Akwai masu bin masallatai an yi haihuwa,

    Gare su suna biɗar abin yin aƙiƙiya.

    13. Akwai masu ƙaryar sun shigo Islamu wai,

    Dangi sun kore su ba abin ci da rataya.

    14. Akwai ‘yan gefen tasha suna wai kuɗinsu ne,

    Na mota bai cika ba zuwa Gombe Zariya.

    15. Akwai mata masu ɗiban yara raɓe-raɓe,

    Suna neman na abin kalaci a rariya.

     

    16. Ko ko wai kuɗin mota ne babu suke biɗa,

    Zuwa Rijiyar Zaki ta Lemo Birgediya.

    17. Kawai sai ka ga mutum ƙaƙƙarfa da lafiya,

    Bara wai yake domin macewa ta zuciya.

    18. Ran nan nai sayayya sai kawai ga wani mutum,

    Cikin duk kamala a shigarsa ba kushiya.

    19. Ya ce min “Ni ne Sharu Naira goma za ka ban,”

    Na ce ban yi niyyar sadaka sai ka zagaya.

    20. Da ƙarshe ake faɗan cewa ai halinsa ne,

    Yana ɓata sunansu sharifai ‘yan Sidiya.

     

    21. Abin tambaya ina dalili na yin bara,

    Da roƙon mutane kullu yaumin a rariya?

    22. Dalilai ba sa wuce biyu ni a nau gani,

    Macewar zuci da ƙin zakkar masu dukiya.

    23. Macewar zuci kan sanya ƙato ya langaɓe,

    Wai shi ya naƙasta ba shi neman halaliya.

    24. Macewar zuci kan sanya mata na ƙauyuka,

    A birni ba ƙodago sai yawon barar tsiya.

    25. Macewar zuci kan sa mutum yai zaman kawai,

    Ba nema sai raraka da maula duk safiya.

     

    26. Macewar zuci kan sa ɗan boko ba zai dako,

    Ko yai leburanci sai ya zauna ba moriya.

    27. Macewar zuci in tai ƙamari ke haihuwar,

    Aƙidar Allah ba ku mu samu abin miya.

    28. Rashin ba da zakkar dukiya yadda anka ce,

    A Qur’ani shi ka sa talauci annakiya.

    29. Zakka ba sai wanda an sani za a bai wa ba,

    Dukkan mai buƙata na da haƙƙi na bai ɗaya.

    30. Zakka in an fid da ta haƙƙin fuƙara’u ce,

    Lallai ne a ba su dunƙule babu wariya.

     

    31. Mece ce ɗari biyar? A ba shi dubu biyar,

    Ko goma ya ja jari ya kauce wa shan wuya.

    33. Zakka har gwala-gwalai na mata sai an fitar,

    In sun kai nisabi shekara in ta dawaya.

    33. Idan har ana bashe ta zakka a kan kari,

    Ga wanda sun cancanta roƙo za ya sanyaya.

    34. Ka ɗauki lauje ka yo ciyawa ka zam sayar,

    Shi yaf fi yawon roƙo a ba ka ko a ƙiya.

    35. Idan har ɓera sata an ce wai halinsa ce,

    Wari ne halinta daddawa babu tankiya.

     

    36. Ta yaya mutum ƙalau madokin kare da shi,

    Zai zo ma bara ka ba shi ba yin tunaniya.

    37. Roƙo bai halatta sai idan an matsu ƙwarai,

    A hanzarta bar shi in buƙata ta zam biya.

    38. Yaƙi da macewar zuci lallai a kanmu duk,

    Bara ba sana’a ce ba roƙo haramiya.

    39. A nan zan tsaya kishi Allahu ba mu shi,

    Mu zam masu dogaro da kai dukka safiya.

    40. Sunana Muhammad Nasiru G. ɗan Ahmadu,

    Baiti Arba’in na shirya wannan ƙasidiya.

     

    Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.

    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Abokin Tafiya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Warin Jiki Yake (Body Odour)

    Yadda Warin Jiki Yake (Body Odour)

    Mutane da yawa suna fama da wannan matsalar ta warin jiki, duk inda suka wuce sai an toshe hanci, wasu kan warin jikin su yana damunsu sosai. Yana yin zufa kaɗan shikenan sai ya fara wari, koda kuwa ya fito da ga wanka ne ya yi zufan. Zufa a asalin sa bai da wari ko kaɗan, To me yake kawo wannan warin?

    Wasu ƙwayoyin cututtuka na bacteria da suke fata su suke haifar da wannan warin jiki, in suka haɗu da zufa sai su ƙara yawa suna producing ɗin wari mai tsananin gaske. Shi yasa in mutum ya yi ɗan zufa ko kaɗan ne sai ya fara wari.. bacterian suna bukatar ruwa kafin su haɓaka shi yasa ko wanka mutum ya yi bai bushe da kyau ba, in ya sa  kaya can sai dai ya ji ya fara wari.

    In mutum yana fana da wannan matsalar ba turare ne maganin ba kuma ba shi ne mafita ba wani lokaci turare sai ya haifar da wani wari-wari ƙamsh-ƙkamshi da ya fi warin wari. Tabbas yana da kyau saka turare amman bai maganin warin jiki zallar shi har sai an haɗa wasu da ga cikin abubuwan da zan jero a ƙasa…

    • Na farko dole mutum ya zama yana wanka da kyau, yana ƙoƙarin wanke duk wata zufan da yake hammata da tsakankanin cinyoyin sa da duk wani lungu da saƙon da yake da gashi a jikin shi.
    • Sai kuma aske gashin hammata da na tsakanin cinyoyi don kuwa shi ke riƙe zufa ya ƙi bushewa da wuri.
    • Da su iya amfanin da sabulun wanka mai antibacteria don rage waɗannan ƙwayoyin bacteria.
    • Akwai masu matsalar yawan zufa sannan kuma ga warin jiki, suna iya amfani da maganin rage fitan zufa waton antiperspirant ana shafa shi a hammata.
    • A kula da wanki da canza kaya akai akai.
    • Akwai abubuwan da ake ci da yake fita ta zufa ya haifar da wani wari, misali tafarnuwa da albasa. In mutum yana yawan cin su sai ya rage.
    • Rage cin abincin mai yaji don yana sa mutum zufa sosai.

    In abu ya ci tura yana da kyau a nemi shawaran likitan fata. Allah ya ƙara mana lafiya.. Amin.

    Danna nan don karanta Yadda Hawan Jini Yake (HYPERTENSION)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Rawar Da Ƙirƙirarrar Basira Ke Takawa Wajen Ƙarfafa Tsaro Da Bunkasa Tattalin Arziki

    Rawar Da Ƙirƙirarrar Basira Ke Takawa Wajen Ƙarfafa Tsaro Da Bunkasa Tattalin Arziki

    Gabatarwa
    Kalubalolin Tsaro
    • A karni na ashirin da ɗaya, matsalolin tsaro sun ƙara zama masu sarkakiya.
    • ‘Yan bindiga, ta’addanci, laifukan yanar gizo, yaɗa bayanan ƙarya, matsin lambar sauyin yanayi, da rashin aikin yi suna da alaƙa da raunin tattalin arziki da rugujewar zamantakewa.

    Ginshiƙan Bunƙasa
    • Wadata a yau ta dogara da ilimi, fasaha, ƙirƙira da ƙarfin ɗan Adam—ba albarkatun
    ƙasa kaɗai ba.
    • Waɗannan ginshiƙai ne ke haifar da juriya da ci gaba mai ɗorewa.

    Ƙirƙirarrar Basira A Rayuwarmu

    Tsaro
    Yadda muke kare iyakokinmu da al’ummominmu

    Tattalin Arziki
    Yadda muke tafiyar da noma, kasuwanci da kasuwanni

    Ilimi
    Yadda muke koyarwa, horaswa, da gina ƙwarewar matasanmu

    Labarai
    Yadda ake gina tsararrun labarai da yaɗa su tsakanin jama’a
    Kirƙirarrar Basira ba wata aba ce ta nesa ba—ta riga ta fara tasiri a rayuwarmu ta hanyoyi da dama.

    Mecece Kirƙirarrar Basira

    01
    Koyo daga bayanai
    Tsarin kwamfuta da ke nazarin bayanai don samun fahimta
    02
    Fahimtar alamu
    Gane tsari da ma’ana a cikin bayanai masu sarƙaƙiya
    03
    Yin hasashen abin da ka iya faruwa
    Hasashen gaba bisa ga bayanai da aka tara
    04
    Taimaka wa ɗan Adam
    Tallafawa yanke shawara mai inganci da sauri

    Kirƙirarrar Basira Ba Zata Maye Gurbin Ɗan Adam Ba

    Kamar yadda rubutu ya faɗaɗa tunanin ɗan Adam kuma ya adana ilimi tsawon ƙarni,
    Tana ƙara masa ƙarfi ne. Haka ƙirƙirarrar basirar ke ƙara sauri, faɗi da tasirin aikin
    ɗan Adam.

    Rawar Da Kirkirarrar Basirar Ke Takawa Wajen Ƙarfafa Tsaro

    • Bayanai da Gargadin Wuri-wuri: Tantance tarin bayanai masu yawa daga na’urorin sa ido domin gano barazanar tsaro
      tun kafin ta rikiɗe zuwa rikici.
    • Tsaron Iyakoki da Al’umma: Jiragen sama marasa matuƙa da tsarin sa ido na taimaka wa tsaron manyan yankuna, musamman inda ma’aikata ba su wadatar ba.
    • Yaƙi da Ta’addanci: Tsarin hasashen laifi na taimaka wa jami’an tsaro su fahimci tsarin aikata laifuka, su hana su kafin faruwa.
    • Tsaron Yanar Gizo: Gano barazanar satar bayanai da kare kadarorin na’ura-mai-lamba na ƙasa.
    • Muhimmi: Hukunci, hankali, ɗabi’a da alhaki suna hannun ɗan Adam. Kirƙirarrar Basira tana taimakawa masu yanke shawara ne, ba ta maye gurbinsu ba.

    Rawar Da Ƙirƙirarrar Basira Ke Takawa Wajen Bunkasa Tattalin Arziki

    • Noma: Inganta hasashen amfanin gona, gano cututtuka, inganta ban ruwa, da sauƙaƙa
      samun kasuwa.
    • Masana’antu: Injina masu sarrafa kansu na ƙara yawan aiki da ake yi da ingancin kayan da ake sarrafawa.
    • Ilimi da Ƙwarewa: Tsarin koyarwa na daidaita darasi da buƙatar ɗalibi, rage giɓin karatu, da faɗaɗa damar samun ilimi.
    • Kasuwancin Ƙirƙira: Marubuta da masu zane na iya kai ayyukansu duniya ta
      hanyar fassara da tallatawa ta dijital.
      Kirƙirarrar Basira ba za ta kawar da ayyukan mu ba; za ta ninka darajar aikin ɗan Adam ne.

    Rawar Da Marubuta Za su Taka A Zamanin Ƙirƙirarrar Basira

    • ƘirƘirarrar basira ba za ta rage muhimmancin marubuta ba; a maimakon haka, tana ƙara
      karfafaku ne. Rubutu ya tsira daga injin bugu, rediyo, talabijin da intanet—ba ta hanyar ƙin sauyin ba, sai dai ta hanyar yin amfani da su.
    • Gina labarai sahihu da ɗabi’u masu kyau game da fasaha da al’umma, Kare harshe, al’adu da asali a duniyar dijital
    • Yaƙi da yaɗa ƙarya
    • Tsattsauran ra’ayi da ruɗani
    • Ƙarfafa ƙirƙira: Bisa ɗabi’un Afirka da na Hausa

    Harshen Hausa, mai ɗimbin tarihi na baka da rubuce-rubuce, bai kamata ya tsaya a baya ba. Ya kamata a horar da ƙirƙirarrar Basira da yaran Hausa.

    Marubutan Duniya Da Kirkirarrar Basira

    Darussa ga Marubutan Hausa
    Marubutan Larabci

    1. Adana tsofaffin rubuce-rubuce ta hanyar na’ura-mai-lamba, fassara ayyukan zamani,
      da yaƙi da tsattsauran ra’ayi. Darasi: Kare harshe da tsaron ƙasa na iya tafiya tare.
    2. Marubutan Turanci: Amfani da AI wajen binciken jarida, tantance gaskiya, da nazarin manufofi. Darasi: AI na iya sauƙaƙa fahimtar abubuwa masu wahala ba tare da rasa inganci ba.

    3. Marubuta a Sin Nazarin ra’ayin jama’a da daidaita tsararrun labarai tsakanin yankuna. Darasi: Fasaha na iya ƙarfafa al’adu maimakon gogewa ko rusa su.

    4. Marubuta a Indiya: Tsarin AI na murya da fassara wajen isar da ilimi ga al’ummomin karkara. Darasi: Kayan aikin AI na murya na da matuƙar amfani wajen ilimantar da al’umma.

    5. Marubuta a Afirka: Horas da tsarin AI a harsuna kamar Swahili, Amharic da Zulu. Darasi: Duk harshen da ba ya cikin tsari na AI na fuskantar barazanar shiga gefe.
    Ga marubutan Hausa, wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci. Idan ku ba ku tsara
    tsararrun labaran ƙirƙirarrar Basira da kanku ba, wasu za su fassara Hausa a madadinku.

    Matsalolin Ƙirƙirarrar Basira A Kan Ɗabi’a Da Al’adu

    • Amfani da Fasaha ba Daidai ba
    • Barazanar nuna son kai ko wariya a cikin tsarin AI
    • Rasa Sirrin Bayanai
    • Matsalolin kariya da aminci na bayanan sirri
    • Lalacewar Al’adu
    • Haɗarin rasa asali da kimar al’adu
    • Dogaro Fiye da Kima
    • Raunin ƙwarewar ɗan Adam da hukunci
      A nan ne rawar marubuta, masana, da jagororin al’adu ta fi bayyana. Fasaha ba tare da ƙima ba barazana ce; amma fasaha da aka jagoranta da al’adu da ɗabi’a na zama hanyar ci gaba.

      Ina Mafita

    Domin cin amfanin ƙirƙirarrar basira yadda ya kamata, ana buƙatar tsari mai ma’ana da haɗin kai. Akwai matakai huɗu masu muhimmanci:

    • Zuba Jari a Ilimi da Ƙwarewa: Hada ilimin AI cikin ilimin boko, rubuce-rubuce na ƙirƙira, koyon sana’o’i, da ilmantar da al’umma. Matasa da aka ƙarfafa da irin wannan ilimi na da wahalar faɗawa cikin munanan ɗabi’u.
    • Ƙarfafa Ƙirƙira ta Cikin Gida: Tallafa wa masu bincike, marubuta, masana
      fasaha da ‘yan kasuwa na cikin gida. Ƙirƙira ta cikin gida na ƙarfafa dogaro da kai, juriya da haɗa kowa cikin tattalin arziki.
    • Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Mai Tsari: Haɗa marubuta, masana fasaha, masu tsara manufofi, da hukumomintsaro. Idan aka haɗa waɗannan ɓangarori, AI na zama ginshiƙin kwanciyar hankali da bunƙasa.
    • Kare Al’adu yayin Rungumar Ƙirƙira: Fasaha ya kamata ta yi wa al’umma hidima, ba
      ta goge asali ba. Harshe, ƙima da labaran al’adu muhimman kadarori ne ga tsaro da ci
      gaban al’umma.

    A taƙaice, ƙirƙirarrar Basira za ta ƙarfafa tsaro da bunƙasa tattalin arziki ne kawai idan aka jagorance ta da ilimi, aka dasa ta cikin ainihin yanayin zaman takewar mu, aka daidaita ta tsakanin sassa, kuma aka jingina ta da al’adun mu.

    Kammalawa

    Ƙirƙirarrar Basira ba barazana ba ce da za a ji tsoro, kuma ba abin bautawa ba ne—kayan aiki ce abar runguma. Sakamakonta bai dogara ga fasahar kanta ba, sai dai a kan yadda muke amfani da ita, wa ke sarrafa ta, ɗabi’un da muke amfani da su wajen sarrafa ta.

    Tambayar ita ce ko za mu bar AI ta ƙara kawo mana rarrabuwar kai da rashin tsaro, ko kuma mu sarrafa ta wajen ƙarfafa haɗin kai, kare al’ummominmu da faɗaɗa damar tattalin arzikn mu.

    Mu zaɓi hanya mai hikima. Mu tabbatar ƙirƙirarrar Basira tana yi wa ɗan Adam hidima, tana ƙarfafa tsaro, kuma tana haifar da bunƙasar tattalin arziki mai haɗa kowa, tare da kare harshenmu, al’adunmu, da ƙimar mu ga al’ummomi masu zuwa.
    Nagode

    Allah ya albarkaci Marubutan Hausa.
    Allah ya albarkaci Jihar Jigawa.
    Allah ya albarkaci Tarayyar Najeriya.

    Daga
    Kanal (Farfesa) AS Imam
    Shugaban Cibiyar Ƙirƙira da Sabbin Fasahohi Kwalejin Horon Kanana Hafsoshin Soja ta Nijeriya (NDA), Kaduna
    31st December, 2025

    Wannan maƙala ce da aka gabatar a taron Ranar Marubuta karo Na 3, wanda ya gabata a ranar 31/12/2025 a Dutse Jihar Jigawa.

    Karanta Labari Mai Taken Ina Za Mu Je!

    Edita@rumasau-kallamu

  • Labari Mai Taken Ina Za Mu Je!

    Labari Mai Taken Ina Za Mu Je!

    Ina za mu je, ina ake so mu je? Gidajenmu sun zama tamkar ƙaburbura, Makarantunmu sun zama wuraren da ake farautar rayukanmu. Ya ke uwa Najeriyarmu, ina za mu je? Don samun mafaka wanda ta wuce bayan ki.

    Bayan mun ci abinci mun sha ruwa, muna latse-latsen waya, kwatsam! Sai ga Laure ta shigo cikin falo a firgice, tana cewa: “Anti, zuciyata ta kasa samun sukuni, a lokacin da na ji labarin da ya faru da ni, ya sake faruwa da wasu ‘yan mata har ashirin da biyar (25) a Jihar Kebbi. A lokacin da labarin ya iske ni, sai na ji komai ya dawo min sabo, na shiga ɗimuwa, hankalina ya ɗugunzuma.

    Innalillahi wa’inna Ilaihi raji’un! Shin rayuwar da muka yi a sansanin da a ka kai mu, lokacin da aka sace mu, irin ta waɗannan ‘yan mata za su yi?” Da labarin fitowar su ya riske ni, na yaba da ƙoƙarin masu juya sitiyarin mulkin ƙasar mu, sai dai ya kamata a ce, an mayar da hankali a kan matsala tun kafin afkuwarta, a yi tsayin daka wajen daƙile matsala kafin faruwarta.

    A samar da tsaro mai ɗorewa, don ina gudun kar abin da ya faru da Laure, ya sake maimaituwa ga ‘yan mata masu ƙananun shekaru irin ta. Wacece ke, me ya faru da ke? Tambayar da na yi wa Laure kenan don jin ƙarshen labarinta. Ta kada baki ta ce:

    “Anti, na kasance ɗaya daga cikin ‘yan matan Chibok, waɗanda ‘yan bindiga suka raba su da ahalinsu, suka rusa duk wani buri na rayuwarsu, suka mayar da gonakinmu mafakarsu, ta gudanar da dukkan tsiya da wasali.

    An killace mu a wani sansani, wadda ake gudanar da rayuwa tamkar rayuwar dabbobi, babu tausayi ko imani a zuƙatansu. An min fyaɗe a wannan waje, wanda ya kasance na samu juna ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. Kaico! na yi ɓarin ciki har sau uku.

    A karo na ƙarshe ne na haifi yarinya ta, wanda ni kaina ban san haƙiƙanin wanene mahaifinta ba, domin a rana na kan samu zaratan maza da suke keta min haddi sama da mutum uku. A lokacin da nake renon cikinta, na haɗu da ibtila’i iri-iri, daga ni har jaririyar cikina mun sha uƙuba, sai dai alƙawarin Allah tabbatacce ne, to wannan ne ya sa yarinyar ta rayu.

    A lokacin da nake naƙuda, na yi matuƙar tausayawa kaina da abin dake cikina domin irin halin ƙaƙa-ni-ka-yi da mu ka tsinci kai ciki daga ni har jaririyar. Na yi doguwar naƙuda, wanda har wani ya ɗana bindigarsa zai harbe ni, don haka suke yi idan irina ta kasa haihuwa da wuri, sai su harbe ta su cilla ta cikin daji abin su.

    Shugaban runduna ne ya ba da umarnin a ƙyale ni, wanda ban san dalilin hakan ba, sai dai na fi tunanin kwana na ne kawai bai ƙare ba. Haka na yi ta fama, jini ya ɓalle min, a haka har Allah ya yi ikonsa na haihu. Babban tashin hankali na shi ne, yadda na haɗu da ciwon yoyan fitsari.

    Innalillahi wa’inna Ilaihi raji’un! Haka na yi ta fama, wadda ta kai har sauran ‘yan uwana waɗanda aka sato mu tare, sun fara ƙyama ta, saboda yadda nake zarni ga ƙarnin jego, har ta kai ga na fara wani irin wari, tsutsa ta fara bayyana a gefanni na, wanda ni kaina abin ya fara damuna, har na fara burin mutuwa.

    Yarinyar da na haifa ciwon shawarar yara ya kama ta, idonta ya mata rawaya-rawaya (yalo shar), ga ba ishashen ruwan nono, domin ni ma ban samu isashshen abincin da zan kai baki na ba bare na samu ruwan nonon da zan shayar da ita, har ta kai na fara addu’a Allah ya sa mu mutu, domin ina ganin da wannan rayuwar ai gara mutuwa, wataƙila ita ce hutu a gare mu.

    Anti kina ji na, a cikin ‘yan uwana da aka sato mu tare, akwai wata wadda ɗaya daga cikin ‘yan ta’adar yake ji da ita, to, da taimakon ta ne, nake samun ruwan zafin da nake gasa jikina, da wani magani wanda ban tantance sunansa ba, sai kuma ɗan abincin da nake sawa a bakin salati. Cikin ikon Allah sai yoyon fitsarin ya tsaya daga nan ne na fara jin ɗan dama-dama wanda har yanzu ina fama da ciwon sanyi, kuma har yanzu ban warke ba.

    A cikin wannan tashin hankali muka ci gaba da rayuwa, wasu an kashe su, wasu kuma an gurɓata musu rayuwa. Ni yanzu babban tashin hankalina shi ne, idan yarinyata ta kai munzalin girma, wane jawabi zan mata har ta gamsu, a kan wanene mahaifinta? Saboda yanzu na cire ƙauna da yin wata kyakkyawar rayuwa don an gurɓata min ita gaba ɗaya.

    Anti, kin san me, dukkan abubuwan nan da suka faru da ni, a lokacin ban wuce yar shekara goma sha huɗu zuwa biyar ba (14-15), a yanzu haka ban san ina ne makomar rayuwata ba.”

    Na yi kasaƙe, ina sauraronta, ban san lokacin da ƙwalla ke fita daga idanuwa na ba. Ke duniya, ina za mu je, ina ake so mu je! Ya ku al’umma ku gane!

    Dukkan al’ummar da ta tozartar da rayuwar ‘ya’ya mata, wannan al’umma ta kama hanyar tozarci da ƙasƙanci a rayuwa ta gaba.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga maƙala mai taken INA ZA MU JE! wadda Na’ima Sulaiman Dakayyawa (Oum Fatayat) ta wallafa, wadda aka gabatar a Taron Ranar Marubuta Ta Duniya na ranar (31/12/2025) a Dutsen Jihar Jigawa.

    Danna nan don karanta Ya Ake Sanin Kai?

    Edita@rumasau-kallamu